Sashe 7
Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“naji dad'in tarbar dana samu agareku Malam, abinda banyi tunaniba, duk da nasan irin karamci na zur'armu, nayi tunanin zaku tambayeni tun ajiya, amma sai naga,kunyi kawaici ha'ki'ka naji dadi, wannan ba kowa bace illa Amina, Amina balarabiyace danginta kaf larabawane na had'u da Amina tunfarkon zuwana saudia, ta nunamin so da kauna tsan-tsa, tare da iyayenta,asalima agidansu nazauna, har zuwa kammala karatuna, munsha'ku da ita sosai Malam, sai dai iyayenta sun nuna bazata biyoni nugeria muyi aureba sai dai ni inkoma can na aureta, duk yanda naso infahimtar dasu bazan iya rabuwa da kuba da mahaifata sungaza fahimtata, nafad'a musu koda natawo da Amina nigeria hakan bazai saka nakasa kai musu itaba, amma sun'ki yar da, nayanke hukuncin rabuwa da ita, amma sai abin yazama illa agareta har ciwo takwanta, ana igobe zantawo kwana tayi tana kuka Malam, ganin hakan yasaka mahaifinta ya yarda mutawo da ita duk da dai,mahaifiyarta ta'ki yarda, amma akan sharad'in duk shekara zamu dunga zuwa da ita, da dai kamar bazan aminceba, amma sai tausayinta yakama ni har dai na amince da hakan, yanzu dai Malam gani gareka duk abinda kayanke akaina ni mai biyayyane”
kowa yayi shiru haka falon yad'au shiru, illa kukan Amina dake tashi, wadda duk wanda ya lura da ita tun da suka zo kukan take, ba fahimtar abinda ake fad'i takeba, amma tasan fad'a ake, magana ake akanta, hakanne yasaka kukanta 'kara sauti, gani take kamar bazasu aminta da itaba, kafin Malam yace wani abu, Abba yarigashi da fad'in “malam kuyi ha'kuri kukar'bi Amina matsayin 'ya agareku, ha'ki'ka Amina taso Auwalu tayi masa halaccin da ba du macace zatayiba, ta nuna masa so wanda da wuya yasamu wadda zata soshi tsakani da Allah haka, sannan ina ro'kon masa, afuwa idan har yayi laifi”falon yasake d'aukan shiru, kafin Malam yayi gyaran murya yana murmushi yake fad'in “ai babu abinda zamuce illa fatan alkhairi kawai, Auwalu baiyi laifin komaiba agare mu, illa yayi 'ko'kari yadinga cika al'kawarin daya d'aukowa iyayen Amina”yayi shiru yana d'an tari, Inna tace “gaskiya nayaba da nutsuwa da hankalin yarinyar, na amince Auwalu ya aureta Allah bada zaman kafiya da zuri'a,tagari”“amin” suka amsa, kafin Malam yace “babu wani 'bata,lokaci nan da sati biyu masu zuwa insha Allah za'a d'aura auren Auwalu da Amina”😁
[27/11/2017, 22:10] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈QIYAYYA SA GANIN LAIFI🌈🌈🌈Book 1
MALLAKA......QURRATUL-AYN
10
(kuyi ha'kuri abisa yanda nake baku labarin ASALIN SU NURATU inshort ina fatan hakan bazai bada matsalaba zaku fahimce ni nagode sosai NURATU FANS😘)
RANA BATA 'KARYA
Kamar yanda Malam yafad'a, sati biyu na zuwa ranar juma'a bayan saukowa daga mallaci aka d'aura auren Auwal da Amina, ta tare itama awasu d'akuna dake cikin gidan nasu, Amina taga so da 'kauna daga d'angin Auwal, babu tsangwama bare nuna ban banci, ta zauna cikin so da yarda da aminci, kamar yanda Malam da Inna suka d'auketa matsayin 'ya agaresu, ita batayi 'kasa agwiwaba wajen yimusu biyayya.
BAYAN SHEKARU UKU
Hafsa na da shekaru uku a duniya tayi wayo sosai tana yawonta ko ina, gata da surutu tubarkalla, bakinta yafara bud'ewa ne da kiran Mama da Abba.
Ranar wata laraba aranar ciwon malam yatsananta sosai, amma duk da haka yana daure yatara dukkan iyalensa, yayi musu nasiha mai ratsa jiki, da yanda kowa zai zauna da duniya lafiya, Abba yaso akaishi asibiti amma Malam ya'ki yanuna lafiya 'kalau shi dai yake.
kwana biyu dayin hakan ranar juma'a da asuba Malam yace ga garinku nan, mutuwar malam ta girgiza al'umma da dama bama iyalensaba, Amina tayi kuka tamkar mahaifintane ya mutu, ko dayake mahaifin tane mana, tunda shine yahaifi mijinta.
haka aka had'a Malam domin kaishi gidanshi na gaskiya, iyalensa sunyi kuka sosai, har akayi sadakar bakwai mutane na zuwa gaisuwa sai sati biyu da rasuwar sannnan 'yan jigawa suka koma gida.
Ranar da Malam yacika kwana arba'in da rasuwa, ranar Mama tatashi da wani irin ciwon ciki, wanda tun tana daurewa sai da aka nufi asibiti da ita, ana zuwa sukace na'kudace, kowa ya cika da mamaki da murna, domin babu wanda yata'ba tunanin da ciki atare da itama,bare kuma labarin haihuwa, kowa addu'ar sauka lafiya yahauyi mata.
sai da tashafe kusan rabin awa da kawota asibitin sannan tahaifo d'anta namiji mai kama da mahaifinsa, aka wanke yaro sannan nurse tayo waje dashi, Abba yacika da murna sai godiya yakeyiwa Allah, amma murna babu kamar Auwal dayakeji kamar shi akayiwa haihuwar, sai da aka gama gyarata sannan aka kawota d'akin hutu, sai lokacin su Abba suka samu damar ganinta akahau yimata sannu.
kamar akan yaron aka fara haihuwa ranar suna yaro yaci suna NURA, babu irin fad'an da Inna batayiba akan bai mai da sunan Malam ba, sai da 'kyar taha'kura shima sai da yace mata malam dakansa yabar wasiyyar sanya sunan Nuran sannan aka samu lafiya.
yaran suntaso cikin gata da so da 'kauna, har dai Amina tanason yaran kamar tahad'yesu, musamman Nura yyatone mai shiga rai, domin kusan kayansama d'akinta suka koma, ita keyi masa komai
lokacin bakinta yafara gogewa da yaren nan 'kasar wato Hausa, daman gata da son al'adun nan, wajen shiga da irin girke girkenmu da dai sauransu, hakan yasaka komai baya yimata wahalar kowa, kasan ance duk abinda kake so, bazai baka wahala wajen koyaba.
BAYAN SHEKARU BIYAR
“haba Ammy, kidaina zubda ha
wayenki akaron banza, haihuwafa ta Allah ce, ni da Allah yabani yara,biyu aiba cemiki akai yafi sona dakeba, dan Allah kidaina wannan kukan, a gidannan akwai mai miki ba'kar magana kan haihuwane ?”cewar Mama kenan, dake zaune tare da Amina tana aikin kuka, da yake yanzu Nura da Hafsa sun sanya mata Ammy, hakan yasa kowa na gidan ke kiranta da hakan.
Ammy ta goge kwallar dake gefan idonta ta dubi Mama “ba
wai ina fushi dayin hakan bane, yaufa shekara takwas kenan da aurena babu ko da 'batan wata, haka kawai nakeji araina ina son nahaihu kodan insamu maiyimin add'a, tunda banda ku yanzu bani da.....”sai kuma tayi shiru, Mama tatsareta da ido kafin tace “naji koma dai menene kifauwalawa Allah dukkan lamarinki, kimai da komai ba komaiba, sai kiyita addu'a sai kiga komai yawuce yazama labari”Ammy tashare hawayenta tana fad'in “nagode sosai da shawaranki agare ni”shigowar Nura da Hafsa shine yayi sanadiyyar yin shirunsu, suka hau wata hiran domin basaso yaran sufara sanin damuwa tun suna yara.
“nidai kam yanzu jigawa nake son komawa, inyaso duk mai son ganina yaje can, akan me kuke son rabani da mahaifata?”fad'in Inna kenan dake zaune saman kujera, yayin da su Abba ke zaune 'kasa a gabanta, Abba ya girgiza kai yana fad'in “bawai zamu rabaki da mahaifarki bane Inna, amma idan kin koma can aibazamuji dad'iba, muna son zamanki anan sosai Inna”Abba 'karami kamar yanda su Nura ke kiransa yakar'be da fad'in “ki daiyi ha'kuri Inna, kizauna damu zamufi jindad'in rayuwa tare dake”wata harara Inna tawatsa musu da fad'in “wato kunfi son ganin 'bacin raina ko akan kufarantamin”ta'karashe maganar tana mai fashewa da kuka, hakan yasaka hankalin su Abba tashi baki d'aya, nan da nan Abba yace tashirya sukaita babu komai, su dai addu'arta suke bu'kata, sai sannan tahau sanya musu albarka, aranar Abba 'karami ya aike da kud'in siyan gida madai daici, yasaiwa Innarsu, da yake shima yanzu babu laifi arzi'ki yabud'e masa, domin shine headmaster nawata makarantar islamiyya private ce, nan da nan aka yiwa gidan d'an gyararraki, akayi fenti da yamma kuwa suka kaita jigawa ta tare agidanta, basu baro garinba sai da suka ajiye mata dukkan wani abu dazata bu'kata, Suwaiba tayi murna sosai jin cewa Inna tadawo jigawa, yanzu kewa tad'an kau aranta, tun da haryanzu Allah baibata haihuwaba, har mijin nata ya'karo aure ma wata mace mai kirki mai suna Jamila, suna zaman lafiya abinsu domin tana baiwa Suwaiba girmanta yanda yakamata, haka itama Suwaibar tana jan girmanta.
“wai har yaushe zaki barni incika al'kawarin dana d'aukowa iyayenki da Malam, Amina?”fad'in Abba 'karami kenan yana mai kai cokalin abincin daya d'ebo bakinsa, Ammy tad'anyi ajiyar zuciya “bawai na'ki barinka kacika al'kawari bane, kasan cewa idan har zanje gida ayanzu tabbas sai dai kadawo batare da niba, domin kuwa indai zanje batare da ciki ba ko d'a tabbas aurena dakai yazo 'karshe, ni kuwa bana son abinda zai rabani da kai”tayi shiru jin kukan datake 'ko'karin 'boyewa zai fito, Abba 'karami yayi ajiyar zuciya, “ki kasani ko yanzu su sauya ra'ayi akan hakan?, yau shekara takwas kenan amma duk shekara sai Yaya yayi batun tafiyar taki, har yafara ganin laifina, gani yake nasan illar rashin cika al'kawari amma ina takewa, har cewa yake idan kud'in tafiyar takine babu shi zai biya, to mai kike so ince mai kuma Amina?”Ammy tagoge kwallar data kawomata, “nidai kayi ha'kuri, karo na farko arayuwa zanyi maka musu, bazanje gidaba, domin bana son rabuwa da kai”Abba yayi shiru yana dubanta, shima bawai yana son rabuwa da ita bane, amma yana ganin kamar yana tauye mata ha'k'kine, ruwan data zuba masa mai sanyi yad'auka yasha dayake ana zafi agarin, sannan yace “shikenan bazan takuraki ba, amma zamuje dake kifad'awa Yaya dukkan abibda kika fad'amin, domin bana so Yadinga kallona da laifin tauye maki ha'k'ki”Ammy ta gyad'a kai alamun to.
SHEKARU BIYU
cikin shekarun abubuwa da dama sunfaru, ciki kuwa har da 'karuwar arzu'kan da Abba da 'kaninsa suka samu, domin kuwa Abba 'karami harya sayi filin dake gaban gidansu, yayi gini ma dai-daici amma kuma gidan mai kyau sosai, ya tashi daga cikin gidansu suka tare asabon gidan, Abba yayi murna sosai domin su 'yan uwane da basa kyashin samun 'yan'uwansu, suna so ace nasu ya cigaba sosai, Abba ma ya gyare gidan sosai, lokacin Hafsat nada shekaru goma aduniya yayin da Nura ke da shekaru bakwai, domin ta girmashi da shekaru uku idan baku manceba.