← Book details Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 30

Sashe 23

Sakacin Waye Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

don jinin sa ce, kuma bashi da wanda ya fita a duniya. Yau sati biyu kenan Kaka na masa rigimar yayi mata visa ta taho United States, a cewar ta, bata ce zata zo don ta raba shi da matar sa ba, amma ta gaji da zama ba tare da shi ba. Ta azabtu da rashin sa a kusa da ita. Tunda ya san shikadai ta ke da a duniya. A ranta kuwa ta kudire idon ta idon matar Mawonmase…. sai dai iyayen ta su haifi wata ba ita ba. Hamzah ya san rigimar Kakar sa sarai, bayan rikicin tsufa tanada rigima a kan karan-kanta, in bata son abu bata son shi, ta tsani musulunci da musulmai gata da kabilanci mugun gaske, don haka bai ga me zata zo ta yi a gidan sa ba banda ta tada ma iyalin sa hankali, suna tsaka da tasu ‘yar tsamar shi da Siyama, shi yasa yayi ta yi mata hanya-hanya har zuwa yau. Dalilin da yasa kenan duk sanda ta kira shi yanzu sai gaban sa ya fadi. To yanzun ma hakan ce ta faru, da ya ga sunan Grandma akan screen din wayar sa sai da gaban sa ya yanke ya fadi, gashi ba zai iya ignoring call din ta ba no matter what rigimar da ta zo da shi, tana da matsayin Uwa ne a gare shi ba na Kaka ba. Uwar ma ta musamman, wadda ta yi masa abinda ko mahaifiyar sa da ta kawo shi duniya bata yi masa ba. Sai ya gyara zama a kan kujerar dining din da yake zaune, sannan cikin nutsuwar sa ta halitta da sanyin murya mai ‘yar sassarfar nan ya amsa mata. “Woso Tyang GrandMa”. (Good evening Granma). Hamzah ya fara da gaishe ta cikin yaren Birom, amma ko kafin ya rufe bakin sa sai yaji tsohuwar ta rushe da wani irin kuka mai gigitarwa da rikita kwanya iyakar iyawar ta. “Mawonmase mace ta raba mu ko? Mawonmase yau ka zabi mace a kai na ko? Kusan shekara guda ban gan ka ba, ban sa ka a ido na ba, yau ni ce baka so in zo inda kake sabida ka auri mata Musulma?” Kaka ta fada da yaren Berom, sannan ta fyace hanci cikin kakabi da hargagin kuka tace “Oh Jesus! Inama Ezekeil (Baban Hamzah) ya dawo duniya yau, ya ga yadda Mawonmase ya juya min baya yau a kan mace!”. Hamzah ya shiga damuwa da rudun koke-kokenta, ya sauke numfashi a hankali, kirjin sa ya hau bugawa da jin irin kukan da take yi, yace “GrandMa, you know I love you koh? And I care for you more than anybody, me yasa kike tunanin mace ta raba mu, ko bana so ki zo inda nake? Ina da wadda ta fi ki ne duk duniya? Aiki ne kawai yayi min yawa, sannan mata ta mutuniyar kirki ce, mai kaunar ki, ki kwantar da hankalin ki da ita”. “Ba zan yarda da hakan ba sai na ganta da ido na, sai na kaita wajen Pastor David ya duba min zuciyar ta, ban yarda haka ta barka ba, don na yi mafarki kana karanta littafin su, I’m afraid Mawonmase kada ta ja ka kaima cikin addinin ta…!”. Hamzah ya runtse ido yana hango Malamar Musulunci (Islamic Scholar) kuma Hafizah Siyamah Mamman Gembu gaban Pastor David ana karanto mata ayoyin Bible a kan ta. Wani abu da ya san ko sama da kasa zata hade Siyam bazata taba yarda da shi ba, shi kan sa ta hakura da shi duk da son da ya samu labarin ta yi masa, lokacin data ji cewa shi ba musulmi bane ta hakura. Ko a cikin musulmai Siyama is Pious wato Aabidah ce (mai ibadah) wadda bata dauki addinin ta da sauki ba, bata kuma hada shi a muhimmanci da komai ba. Wannan kuma ya biyo bayan zuzzurfan ilmin addini data samu a (Daar Al Uloom Al Madaniyyah) kamar yadda ya samu labari a bakin Nasara. Shi yanzu sallahr ma kanta wuya take bashi, ya rasa me yasa, ba kullum yake iya yi ba, ko don kusan kullum sai ya shagiya ne yanzu? Idan yayi kokarin yi, sai yaji kasala da nauyin jiki sai kuma ya manta ya shiga sabgogin sa, yana mai cewa sai a hankali, a hankali din da bai san ranar zuwan ta ba, ita kuwa Siyam sai ta kwana tana yi bata gaji ba, duk wani bude ido ko juyi da zai yi cikin dare zai gan ta akan sallaya ko cikin sujjadah. Tunda ta daina yarda ta hada jiki da shi. A kan laifin da bai sani ba. Ajiyar zuciya Hamzah ya yi, sannan a kagauce cikin gajiyawa da tarin korafi irin na Kaka ya ce “Yanzu dai Kaka me kike so a yi?” Da sauri ta amsa “ka kawo ta Jos nace, nan Riyom, in kai ta wajen Pastor David yayi min bincike da addu’a a kan ta. (A ran sa kuwa ya san tarko ne Kaka ke son haka masa, muddin ya kai Siyama cikin ‘yan kabilar su suka kuma samu labarin ya musulunta a kan ta ba abinda zai hana su kashe ta, don kashe musulmai ba komai bane a wurin su). Data ga alamar wannan idea din bata samu karbuwa wajen Mawonmase ba sai ta canza. “Ko kuma ni ka bar ni in zo inda kuke ko sati biyu ne nayi na ga irin rayuwar da kuke yi, in tabbatar bata cuta maka, tana kula min da kai kuma bata ja ka cikin halaka ba!”. Ta cigaba da fyace hanci tana sheshshekar kuka tana cewa “Da Ezekiel yana raye (Dan ta, mahaifin sa) da ba’a yimin wannnan tozarcin ba, Mawonmase dana gama ginawa na gama shan wahalar sa da dawainiyar sa har ya kafu, shine yayi aure yau ba da yawu na da sanya albarka ta ba, kuma ya dinga gudu na bayan auren sabida ya samu jikin mace!”. Shi kunya ce ta kama shi a kan kalaman ta, ya ce “Kaka shikenan kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki, ki yafe mini in na bata miki rai ban yi da niyya ba, ki so mata ta don ina son ta sosai, ina kaunar ta Kaka, kuma tana girmama ki tun bata gan ki ba. Wani lokacin har cewa take in bata labarin zuwan mu gona, yadda muke yin shuka da girbin Cocoa, da yadda ake noman Irish, tana matukar so na Kaka, a dalili na ta bata da iyayen ta, tana min duk wani girki irin namu, tana son jin labarin rikice-rikicen kabilar mu na Riyom dana Berom Kingdom. Sau tari tana son jin yadda ake yin ‘Nzem Berom festival’ da….”. Kaka ta kara harzuka fiye da tunani. Jin ya tsinke da bata labarin matar sa cikin shauki na soyayyar da ga dukkan alamu bai san yana yi ba, kamar ya manta da wa yake magana. Kaka ta ce a ran ta, “Oh! Jesus have Marcy on my grandson, he’s been caught by an evil woman” (Almasihu ka yi afuwa ga Da na, shaidaniyar mace ta kama shi). Amma da yake so take ya bar ta ta je U.S, kota halin kaka, a fili sai tace masa “to shikenan, yanzu yaushe zan taho?” Hamzah yace “ki shirya zan turo a kai ki Visa Abuja, in an gama zan turo miki tikiti sai ki taho, it may take few weeks”. Daidai lokacin da ya kawo kofar dakin Siyam, sai ya kashe wayar ya saka a aljihun jamfar sa. Yana shiga dakin ina fitowa daga toilet, daure da tawul iya gwiwoyi na, wanka na fito na kuma wanke gashin kaina yana ta yararin ruwa, duk ya hautsine ya jike, yana bukatar in busar da shi da (hand-dryer) kafin na kwanta barci. Ina jin sa yana ta magana a waya amma ban san me yake cewa ba ko da wa yake maganar, kamar dai cikin yaren sa yake maganar, na dai tabbata daga shigowar sa zuwa yanzu ya ci abincin da na ajiye masa don a kan Gwaten Acca baya da fulako. Ido muka hada ni da shi ta cikin hasken kwan lantarkin da ya dallare dakin nawa kamar rana, ga mamakin sa, abinda bai taba zato ba, ‘yar far’a na saki na ce da shi “sannu da zuwa” amma ba tare da na dago na dube shi ba. Saidai na cire kalmomin nan guda biyu ‘Shaheed’ ko ‘Habeeby’ da na ke kiran sa da shi a lokutan mu na dadi. Wasu sunaye da yafi son ji daga bakin Siyama koda cikin fushi zata fade su, sunaye ne da ya rabu da ji daga bakin Siyam din sa kwana da kwanaki, so he missed it. Rabon da in ce masa sannu da zuwa ma ba zai iya tunawa ba. Shigowa ya yi cikin dakin yana taku a hankali zuwa gare ni, hannayen sa duka biyu zube cikin aljihun wandon jamfar sa, kallo daya nayi masa naji tausayin sa ya kama ni, domin na ga ya fada sosai na alamun rashin kwanciyar hankali da nutsuwa a tare da shi, sai karan hancin da ya kara tsini, ya tafi dodar ya tsaya a tsakiyar kyakkyawar fuskar sa. Almond - shaped eyes din sa, sun yi ciki sosai, sun dan kada, launin su ya canza zuwa brown, wannan dan sannu da zuwan da ya samu daga baki na yau, shi ya bashi kwarin guiwar isowa gare ni. Hannun sa yasa yana taba jikakken gashin nawa, ba karamin sha’awa gashin nan yake bashi ba, ga santsi, ga laushi ga baki da tsayi sannan Siyam bata wasa da gyaran sa, da lallashi a muryar sa yace “where’s your dryer? Can I help you with this (ina abin busar da gashin ki, zan iya taimakawa da wannan?) Yana nufin yana so ya busar min da gashin da kan sa”. Fuska ta ba yabo ba fallasa, zuciya na son tuno min da kalamansa na jiya wadanda koda ya kasance cikin maye ya furta su, na san yana nufin su har zuciyar sa amma ya zanyi tunda ni na saya aka sayar min dole in karba, da hannu na nuna masa inda take ajiye, ina mai kai zuciya ta nesa, ina kawar da kai daga duban sa. Sai Hamza ya ja hannu na zuwa kan stool din mudubi, ban
Chapter 23 · 0% Book details