Sashe 9
Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sukaita jayayya hakan yasaka Abba tara dukkan mutanan gidan adaren amma kowa yace bashi yad'aukaba, Abba ransa ya'baci, yacrr kowa yaje har ita Auntyn yace takoma d'akinta, baya bu'katar kowa.
nan da nan Momyn Haby ta lalla'ba tashiga d'akin nasa, mai tace masa oho, sai gashi ya fito yanufi d'akin Aunty, yana zuwa yahau bincike, Aunty tayi tsaye tana kallon ikon Allah sai da yahargitse d'akin baki d'aya, har zai fita sai kuma yakoma yad'age katifar gadonta sai kuwa ga kud'in.
Aunty tayi tsai tana kallon ikon Allah, tana tunanin yanda akai,kud'in yazo d'akinta,kuma,'kasan katifarta.
Abba kuwa tsareta yayi da idanunsa, yanayi mata kallon tuhuma, Aunty tadur'kusa tana mai neman yafiya da fad'in ba ita tad'aukaba, asalima batasan yanda akai suka zo d'akiinba, Abba jin zancen nata kawai yake kamar rainin hankali, hakanne ya'kara fusatashi yace gobe da safe taje gida kawai.
Momyn Haby na la'be tanajin dukkan abinda yafaru, tayi dariya aranta tana fad'in “kad'an kika gani, ingama dake kafin inkoma kan uwar gijiyar taki wato Mama”
gari nawayewa Aunty tanufii gidansu, har tsawon wata guda Abba yawatsar da lamarinta, Mama da Ammy sunje har gidan nasu Aunty bata ha'kuri, amma Momyn haby ko le'ke, hakan yasanya jikin Aunty yin sanyi da al'amuran Momyn haby.
sai da Abba 'karami yasanya baki, yaje kuma yahad'oshi da Yayan Innarsu, sannan Abba ya dawo da Aunty, lokacin watanta biyu a gida.
tun da tadawo tafita hanyar Momyn Haby, Aunty tabaiwa Mama ha'kuri suka koma kamar da abinsu suka aje Momyn haby a gefe.
Wata ranar alhamis tunsafe da Abba 'karami yatashi yake fad'in baya jin dad'in jikinsa, gashi kuma zasuje d'aurin auren wani amininsa zai sake aure matarsa tarasu, Ammy ce tad'inga 'karfafa masa gwiwa duk da itama bawai dad'in take jiba, daurewa kawai take, da 'ker yasamu yafita, kafin yatafi dawowarsa uku, sannan yatafi adaddafe.
'karfe biyun rana sai ga ambulan a 'kofar gidan, motar Abba na biye da su, cikin gidan Abba aka shiga da gawar Abba 'karami dake lullu'be da farin yadi, mintuna biyar da shiga sai ga Ammy tashigo ko mayafi babu, tana fad'in, anuna mata mijinta tasan ba mutuwa yayiba, kowa yacika da mamakin wanda yasanar da ita, domin ance kada afad'a mata, basuyi auneba sai ganinta akayi ta zu'be 'kasa jini ya 'balle bashiri sai hospital, ana zuwa akayi ciki da ita, doctor yadawo yasanarwa Abba sai dai ayi operation aciro abinda yake cikin domin zai iya rasa ransa, nan da nan Abba yasanya hannu.
mintuna goma sha biyar sai ga nurse d'auke da jaririya kyakkyawa, Mama takar'bi jaririyar tana tambayar “Ammyn tana lafiya kuwa?” nurse tace “ yanzu itama za'a fito da ita tana nan lafiya”
Ammy data dawo haiyacinta,babu abinda take sai kuka, har dai idan takalli jaririyar data haifa sai zuciyarta takarye tausayin yarinyar yakamata.
har akai sadakar bakawai Ammy na hospital yawanci idan anzo gaisuwa sai kuma awuce hospital dubiya, ranar da jaririyar ta cika kwana bakwai a duniya Abba yace Ammy dakanta zata za'bi sunan da za'a sanya mata, nan take Ammy tace “NURATU”shine sunan da take so, Abba yasanya mata kuwa.
Haka Ammy tad'au ha'kuri da dangana tasanyawa ranta, ta tsaya kai da fata wajen rainon marainiyar jaririyarta.
shekarar Nuratu guda aduniya ya Nura yazo hutu gida, tun da yazo yatarar anhaifi Nuratu, ko d'aukanta bai ta'ba yiba, asalima yakanji yatsani kallon yarinyar, amma yarasa dalilin hakan, bayan tunda akayi masa waya akace anyi haihuwa yake Allah Allah yazo gida yayi 'kanwa, amma yarasa mai yasa,ko kallon yarinyar bayasonyi yanzu, bayan yana ganin mutane da dama kowa da yaga nuratu shidai burinsa yad'auketa amma shi banda shi.
wata shida yayi yakoma sannan Mama Allah yataimaketa da shigar ciki, shekarar Nuratu biyu a duniya Mama tahaifi NANA, bayan shekaru biyu kuma ta haifi 'yan biyu sune RAHMA da SAlisu sunan malam suke kiransa HILAL.
Har lokacin Aunty ko 'bari batayiba, hakama Momyn haby, kullum sai 'karyar zubewar ciki.
Nuratu ta girma,Nana da shekaru biyu, sannan Nana ta girmi su Hilal da shekaru biyu.
yanzu tsakanin yaran Nuratuce babba shiyasa suke binta da duk abin da tace dasu
tun tasowar Nuratu yarinyace mai rigima, ga uwa uba tsokana da rashin ji, wanda ada suke ganin yarintace kawai zata daina, amma har ayanzu da Nuratu takai shekaru takwas aduniya, mai makon abin yaragu saima 'karuwa kawai da take.
Tunda ya Nura yakoma bai sake zuwaba sai bayan shekaru uku yazo yayi wata biyu yakoma, a wannan zuwan su Nuratu sunci kwakwa, domin da ahoto kawai suka sanshi, basu zaci haka yakeba, shiyasa da yakoma sukayita addu'ar Allah yasa kada yadawo.
Da Khaleel suke d'asawa, domin shi babu ruwansa duk abinda sukace hakan za'ayi, shima kuma Abba yad'aukeshi yaturashi karatu, ranar su Nuratu ansha kuka, kamar ance idan yatafi bazai dawoba.
Dama can a gidan basa shiri da Kamal da Habiba, Haby cema indai zasu had'u da Nuratu saii anji kansu, acewarta tatsani yarinyar.
wannan kenan shine ASALIN NURATU
yanzu zamu koma ASALIN LABARIN
[30/11/2017, 22:18] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈QIYAYYA SA GANIN LAIFI🌈🌈🌈Book 1
Mallaka.......QURRATUL-AYN
12
MU KOMA BAYA
【】【】【】 【】【】【】
Ya Nura yad'ago kansa daga kwanciyar da yayi, yadubi Khamis yana mai fad'in “ba'kanwa tabace, da ita mahaifiyarta tazo gidan nan”“ohh kacemin agolace dai kawai”Khamis yafad'a yana dariya, bai jira mai Nura zaiceba yad'ora da fad'in “nidai shawara agareka kawai kayi biyayya da abinda iyayenka suka za'ba maka”Ya Nura yayi murmushi “biyayya ai tazama dole, ko dan murabu lafiya”
Khaleel zaune falo, yayin da su Nuratu suka kewayeshi sunata faman zuba masa surutun da suka saba, Nuratu tace “yanzu ya Khaleel mai kaje ka karanta ne? dan kasan nidai bana son aikin soja wallahi natsani sojoji”Khaleel yayi dariya “Nuratun Ammy kenan, ni doctor na karanta, amma mai yasa bakyason soja?”Nuratu tad'an ta'be baki “kawai dai natsanesu domin mugwayene azzalumai har dai wannan Yaya Nuran na.....”bata 'karasa maganartaba taji anbuge mata baki, Nuratu da sauri tami'ke tsaye taganshi tsaye kansu kamar mala'ikan mutuwa, murgud'a baki tayi tana fad'in “Allah ya isa mugu”tawuce d'akin Mama da gud yabita shima, amma kafin ya kai harta kulle 'kofar.
ya Nura yadawo ransa a'bace yana duban su Nana dake zaune, wata uwar tsawa yawatsa musu, wadda tasanya Rahma sakin guntun fitsari awando “ubanwa kuke kallo kuna muzurai, kosaina 'ba'b'ballaku kuma, tashi kumar falon nan”da gudu suka mi'ke suka fita, Nana ce aka d'an barta abaya, sabida 'kafarta da haryanzu d'ingisawa take.
Khaleel yad'anyi dariya yana mai fad'in “ni kuwa broda al'amarinka da Nuratu nabani dariya, kasan halin Nuratu sarai, amma kadinga shiga shirginta, Nuratu nada sau'kin kaifa kuma bata da raini, idan kaga tayi wad'annan abubuwa biyun to shiga hanyarta akai”Ya Nura yajefi Khaleel da wata irin harara yayi kwafa yana mai fad'in “to babanta, ai na fahimci ma komai yarinyar nan keyi da had'in bakinka, idan ba hakaba mai yasa zaka sasu gaba tana zagina kanaji”Khaleel dariya yasakeyi karo na biyu yana mai girgiza kai “broda kenan, dad'ina da kai d'aukan zafi, yanzunan har wani abu tafad'a dazai 'bata ranka abanza”Ya Nura yakalli Khaleel kawai yad'auke kansa, bai kuma tanka masaba yafice, domin jiyayi maganganun Khaleel d'inma sunfi na Nuratun 'kona masa rai.
Wasa-wasa dai sai ga soyayya na'kulluwa tsakanin Ya Nura da Haby, wadda kowa yake mamakin hakan, amma awajen Abba yaji dad'in hakan sosai, Mama da Aunty nema suke shakka akan son da Nura ke nunawa Haby ahalin yanzu, domin soyayyar tana so tayi yawa, hakan yasaka Mama du'kufa da yimasa addu'a sosai, a'ban garan Haby da Momynta kuwa sunfi kowa murna da hakan, ji suke tamkar burinsu ya gama cikama tun ahalin yanzu.
8:40pm
Zaune yake cikin gaiden, kan had'addaan carpet ma dai-daici, ga kayar fruit cike agabansa, sanye yake da blue d'in jeans, mai ratsi irin kayan sojoji da farar t.shert gaban rigar anrubuta MEGA POWER STAR da ba'in rubutu, wayace ahannunsa yake daddan nawa, gefe guda kuma Haby ce zaune kusa dashi, tana yanka masa Apple, taci ado kamar wadda zataje gasar kyau, domin babu laifi Haby itama nada kyawunta dai-dai gwargwado, gata ma'abociyar son make-up ce sosai, da shiga takece raini, yanzuma riga da siket ne ajikinta, na wata super koriya mai ratsin fari da ba'ki, abinka da farar mace duk da dai an'kara da mai, atamfar tayi mata kyau sosai, gaban rigar kamar da tayi kwakw-kwaran motsi albarkatun 'kirjinta zasu fad'o waje, ciket d'in kuwa kamar kad'an yake jira ya yage tsabar kamata da kayan yayi, tayi d'aurinnan da ake kira gobarar mata, wanda da dukkan alamu yazamewa haby jiki, domin d'aurin d'ankwalinta kenan kodan tafahimci yanayi mata kyaune oho, fitilun dasuka haske wajen sune suka 'kara 'kayata wajen da kyau.
matsowa tayi kusa dashi har jikinsu na d'an gogar juna, tasanya masa apple d'in dai-dai bakinsa yana ci ahankali tamkar baya so, ya juyo kad'an ya dubeta sai kuma yayi saurin d'auke kai yana fad'in “mai yasa kikeson irin wannan shigarne?”tad'anyi farr da ido kafin tace “naga hakan ba illa bane, kuma aikai zan aura, menene dan nayi maka kowacce irin shiga?”Ya Nura yatsareta da mayun idanuwansa yanajin wani abu nafizgarsa, hakan yasanyashi d'auke idonsa daga dubanta yana mai fad'in “ai yanzu baki zama matar tawaba tukunna, kijira a gidana sai kidinga yimin, kinsan ina da kishi sosai ko? ”Murmushi tayi mai jan hankali, wanda yakusa sumar da ya Nura, takamo hannunsa tasanya anata tana murzawa kad'an-kad'an “zankiyaye insha Allah Dear”jin dayayi kamar tana neman tafiya da wani 'bangare na jikinsa, yasanyashi janye hannunsa ahankali, yad'auko ayaba yakama ci, yana mai 'ko'karin mai da numfashinsa.