← Book details Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 30

Sashe 15

Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mace wadda ta zarcewa burin sa. Matan da ake kira “shu’arah” a harshen larabci wadanda daidaiku ne a cikin matan duniya. A karo na biyu, Hamza ya sake neman kari, bai ko yi la’akari da kukan da na ke ta yi ba, tunda ya yi lallashin har ya gaji ban daina ba, kukan nawa ma sai ya zame masa tamkar ziga, sai dai this time around he is doing things very gently. Kokarin Hamzah shine ya samu rangwame daga tarin ajiyayyar sha’awar sa ta shekarun rayuwar sa 38, wadda ya yi rantsuwa ya yi alkawarin sai ta hanyar aure kadai zai kawar da ita da kuma matar da ya tabbatar yana yi wa so na hakika har zuciya da bargon sa, daga bisani shi da kan sa ya tausaya min, ya kuma tausayawa kan sa for being insatiable.... Ya tabbatarwa kan sa yanzu kam ya gama sauke dakon samartakar sa, da gwaurantakar shekarun kuruciya. Daga bisani ya je ya sake yin wanka, ya sake shiryawa shirin tafiya ofis, ya shirya ne cikin kananan kayan da suka fi amsar shi fiye da na farko da ya canza. Ni ina daga kwance ina ta ‘yan koke koke na wanda zuwa yanzu ya ce sun koma na shagwaba kuma, har yanzu ban yi shiru ba har ya gama shiryawa, ya shiga kitchen da kan sa ya hado min tea ya dumama samosa ya kawo min, ya ja bedside ya dora a kai. Gashi ana ta kiran sa akai-akai a waya daga office din su (VOA). Duk sun kasa masa hankali, ya rikice ya rasa da harshen da zai lallashe ni in yi shiru kuma, ya ce “ki yi hakuri Sweetheart, na san lamarin nawa is too much idan ni ne na yi laifin nan, amma babu yadda zan yi ne, ya kamata ki fahimta na wahaltu wajen rike kaina har zuwa wannan lokacin, amma hakan bai fi ba akan a ce wata ta riga ki samun wannan alfarmar ta hanyar haramun? Ga lada mai yawa kina ta samu Boddo na Boddon Anti? In this aspect… Na karya miki hula, na lankwasa guiwata a kan ki, na rantse, bazan iya rayuwa ba tare da ke ba Siyaaama”. Kukan nawa wanda babu amo ko sauti sai hawaye masu yawa da sheshsheka ya karu, hudawa yake har cikin ran Hamzah Mawonmase. Ganin ya kasa lallashin nawa in daina kukan kuma dabarar sa ta fara karewa ba tare da ya samu yadda ya ke so ba sai ya ce, “Yanzu dai ki min izini in je office in dawo, kin ga dai duk basu san nayi aure ba, kin dauke hankali na daga kan komai Siyama-Boddo. Ko excuse ban bayar ba, shi yasa da basu ganni ba kwana da kwanaki yau suke ta kira na su ji ko lafiya. Ina so in dauki hutu daga yau don in samu damar da za mu tafi Florida (Miami Resort), don haka bazan jima ba, in na dawo sai na amsa query, daga nan mu dora daga inda muka tsaya”. Ya fada cikin tsokana da son saka ni magana dole. Ai kuwa kuka ya kara kwace mini, ganewa da nayi ya maida ni abar tsokanar sa. Murya ta abin tausayi nace “me za’a dora din daga inda aka tsaya din? Kai fa sai ka koyawa bahaushe Hausa” Hamzah ya kwanto a jiki na gabadaya yana murmushin tsokanar da bai gajiya da ita, ya sakar min dukkan nauyin sa da gangan, na yi ‘yar kara nace “Shaheed za ka balla ni”, ya kanne ido guda yana murmushin abinda zai fada, sai ya yi wani irin kyau a idanu na, cikin sigar jan fada kasa-kasa yace, “wai third round din mu na yau nake nufi ko ya kika gani? We’re going for the third round da zarar na dawo, ko Baby ya yi maza- maza ya shigo gidan Uban sa?” Na yi maza na ture shi daga kai na ina fadin “ni ban isa haihuwa ba wallahi bazaka tsofar da ni yanzu ba”. Sai lokacin ya tuna bai yi sallahr asubah ba. Ya yi tunanin in ya tsaya zai kara bata lokaci ne bari kawai ya je ya dawo sai ya hada ta da azahar yayi, in ya gayawa Siyam bai yi ba kuma ran ta zai sosu. Ya koma toilet da sauri, yana daura alwala. Yana cewa ko kuma ya yi a office in ya samu sukuni. Walha dama wahala take bashi, in Siyam bata ce ya yi ta ba, a lokutta da yawa sharewa yake yi. Har ya dau mukullan mota ya fita sai ya dawo kan gadon inda nake kwance, ya sa hannayen sa ya tallafoni ya dago ni daga kwanciyar ya aza bisa cinyoyin sa, yana min wani irin kallo kamar zai hadiye ni cikin cikin sa ya huta. “Ko dai Babyn Mawonmase har ya samu muhalli ne? Irin wannan fresh da kika yi daga jiya zuwa yau bangane masa ba Siyam-Boddo. Ko duka ‘yan Mambillah haka suke very fresh a satin farkon su?” Cikin kishi mai tsanani nace “akwai mata da suka fi ni kyau da yawa a Mambillah, in muka je zaka gan su fal, har in kana son kari ka kara da guda uku”. Dariya yayi cikin matsanancin nishadi. Ya fahimci Siyamah akwai kishi. Ya ce “wa? Ni Hamzan wai? Yanzu in kara aure in bawa matar me? Bayan saboda greadness (hadamar ki) kin kwashe komai dake cikin jikin Hamzahn, baki barwa sauran mata komai da ya danganci sperm daga Hamzah ba. I’m now empty. Habeebty yau ji na nake wani irin sakayau! Fresh and reborn, kamar yau aka haifo ni. Thanks for the wonderful gift of love and and all the sacrifices Siyam. You know I LOVE YOU ko? To a yau na ninka wannan statement din zuwa sau trillion. In tsaya ina ce miki “INA SON KI” will not be enough to express my gratitude to Allah and to you Aisha-Siyama. Insha Allahu zamu je gida Najeriya don nasan damuwar ki kenan, idan na gama mana shirin tafiya a sannu, in je ga Abba in durkusa in nemi albarkar sa, in gaya masa ya iya haihuwa, ya bani farin cikin duniya bakidaya sai fatan samun na kiyama. Daga nan in ga tsaunin Mambillah (Mambillah Plateau), in ga garin Gashaka (bangaren surukaina na wajen uwa), in hau tsaunin Mayo Selbe in hango ko’ina na Gembu, in kuma ga Kakar mu abar son mu, Ummati”. Wani murmushin dadi ya subuce min, ban san na yi kewar gida har haka ba sai yau da ya ambato tushe da asali na. Bahaushe yayi gaskiya da ya ce “KOWA YA BAR GIDA GIDA YA BAR SHI”. Ko babu komai na dan ji sanyi a rai na, at least he cares, tunda ya yarda zamu je ga Abbana ya taya ni rokon gafara, ya kuma nuna damuwa da damuwa ta. Sannan ya bani dukkan kulawar data dace miji ya baiwa matar sa da ke cikin hali na damuwa. Ka tsaya karantar halin da matar ka ke ciki ma soyayya ce mai zaman kanta, da ba duk maza ke yi ba, in dai sun samu biyan bukatar gangar jikin su. Ina so mu je ga Abba kwarai don in nemi gafara ko in bashi dama ya yanke min duk wani hukuncin da zai wanke ni a wurin sa, in dai ba zai raba ni da miji na ba zan dauka, koda kuwa zai ce in fita neman Ya Omar kasa-kasa ne, amma bana son tuna ranar haduwa ta da Ummati, ba don komai ba sai don na san sai tafi Abba daukar zafi don mutum ce mai matukar kabilanci da wariya ga wadanda ba Fulani ba, musamman kuma a gaya mata asalin ko wanene Hamzah, a can baya ta kan bamu labarin arnan Jos da kiristocin cikin su kasancewar akan samu auratayya tsakanin Beroms da Fulanin jeji, ta sha gaya mana labarai a kan su da yadda sukewa musulmi da hausawa kisan gilla a yankin su, ban san hukuncin da zata dauka a kan aure na ba, idan ta ji ko wa aka aura min/wa na zaba ya zama miji na, ba kuma da sani da yardar ta ba. Kai bana zaton ma ta san da maganar auren. Tunda Young Abba yace sai gashi ga ta zai fada mata. In ya so ya jurewa duk boren ta. Na kuma tabbata yadda Abba ya ki tsayawa ma ya saurari zancen auren daga bakin Young Abba da kyar in zai yi wa Ummati zancen. Shi kuma Young Abba ya ce ba zai gaya mata a waya ba tunda ya kusa tafiya gida Najeriya sai sun hadu gaba da gaba zai mata bayanin Hamzah, asali da tushen sa zata fi fahimtar sa fiye da a waya. Amma tabbas ya san (she will retaliate). Hamzah na tafiya office bayan na ce “a dawo lafiya Shaheed”, ina so in ce masa baka yi sallahr walha ba, kuma sallahr walha ba’a farawa a daina, amma na yi shiru na barwa rai na, dole sai ana masa uzuri a hankali, amma na sa a raina zan cigaba da naci a kan sa kwarai da gaske, har zuwa ranar da Allah zai sa ya rike sallolin sa biyar da nawafil da kyau da ikhlasi. Fitar sa ba jimawa na tashi na yi wanka na shirya na yi tsaf da ni, gidan Hamzah Mawonmase dan karamin American-Condo ne, amma komai na bukatar rayuwar dan adam ya ji sharr a cikin sa. Fasalin gidan da komai da ya zuba a cikin sa ya yi min daidai da nawa tsarin rayuwar, ya yi daidai da yadda nake son gidan aure na ya kasance in dai a rayuwa ta diaspora ne. Perhaps sabida zukatan mu tare suke motsi, shi yasa hatta likes and dislikes din mu na tsarin muhalli ya zamo daya. Ina son farar kala Hamzah na son fararen abubuwa. Shi ba tankareren gida ba, ba kuma gida ne mai yawan dakuna ba, a’a dan karamin apartment ne mai dakuna biyu daga nawa sai nasa sai study da babban falo. Babban madafi da toilets a kowanne daki. Na yarda na amince ni din, wato ni Aisha-Siyama Mamman Gembu, mutum ce mai sa’ar samun dace da samun burirrikan ta. Hamzah Mawonmase ta wani wani fannin ya zo a yadda nake son sa,
Chapter 15 · 0% Book details