← Book details Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 30

Sashe 27

Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sa ta zauna na rufe mata kofa sannan na shiga baya. Sai da ya kunna motar yayi reverse zai fita daga parking lot din, sannan na ce “Sannu da zuwa Grandma, sannu da hanya. Welcome to Washington”. Ko kula ni bata yi ba, sai fiffizga take yi kaman ta ci babu, yace cikin damuwa, “Kaka ba kya ji ana gaida ke ne?” Ai kamar jira take ya tanka ta balle mana. Cikin hargagi ta ce, “idan kuma ni din kurma ce fa Mawonmase? Sai aka ce dole sai na amsa? Idan Jesus ya sa na kurumce daga sanda ka baro ni a Jos, zuwa yanzu abin mamaki ne? Nace abun mamaki ne? Ko kuma idan na ji sai aka ce dole ne sai na amsa?” Don haka daga ni har shi ba wanda ya kara cewa komai muka kama kan mu, muka kuma kama bakin mu, har muka iso gida. Shi ya dauko kayan ta ni kuma na bude gidan muka shiga dukkan mu, ina gayawa raina zan jurewa wannan tsohuwar da duk abinda ta zo da shi albarkar ‘soyayyah’ da ‘amanar kaunar’ dake tsakani na da jikan ta. Ba don haka ba bazan dauki tsawa da diban albarka ba wanda ko tawa Kakar bata taba yi min ba. Grandma Veronica na shigowa falon gidan mu da katoton frame baki mai rubutun golden ta yi tozali an rubuta “ALLAHU-MUHAMMAD” a jikin sa da Arabic. Ba wai ta iya karantawa bane amma ta san ‘is a symbol of ISLAM’. Abin takaicin a gidan Mawonmase tunda ya zabarwa kan sa auren musulma, ta kada kai cikin tashin hankali ta juyo gare mu ni da shi duk muna tsaye cirko-cirko mun yi tsuru-tsuru sabida tsabaragen bala’in da muka hango cikin jajayen idanun ta. Sai ta ce masa “na ga ‘symbol’ na nata addinin daga shigowa ta an kafa a gidan ka, kai ina hoton Jesus Christ? Kamata yayi tunda ta zame maka dole a ce duka biyun akwai symbol na addinin sa, don kowa ya samu albarkar nasa, tunda gidan ba nata bane ita kadai”. Hamzah ya nisa, sabida shi bai saba tashin hankali ba, duk ya muzanta. Ya ce cikin lallashi. “Kaka, ziyara kika zo mana ko neman magana? Kamata yayi ki zauna ki huta ki ci abinci ki yi wanka, son samu ma ki kwanta ki yi barci, kin yi kwanan zaune a jirgi you need to rest first, sabida blood pressure din ki, ba neman rigima ba”. Yayi maganar ne cikin yaren Birom, Kaka ta ce. “Uban ka Ezekeil da ke ‘heaven’ shi yake rigima amma ba ni ba! Mawonmase ka yi disappointing Jesus, da kyar in albarkar ‘Christ’ bata bar jikin ka gabadaya ba. Bana raba dayan biyun ta dage ta aure ka ne don ta ja ka nata addinin kaima, idan kuwa ta yi wannan nasarar ka gama yin asara da haihuwarka gwara barin ka”. Ta fashe da kuka ta tsugunne a wurin, ta hada hannayen ta biyu ta na kuka tana fadin “Oh Dear Jesus, forgive my Grandson, have marcy on him, ba laifin sa bane, she charmed him!”. Hamzah ya kama ta ya mikar da ita tsaye, ya rike ta cikin hannayen sa yana fadi cikin lallashi da rawar da jikin sa ya soma, “stop crying Grandma, everything will be alright, now, go to the bedroom and rest. Siyam zata kawo miki abinci.” Da jin haka kuwa Kaka ta fasa sabon ihu tana cewa “abincin Moslem girl zan ci? Ai gara yunwa ta kashe ni na san direct paradise zan wuce.” Hamzah ya ce “okay-okay Grandma, take it easy, let me wear my Apron and cook for you”. Sannan ne ta yarda suka wuce tare zuwa dakin da muka tanadar mata wato daki na. Suka bar ni tsaye a falo kamar an dasa ni a wurin. Amma tana shiga ta sake yin tozali da window-size frame na Ayatul Kursiyyu, sai ta ja baya da sauri tana fadin “Jesus Christ, have Mercy! Ba zan kwana a dakin nan ba, tukunnama dakin waye a cikin ku?” Hamzah yace cikin fara kosawa da rikicin ta, “Grandma I think I told you that my house is small, very small, kika ce you can manage with us a hakan, Siyam ta hakura da dakin ta ta bar miki, I think this is respect to you, yanzu kuma kin ce bazaki shiga ba” tace “sai an cire wannan abun fadar min da gaba yake yi”. Hamzah ya dube ni cikin idanun bidar neman yarda ta, dai-dai lokacin dana biyo su dakin jin hayaniyar ta taki karewa, na kuma ji me ta ce, na kuwa yi kicin- kicin da fuska ba rahma ko kadan a kan fuska ta, zan ga wanda zai cire min Ayatul Kursiyyu a daki na sabida wata katuwar kedara, mushrika, ta fara kure hakuri na wallahi. Hamzah ya ga babu fuskar ma da zai nemi wannan yardar daga gare ni, ta a sauke ‘frame’ na Ayatul kursiyyu, sai ya ce mata “to ina zan kai ki Grandma? I have no guest room na gaya miki tun kafin ki zo”. Na ce ba matsala Habeeby, pls bear with her, kai ta naka dakin amma shima akwai ‘frame’ din Bisimillah, ya za’ayi kenan?” Hamzah ya shiga tsaka mai wuya, ga fuskata ba rahma ga Kaka ta kasa ta tsare tana jira ta raka a cire mata Ayatul kursiyyu a daki. Sai ya ce a wahale. “Grandma, kina so jikan ki guda daya tal zuciyar sa ta buga ko?” Tace “no, no, no” ya ce “in bakya so zuciya ta ta buga ‘stop creating commotions’, ki shiga daki ki huta a kawo miki abinci”. Kaka sai ta rintse ido sannan ta shiga dakin nawa da kafar hagu, tana fadin “Jesus save me!” Na juya na wuce kitchen ba tare da na dube shi ba sabida yadda dariya son kama ni, na wuce don na kawo mata abinci, sai ya biyo baya na da sauri. Ina cikin harhada abincin akan tray ya riko kuguna ta baya, “Siyam please, i know she’s worrisome, ki yi hakuri ki taimaka min mu zauna lafiya da ita, ina so in kaita asibiti ne akan hawan jinin ta so probably tayi sati biyu”. Na ce “in dai ni ce kada ka damu, amma ya maganar tafiyar mu Najeriya?” “Magana tana nan, ki bani lokaci in kammala da hidimar asibitin Kaka, in taji sauki….”. Na katse shi da cewa “na rantse da Allah bazan haihu a kasar nan ba, haihuwar fari, ga dan an ce mara lafiya ne, tukunnama tsakani da Allah ka fada mata ka musulunta?” Hamzah yayi shiru, kafin ya ce “I lacked the courage! Sabida hawan jinin ta kada ta samu ‘stroke’ kuma” Wato ya rasa karfin zuciyar fada mata. Nace “then imanin ka na da rauni har yanzu Hamzah!”. Ya kankame ni sosai jikin sa yana rawa ya ce “ina tsoro ne ta tsine mini” na ce “ta dade bata tsine ba, ba abinda tsinuwar ta zata yi maka, babu biyayya ga kowa wajen sabawa Ubangiji, har iyaye kuwa. Ka daina boye musuluncin ka ka fito da shi fili ga kowa in dai ka amince don Allah ka musulunta ba don ni ba”. “Siyam duk abokai na sun san na musulunta, haka abokan aiki, duk wani na jiki na ya sani ita kadai nake shakka wallahi” na ce “ni kuma bana jin zata iya rabuwa da kai wai don ka tuba ka musulunta, inace addini ra’ayi ne ga baligi? Besides, na ga kaunar ka mai yawa cikin idanun ta. Baka ji bama gafara take nemar maka wajen Jesus dinta duk da ka bata mata rai”. Dariya yayi ya sumbace ni a goshi, ya ce muje ki kai mata abincin da kanki, haka zamu yi ta hakuri har su sakko”. Tare muka shiga dakin nawa muka tarar ta bude Bible tana ta addu’a. Kasa zama nayi don bana son sauraron wannan kwarmaton mai neman kashe min dodon kunne saboda rashin dadin sa, na fita, sai shima Hamzah ya biyo ni, muka jera kamar wani mai take min baya. Dakin sa da muka hade tare ya zama namu mu biyun yanzu sakamakon na bar ma Kaka nawa can muka nufa, muna shiga na zauna a gefen gado cikin kokarin boye damuwata, amma Hamzah sarkin fahimtar abu sai da ya fahimci damuwar da nake boyewa din, dama kuma cikin damuwar muke tun kafin zuwan ta ba wai damuwar ta sake mu bane, zama ya yi a gefe na, yace “I know this will surely happen, shiyasa na baki hakuri nace ki jure tun kafin ta zo, I’m very sorry Siyam, na san baki saba da tashin hankali ba, ba yadda zan yi da rigimar Grandma. Amma ki sani ta yi min komai a rayuwa har fiye da wanda uwa da uba zasu su yi wa dan su, itace tsanin duk wani mataki dana ke kai a rayuwata yau.” Na ce “ni ba wannan ne damuwa ta ba Habeeby, karewa ma in don ta ni ta zo kenan bazata koma Jos ba, ko Allah ya sa watarana mu saka ta a hanyar gaskiya, na saba da rigimar tsoffi don Ummati ta fi ta rigima kuma a hannun ta na taso. Damuwata shine ka da ta kore min mala’ikun rahma dake daki na da wannan karatun nata da take yi don anan nake ibadodi na”, Hamzah ya yi dariya ya ce. “Lakum Deenu kum wa liya Deen” ayar Ubangiji ce wadda tun ban dandani zakin musulunci ba na san ta a bakin musulmai, bana jin zamanta da practicing addinin ta cikin gidan mu zai yi affecting din addinin mu da komai, Allah yana ko’ina kuma buri na shine watarana itama ta musulunta, ta dawo cikin hasken shiriya” nace “na yarda da kai, amma duk da haka bari inje in kwashe Alqur’anai na da kayan sallah ta daga dakin”. Na shiga dakin sadaf-sadaf kamar barauniya, har yanzu tana ta addu’a tana wani gyada kai kamar na kadangaruwa, na lallaba na kwaso Al’qur’anai na da carbi na da littafan addu’o’I na su Hisnul Muslim da su Alma’asurat, na kuma sauke frame na Ayatul kursiyyun don hankali na ya ki kwanciya in bar su a dakin. Na juya kenana zan fita sai naji muryar ta daga baya na tana magana cikin nutsuwa, kamar
Chapter 27 · 0% Book details