Sashe 16
Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shi ba mai kudi bane, ba mai tarin arziki bane, amma babban ma’aikacin gwamnatin Amurka ne, sannan kuma babban manomin ‘Irish’ da ‘cocoa’ a gida Najeriya, ya mallaki komai na rayuwa daidai gwargwadon arzikin da dan adam mai wadatar zuci ke burin samu. Domin duk wata bayan albashin sa na VOA, Hamzah Almutapha Mawonmase, yana da kudin da amfanin manyan gonakin sa na Irish da Cocoa ke badawa duk shekara a garin Jos. Don haka a fahimta ta, mijin nawa, wato HamzahAlmustapha, yana da rayuwa ta sukuni da rufin asiri dai-dai nasa, kwatankwacin bukatar kowanne kasaitaccen babban dan boko a irin rayuwa ta Diaspora. Na bude firjin gidan babu nama da kifi sai express foods abinciccika na leda da na gongoni irin wadanda gwauro ke amfani dasu a yawancin lokuta, babu cefanen kayan abinci sam a gidan shiyasa tun zuwa na yake mana takeaway na abinci. Yau kam nasa a rai na zan fara girki miji na ya koma cin abinci na, na gaji da cin abincin kantuna. Wayata na dauka na kira shi, kara daya tayi a na biyu ya amsa alhalin yana tuki, ina jin sa har da ajiyar zuciya kafin ya ce “Siyam ya aka yi? Kin tashi kin yi wanka in ce ko? Kin daina kukan ko? Na iso office yanzu. Kuma in an approximately two hours zan dawo in sha Allah”. Mamaimakon in bashi amsoshin da ya bukata sai na zarce kai tsaye ga gaya masa makasudin kiran nawa, abubuwan da zai taho min dasu na cefane, na fara jerowa, sai ya katse ni ya ce “Afuwan Habeebty, afuwan Sweetheart, ban taba yin cefane ba, don haka bazan iya rike dogon list dinnan naki ba, yafi karfin brain dina, kin san ba kwakwalwar iya lissafi ke gare ni ba sai ta iya soyayya”. Kunya ta kama ni na kama murmushi, sai yace “He who mastered in linguistics has no mathematlics, (wanda ya kware a iya harsuna bai iya lissafi ba) bari in dawo sai in dauke ki muje Walmert Supermarket kawai ki zaba cefanen ki da kan ki. Daga nan ma ki mike kafar ki da ke nade waje guda kwanannan, bana so ki fara kiba”. Har ga Allah naji dadin fitar da yace zamu yi din. Ban san me yasa ba, a rayuwa ta ina son jerawa da Hamzah, a wasu lokutan can a baya, har mafarkin hakan nake yi, balle a ce a cikin motar sa ne, ina zaune (by his side), shi kuma yana tuka ni (like my chauffer). Sai in ji ni ‘on top of the world’. Bazan manta ba. Rana ta farko da hakan ta faru wato ranar haduwar ‘lifter’ da ya rage min hanya zuwa gida don kada ruwan sama ya doke ni, ni kadai na san abinda na ji a rai na. Na ji kai na ya kumbura, na ji ni tamkar sarauniyar duk matan duniyar nan. Don haka cikin farin ciki na ce, “sai ka dawo din Shaheed, can’t wait for you to come back!”. Da wannan ya karasa ofishin sa cikin farin ciki mabayyani, kai in ka ga irin takun da Hamzah Mawonmase yake yi yau a harabar VOA…tafiya yake gab-gab-gab cikin kuzari da koshin lafiya, far’ar da ke fuskar sa kadai in ka gani zaka tabbatar cikin matsanancin nishadi da madaukakin farin ciki yake. Wanda duk ya gamu da shi a hanya ko cikin ofis din sa sai da ya shaida hakan. Da Director Philip ya tambayeshi dalilin wannan annurin na fuskar sa, da musabbabin wannan fara’ar, sai yayi dariya, daga bisani cewa ya yi yana farin cikin zagayowar ranar haihuwar sa ne domin yau ya cika shekaru 38, kuma wadda ta yi daidai da ranar angoncin sa. Sai Director Philip ya gyada kai yace “in haka ne ya kamata ka dau hutu ko na sati biyu ne, don amarya ta samu lokacin ka sosai kai ma ka samu ka rage tsufa”. Hakan kuwa aka yi. Hamzah ya samu leave na sati biyu kamar yadda ya bukata da ya fada cewa yayi aure. Magana tun ana yin ta kadan – kadan, tsakanin masu aikin safen ranar, har kafin dare kowa a VOA ya san Director Hamzah Mawonmase yayi aure kuma wai musulma ce ba Christian ba. Kowa da abinda yake fada a kai. Wasu karyatawa suke yi don an san cewa ‘catholic’ ne, mai kuma farin jinin ‘yammata iri daban-daban na kasashe daban-daban, sun fi dauka cewa ba zai iya ajiye mace daya kwakkwara a gidan sa da sunan auren sunna ba, ganin yadda ‘yammata iri-iri ‘ya’yan gata ke sintiri a kan sa kasancewar sa media celebrity mai tashe da farin jinni a wurin al’umma, a gida ne ko office. Baka raba Hamzah da baki mata. Sai kowa da ke aiki tare da Hamzah ya zaku da son ganin wacece wannan lucky girl din, da Hamzah Almustapha Mawonmase ya zaba ta zama matar sa. Wasu kuwa tausaya mata suke, a ganin su ba zai taba maida hankali ga rayuwar iyali ba. Duk da haka, suna ganin ita din mai sa’a ce. Sa’ar ta guda biyu ce, na farko ta samun miji broadcaster mai farin jini a cikin mutane ta fannin sana’ar sa, daya da daya ta fannin kyau da iya daukar wanka da iya dressing a cikin mazaje bakar fata ‘yan Najeriya, ta kasa ‘yammata bakar fata da farare har ba adadi, sannan gashi gwani a fannin barkwanci da raha, ko a radio da talbijin yake Magana zaka ji baka so ya daina, gwarzo kuma mai sa’a a kan duk abinda yasa gaba. Kowa dake tare da Hamzah a VOA ya san wadannan baiwarwakin da Allah ya yi masa. Amma a iya tsinkayen su babu wanda ya taba kawo zai iya auren musulma, balle kuma a kai ga cewa shi din ma zai iya musulunta. Koda yake sabga ta addini (is a personal issue) su a wurin su. Har office ya tadda surakuwar sa anty Nasara suka gaisa, kasancewar ranar rahoton safe gare ta, ta tambaye shi Siyama da kwanan ta, yace “mun tashi lafiya Anti, tana gida tace in yo mata cefane. Ya ce, “gashi ni ban taba cefane ba Anti, so ban san me da me ake ajiyewa a gida ba, the house is empty she said, kafin aure I use to go to restaurants to eat, ko in ci snacks in sha tea shikenan fa, a haka nake maneji, don haka nace ta bari in dawo sai muje tayi da kan ta”. Nasara tayi dariya tace “wannan shine amfanin auren ai Mr. Hamzah, a kula da kai, a kula da cikin ka, sannan kuma a kuma kula da komai naka. Baban ta ma yace in gaya maka zai kawo ‘gara’ gobe. So baku bukatar sayen komai banda nama da kayan lambu dana gwari. “Menene GAARA?” Hamzah ya tambayi Anty Nasara innocently, da accent din sa mai kama da na Asians. Tsakani da Allah bai san wani abu gara ba. Dariya ta sake yi da yadda ya ja harafin ‘A’ din din ya furta “Gaaara”, ta ce “wata al’adace mai kyau ta dangin mata ga miji, in an kawo anjima zaka gani, ganin idanun ka”. Hamzah bai jima da fita ba Aunty Nasara ta nufi office din Director Philip Carter. Suka gaisa sannan ta gaya masa auren Director Mawonmase da diyar ta. Tana bukatar su hada masa (grand dinner) ba tare da sun yi shawara da shi ba. Dr. Philip was excited, da jin cewa ashe amaryar ma diyar Nasara Alkali ce, so abu duka ya zama nasu maganin a kwabe su, domin Hamzah na hannun daman sa ne sannan na kowa ne a VOA, kowa nasa ne yana da son mutane, yana da yawan taimako ta fuskar aiki ga na kasa da shi, bai da abokin fada. Sai mai wasa da aiki da gangan, shine kadai zai ga fushin Hamzah, nan da nan Director Philip ya hau buge bugen waya department by department yana bada umarnin abubuwan da za’a tsara washegari. Ba tare da Hamzah ya sani ba. Karin armashin abun Nasara ta ce masa yar tata da Director Hamzah Mawonmase ya aura is an intern yanzu haka tare da su a political department. Sosai VOA suka shiryawa Hamzah (grand dinner) din taya murnar aure irin wadda ba’a taba shiryawa kowa a ma’aikatar ba, ba tare da ya sani ba, a babban dakin taro na ‘Muryar Amurka Hausa’. Yana isa gida dai-dai ya isa ma’adanar motar sa Nasara ta kira shi. “Mr. Hamzah ka je gida lafiya? Gobe da dare misalin karfe takwas na dare kuna da wani schedule ne?” Hamzah ya ce “no Antin mu, ai daga yau na rufe fita kuma sai bayan sati biyun nan da office suka bani, in Allah ya sa muna cikin rayayyu. Zamu tafi (MIAMI RESORT) cikin satinnan, ba inda zan kara lekawa sai dalili yayi dalili”, Aunty Nasara tayi murmushi cikin jin nauyin sa amma shi ko a jikin sa, Hamzah ba zai daina bata kunya ba, shi sam baya surakuta, a ranta tana tausayawa ‘yar ta Boddo-Siyama. A irin rawar jikin nan da Hamzah ke yi a kan ta, Allah kadai ya san irin tumurmusar data ke sha, poor Siyama! Amma ta taya ta murna don ka auri mijin da ke son ka, yana mararin ka, yana gayawa duniya lokacin hutun sa naka ne, kuma a kayi sa’a kaima kana son shi, irin son da Siyama ke yi wa Hamzah, wani babban alfarma ne da ba kowa Allah yake yi wa ba. Ba kowa ke dandana irin ni’imar da ke cikin irin wannan auren ba. “Alright, ku shirya Young Abba ya ce zamu zo mu dauke ku zuwa wani guri, kada ka damu (is just for thirty minutes), kada ka tambaye ni ko ina ne amma fa”. Ta karasa da dariya. Kamar mai Magana da kanin ta. “To shikenan Anti sai kun zo. Amma dai Siyam Jilbaab (hijab) din sallahrta zata sanya ko? Idan har kin san akwai maza a wurin?” Aunty ta rike baki tana hadiye dariya, sai kuma tace “duk shigar daka zabarwa matar ka Hamzah ita zata yi!”. “To babu matsala Anti, Allah ya kara girma, sai kun zo”. Duk hirar da suke yi shi da Anti a kunne na ne, don lokacin ya iso gida, ya adana motar a