Sashe 14
Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bazan taya ka ba, ka tashi ka yi sallah ka gaida Ubangijin mu, ya fi min dadin I love you din Habeeby”. Hamzah ya dan bude idanun sa kadan, da suka kankance suka yi ja, yana dan murmushi cikin lumshewar ido, murmushin da ya kara ma kyakkyawar fuskar sa kyau, amma da ace na san giya da na gane, a karshen buge yake a lokacin. Ya ce. “I’m sleepy, Sweetheart!”. Daga haka ya maida su ya rufe, ya koma barcin sa cikin kwanciyar hankali. (Barcin da bai tashi ba sai karfe goma na dare). Amma ya tashi ne cikin hayyacin sa. Ko da ya duba lokaci da sauri ya bar gadon, a gurguje ya fada wanka yana fadin “Siyam, zamu raba alhakin nan na rashin sallah ni da ke, shine ko ki tashe ni?” Ko kula shi ban yi ba, don na cika da takaicin kin tashin sa yayi sallah a kan lokaci, a rayuwa ta bana son jinkirta sallah babu uzuri karbabbe, ko yin kara’in salloli, koda yake an ce wai barci uzuri ne? Ban dai sani ba. In ma uzuri ne in an tashe ka fa? Na cigaba da shafa lipstick da nake shafawa a gaban madubi na ban ce masa komai ba. Yana barcin nasa naje nayi wanka na tsala ado da atampa embellished wadanda musammman Anti ke bada sautu Katsina a kawo mana in ta samu mai zuwa Najeriya, bayan nayi sallahr magriba da isha duk yana barcin asarar lokaci. Ya zo yayi kara’in sallolin la’asar, magriba da ishar sa a gurguje, sai na tuna masa shaf’i da wuturi sannan yayi. Washegari da safe na yi kwalliya ta tsaf cikin swiss lace ruwan zuma, na kafe daurin kai a saman goshi kamar mai shirin zuwa dinar babbar aminiya. Dai-dai lokacin da Hamzah ya fito daure da towel iya kugun sa, ga wani karami a hannun sa yana tsane ruwa daga tarin sumar kan sa da baya askewa sai tsananin kulawa da yake bata, wadda yanzu ma ya wanke ta cikin kumfar Arganavita (Argana care&Lavender). Ta cikin mudubin na hango shi, ba shiri na sunkuyar da kai, my handsome hunk husband, looking obviously ravishing, sunkuyar da kan nawa ya faru ne kasancewar ban taba ganin namiji babba a fili cikin wannan yanayin ba, balle nawa mijin mai zati na gaske, mai kirar fadin kirji wadanda ake ma lakabi da giant, with physique chest, and handsome face, ga wani lallausar gashi da ya bi ya kwanta lambam a saman kirjin nasa, ya bashi cikakkar suffa, ta kasaitattun maza. Sai a lokacin ya gama shiryawa, cikin bakaken suit da suka yi matukar amsar jikin shi, kodayake kowacce irin suttura Hamzah ya saka karbar sa ta ke yi ta kuma dace da zubin halittar sa, ta kasan idanu na nake satar kallon sa kaina a kasa, na kasa dagowa in sake kallon sa ido da ido sabida kunyar da ya bani daga irin kallon da yake yi mun, kato dashi a tube, ya zagayo inda nake zaune ya russuna ta saman kafadu na. Kyawawan fuskokin mu suka koma cikin mudubin, tamkar wata dan daren goma sha hudu da tauraruwar sa Zahrah, don haske da kyallin amarci da fuskokin mu ke yi. Santsin gargasar da ke gefe da gefen fuskar shi da ke jike jagab da ruwa mai dumi ya shiga goga min a fuska, wadda baya rabo da gyaran ta da tsaftace ta, kamshin bath gel din ‘Argan’ da yayi amfani da shi ya mamaye ni, lokacin da ya russuna ta saman kafadu na yana goga min santsin jikakken sajen sa. Sai naji ba abinda nake so a lokacin irin ya sumbace ni, ina so in sa hannu in riko wuyan sa amma na kasa, gashi ni bazan iya fada masa na warke I need him now ba, ko fara aiwatar da sumbar da kai na sabida fulatanci na. Kamar Hamzah ya san me nake ciki sai bai sumbace ni din ba, sai gashi na da ya gyara min ta hanyar tufke shi a baya na. Sannan ya mike hannun sa dogare da kujerar dana ke zaune. Daga tsayen da yake cikin kulawa da sanyin murya ya ce. “Siyam zan tafi office, me kike so in taho miki da shi? Ko kina da sako gun Aunty?”. Ji nayi kamar in dora hannuwa a ka in saka kuka. Cikin damuwa nace “office kuma? Basu baka hutu bane? Ni ban taba jin angon da bai yi sati biyu da aure ba a office ba”. Dariya ya yi, ya ce “idan kina so in dauki hutu ki gama naki hutun daga yau, na fara gazawa, inna dawo yanzu ki daure ki dumama ni, ki armasa min daren yau yadda ya kamata in san cewa hutun amarci nake yi. Tun jiya ina kallon ki wani sabon kallon so kike min, amma fulatancin ki na cutar ki, har da jera wasu munafukan filallika a tsakanin mu. Bude baki nayi cikin mamaki kafin in rufe ido ina dariya nace “ni din Shaheed?” Yace “kwarai kuwa, inada kula fa akan komai nawa balle mata ta uwar ‘ya’ya na, sai wani kallon love kike min ta kasan Ido a fakaice kina fuskewa. Ki cire rigar fulatancin kawai mu yi ta kawar da arna, mu mori ni’imar soyayyah da Allah ya yi mana”. Ban san sanda na kama dariya ba, nace “Sabida Allah Shaheed a ina ka koyi Hausa ne har haka? Har ka san wani a kashe arna?” Sai ya hau warware necktie din sa, ya fara undressing kan sa yana cewa “zancen kike so, bari ki ga yadda ake kasha arnan, ni nan da kike gani har Hausa Bakwai da Banza bakwai na sani, na san Barbushe da Tsimbirbira da Bayajidda har da Sarauniya Daurama”. Sai dariya na ke kyakyatawa shikuwa ya samu gangara ya soma cakumar kirji na yana fadin “ki min adalci mana Aisha_Siyam, in hutu ne ai na bar ki kin huta sosai fa. Kada abin ya koma da daukar hakki”. Wani hali irin namu na mata sai na soma kokarin kwatar kaina ina fadin “Shaheed! Ba office ka ce zaka bane yazun?” Hamzah ya yi min kyakkyawar rikon dana kasa kwacewa yana fadin “yarinyar nan kada mu fara ‘yar haka da ke, zan jure komai ciki har da duka amma ban da wannan yaren a lokacin da nake tsananin bukatar sa. Ko don kinga duk abinda naga kina so shi nake yi babu musu, shine zaki dauka har na gama amarci na? Daga kawai na bar ki ki yi healing? Sai ki mike kafa ki dauka an gama? Wani abun ma ai sai mun dangana da Miami Resort, ba’a yi komai ba fa, sai bude hanya”. Na rufe ido ina dariya kunya kamar ta kashe ni. Daga haka ya shiga seducing dina ko ta ina, in the way and manner (ta hanyar da ya san) duk zukewar da nake faman yi bazan iya na kaucewa bukatar sa ba. Domin wannan karon da canji ya zo; ya zo ne da sassanyar soyayya da na kasa tankwabewa. Haka hanyar da ya biyar da ni wannan lokacin daban take, wato ba irin ta lokacin farko bace, (so soothing and so romantic), ban san lokacin da na sakar masa ragamar rayuwata da gangar jiki na bakidaya ba. Cikin dan lokaci kankani na kara amsa sunan MATAR HAMZAH. Cikakkiyar amsawa mai amo da sauti. Irin amsawar da ko wadanda suka shekara hamsin tare da junan su cikin rayuwar aure basu yi irin ta ba. Babu inda bai bi ya side ya tande a jikina ba. Lokacin da na fahimci Hamzah ya biya bukatar auren sa da ni (in a soothing way), mun kuma samu wata irin gamsuwa a ciki wannan karon fiye da duk yadda zan kwatanta, fiye kuma da lokacin baya Amma sai me? Duk da cewa gashi dai na samu cikar burika na da tabbatuwar dukkan mafarkai na, gashi dai na samu duk abinda nake so a auren Hamzah Mawonmase, na samu duk irin soyayyar dana ke mafarki da kintacen samu daga Dream Husband dina a tare da Hamzah, na samu mijin wato Hamzah a yadda nake so ya kasance. A fannin soyayya da farantawa matar sa ya zarta har fiye da mafarki da burika na, amma sai kawai Abba na ya fado min a rai, naji tamkar Abba ya san abinda nake nan ina aikatawa a bayan idon sa, wato abinda na zaba sama da in yi masa biyayya kenan! Abin nufi, zabar soyayyar Da namiji da jin dadin rayuwa ta a kan sa.....wannan ne abun da nake ganin bazan iya yi da Ya Omar ba sabida nauyin ‘yan uwantaka da respect din dake tsakanin mu, duk da Allah bai haramta yiwuwar aure a tsakanin mu ba. Sai kawai na hau kuka wiwi, kukan da Hamzah bai san dalilin sa ba, kuka nake na karin son miji na da kuma damuwar tunanin mahaifi na rashin kyauta masa dana yi duka a lokaci guda, alhalin a lokacin ina manne cikin jikin sa, mun kasa rabuwa da juna tamkar an sa glue an manne mu cikin jikin juna. Ko kuwa ka yi tsammanin a haka aka halicce mu sabida yadda muka dunkule cikin juna tamkar curin alkaki. Kowannen mu shauki abinda ya faru ‘yan mintunan da suka gabata ya kasa sakin sa. Lallashi da ban baki irin wadanda Hamzah ya rika yi min, kamar shima zai taya ni kukan sabida yadda kuka na ke luguiguita zuciyar sa, a wannan ranar mai dimbin tarihi cikin rayuwar auren mu na kasa manta su, sabida muhimmancin su da tasirin su gare ni. Lallashi ne irin wanda maza basa yi wa mata, shi kam daban yake da mazan hausawa. Abubuwa da yawa na sawa mace ta kara son mijin ta a irin wannan lokacin, ni na kara son Hamzah ne sabida saukin kan sa, duba da yadda ya damu da damuwar dana ke ciki wadda shi bai san ko ta mecece ba har ya fi ni damuwa da kuma irin kalar lallashin da yake min in a soothing and romantic manner. Sabanin ni da nake kukan damuwa da tunanin rashin albarkar mahaifi na na bibiya ta, da kuma tsananin kewar Abba na da ahali na, shi Hamzah kukan farin ciki ya ke yi a wannan lokacin. Farin ciki irin na samun