Sashe 18
Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bayan mun rage nauyin kayan jikin mu na yi sallahr isha da ban yi ba, lokacin Hamzah yana nasa dakin bansan dai ko me yake yi ba dai. Na kashe wuta na kwanta kenan sai gashi ya shigo dakin cikin ruwan tokar kayan barci masu kauri ‘yan gidan ARMANI. Yana tazar gashin kansa da ya wanke cikin kumfar (Argan). Bana gajiya da kallon fuskar miji na Hamzah, kamar yadda idanu na ke son gargasar gefen fuskar sa da ta saman kansa wato tarin lallausar sumar kan sa da yake tarawa mai dan karfi irin ta Black Nigerian Men. Wadda kullum cikin kula da ita da tsaftace ta yake. Ina so na tambayeshi ko yayi sallah amma na daure na yi shiru, don bana so ya gane cikin kwanakinnan na saka ido a kan sallahr tasa. Wadda na lura in ban ce ya yi ba, tun bayan da amarcin ya soma sauka a kan sa to ya daina yin ta sam. Hoping yau zai yi din kafin ya kwanta, ba tare da nace ya yi din ba. Amma har ya hawo gadon da nike kwance da niyyar kwanciya barci bai yi sallolin ke kan sa ba na magriba da isha. Bai kuma san na lura da hakan ba. Ina jin sa ya ja duvet ya lullube mu, ya soma laluba ta, ban san lokacin da na kwaye bargon ba, na dauki filo na jefa can gefe na maida mu kwanciyar kai da kafa. Cikin mamaki Hamzah ya ce “idan na shure idon ki fa ban sani ba da kafa ta? Wannan wane irin sabon salon kwanciya ne na wulakanci? Ko in ce sabon raini? Tukunnama, kin ji na ce ina neman wani abu ne, just daga kawai mutum ya rungumi matar sa?” Na dai yi masa shiru, ko na samu ya gane fushi na akan rashin sallahr sa ne ya tashi yayi amma gogan sam bai gane ba. Hakan ta sha faruwa, ba koyaushe Hamzah ke iya yin salloli biyar a rana ba, watarana asubah kawai yake yi itama don ina saka shi a gaba ne in ce ya yi mana limanci. A haka muka kwana, zuciya ta ta yi duhu, yayi maganar duniyar nan ya yi ban-bakin duniya akan in gyara kwaciyar da na yi, shi ba abinda yake nema yau, ban ce masa kala ba. Don kan sa ya gaji ya juya min baya shima ya kwanta, kan sa daidai kafafuna kamar yadda na zabar mana. Haka washegari na tashe shi don yayi asubah in gani ko zai hada dana jiya da bai yi ba? Hamzah juyi yayi cikin barci yace “Siyam, zan yi in na tashi, yanzun I’m sleepy”. Daga haka ya juya ya cigaba da barcin sa cikin kwanciyar hankali. Watanni bakwai kenan na auren mu, wadanda watanni ne na wata irin koriyar soyayya shar, da fahimtar juna tsakanin ma’aurata mai shiga rai, babu komai a cikin su sai sassanyar soyayya mai tsayawa a zuciyar masoya, musamman wadanda suka yi dace da kasancewa karkashin inuwar aure. Amma kuma daga wata biyar baya Hamzah ya kasa sallah yadda ya kamata, in har ba na ce tashi ka yi ba. Abinda ban fahimta da wuri ba shine Hamzah baya wankan janaba (guslul janabah) sai na sabulu da gel-gel din sa kala-kala na gayu masu dan karen tsada. Sannan ya koma shan giyar sa har fiye da shan da yake mata a baya. Ina ganewa ya sha barasa idan ya buya a dakin sa, alhalin na san yana cikin gidan, da kuma duk lokacin da yake barcin da ya kasa daga ko dan yatsan sa. Amma hakika ya cika umarni na wanda yake kira severe punishment a gare shi, bai kara attempting neman komai daga gare ni ba, tun daga lokacin da na tsiri mana kwanciyar kai da kafa, da jera filallika a tsakanin mu. Sannan ya kasa ganin walwala ta ko kankani. Ya dauki hutun karshen shekara musamman domin yayi settling abubuwan da na tsiro a tsakanin mu ya kuma samu Siyamar da ya yi kewa, amma ya rasa kaina ya rasa kasa na duk da hakan, ni kuma na kasa fitowa fili in gaya masa bazan iya hada jiki da shi alhalin ya kasa tsaida sallah kuma yana shan barasa duk irin son dana ke masa. Ta fannin abinci bana wasa da yi masa girki mai kyau, tuwon Acca ma akai-akai nake yi masa, sai kazo shimfidar mu ka gan mu kai da kafa, kowa na fama da dacin dan uwan sa da rungumar filo, Hamzah na ganin Siyam tana kwarar sa babu hujjah babu dalili sai halin rashin godiyar Allah irin na mata, tunda da me ya raga mata? Kusan duk alkawuran da ya daukar mata daga auren su zuwa yanzu ya cika su banda na zuwa Najeriya. Shima kuma ai sun yi shawara ne sai ta kammala karatun ta gaba daya. Kullum ita yake tunawa kafin ma ya tuno kan sa ko Kakar sa. Amma duk bata ga wannan ba sabida halin su na matan da suka samu miji na son su, ta gwammace ta canza musu rayuwar farin cikin da suke ciki zuwa gaba. A yanzu a yanayin da muke ciki ni da Hamzah (idan har ban yi kuskuren fahimta ba), idan har ba shaidan ne yake ingiza ni ga yarda da wannan sabon tunanin nawa ba, zan iya cewa Hamzah ya koma kiristancin sa ne kawai, wato ya shigo addinin musulunci da fuska biyu (da boyayyar manufa ta ya samu Siyama tunda bashi da alternative banda musulunta din in har yana son samun Siyama), amma ba don tsoron Allah ba ko tsoron haduwa da shi, sai don samun damar auren Siyamar data juya duniyar sa, ba kuma don ya tsira daga azabar wuta ba, tunda in bai musulunta ba babu ta yadda zan yarda in aure shi, ko su Young Abba ma bazasu saurare shi ba, ko da soyayyar sa zata kashe ni. Amma wannan tunanin nawa ne ni kadai tunda shi dai bai gaya min da bakin sa ba. A sabuwar fahimtata da Hamzah yanzu, Hamzah ya aure ni ne da niyyar in ya sameni ya gama daukar abinda zai dauka a jiki na, sai ya daina sallahr ya koma rayuwarsa ta kafurci yadda yake yin ta a baya babu kuma yadda zan yi da shi, tunda na riga na zama karkashin ikon sa, a lokacin da ban isa in ce bana auren sa ba, don in har ba kuskuren fahimta na yi ba, a halin yanzu ina da karamin juna biyu, aure na kuma bai sa ya daina shan barasa ba, bai hana shi zuwa Bar da clubs yin caca ba, duk da yana boyewa har na zo na gane da kai na. A sannu na kara fahimtar abubuwa sun sauya a tare da Hamzah na, dokin musuluncin ya sake shi daga lokacin da na samu ciki na rage bashi hadin kai a shimfida sabida bana son turaren sa, yana murna da cikin, kuma yana matukar son a haife shi lafiya ya samu aboki, sanyin idaniya ko magaji. Sai daga baya na fahimci wani abu, ashe duk sanda muka yi auratayya baya wankan janabar da na koya masa, Young Abba ma ya koya masa tun ranar da aka musuluntar da shi. Don wai wahala yake bashi. Kuma a haka zai zo ya yi sallahr sa idan na takura sai ya yi, wadda baya bata nutsuwa da lokaci, babu ikhlasi da khushu’I a cikin ta sharp-sharp yake yin ta kullum, wannan yasa duk na yi wani irin sanyi da ni a kwanakin nan, gwiwata ta sage na sare daga al’amarin Hamzah, jiki na ya yi yi la’asar, na koma wata irin sukuku! Da ni abun tausayi. Gaba daya na birkice na zama kullum cikin damuwa da tashin hankali. Musamman idan na tuna hukuncin wanda ya yi RIDDAH daga addinin musulunci. Ko far’a ta Hamzah ya daina gani, wanda hakan shima ya birkita shi ya sa ya maida zaman sa a gidan sai lokacin barci kadai, don in zai wuni zaune a daki na uffan na daina ce masa, kallon arziki wannan ya daina samu daga Siyamar sa, rarrashin duniya yayi min daga bakin sa don ya ji laifin da yake yi min ya gyara mu koma rayuwar mu ta baya na ki magantuwa, wai an ce shiru ya ishi mai hankali, idan yayi kokarin taba ni kuwa nan zai ga tashin hankalin da zai gwammace mu raba daki, ko jiya da ya shigo rokon in dafa masa ruwan zafi ya sha, sabida baya jin dadi hararar sa na yi, na kuma gaya masa yayi harkar sa in yi tawa tunda ba kabarin mu daya ba, ba kuma tare za’a binne mu in mun mutu ba, tunda ba tare muka zo duniya ba. Wannan ne dalilin da yasa ya zabi kullum idan ya tashi aiki sai ya zarce ‘Bar’ ko wajen caca (Casino), ya sha giya iyaka shan sa, a ganin Hamzah tunda Siyama ta tsane shi yanzu, meye amfanin sa banda ya koma drunker? Na kuma rasa wanda zan iya samu in gayawa damuwa ta a kan Hamzah ko shawara in samu, sai in ga kamar dariya duniya baki daya zata yi min. Idan har ban manta ba, Aunty Nasara da kan ta tun da farko ta fada min cikin karaji, lokacin da ta dawo Atlanta ta fahimci har lokacin da ta yi min bayanin wanene Hamzah Mawonmase ban rabu da shi ba mun hadu mun sarke, bazan manta ba Nasara da yake mai hangen nesa ce ta ce da ni tun a lokacin “HAMZAH MAWONMASE DA TA SANI KARYA YAKE YI BA ZAI TABA MUSULUNTA SABODA NI SIYAMAH BA!”. Ta kara da cewa “kafun ni an yi dubu na, da suka fi ni komai a kan sa, sai dai su su yi riddah, kuma hakan baya sakawa ya aure su”. A lokacin na ji Anty ne kawai, a matsayin ‘yar hana ruwa gudu, kuma maganar ta ta bayan kunne nata bi ta wuce fit, thinking that, in everything there’s exception, wato case dina is different dana sauran matan, don ni Allah ne ya qadarta shigowa ta cikin rayuwar sa ba kyale-kyalen da ya mallaka ba, wanda na ke da tabbacin su sauran matan shi suke bida, da kuma kasancewar sa ‘media celebrity’,