← Book details Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 23

Sashe 21

Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khamis yad'an muskuta yafara magana"nayi maki al'kawarin binciki ko halin da Master yake ciki idan baki manceba?" "ehhh inajinka" tafad'a a gaggauce, alamun ta matsu taji labarin.
Khamis yacigaba da fad'in " tabbas nasamu labari akan hatsabibiyar matarsa, dukkan halin da Master yake ciki to Habyce silar jefashi, kafinnan yakamata ma kisan wacece Haby" yad'anyi ajiyar zuciya, ya cigaba da fad'in " shekaru uku kenan bana 'kasarnan, naje malesia batare da Master yasan inacanba, acan naga abin mamaki, idan baki manceba kinsan 'kawayen Haby ai? ZULY da BABY, to sudai bansamu wani labari akansuba, amma suma suna can malesian, sai dai abinda nafahimta Master baisan suna 'kasarba, dalilin daya sanya nasaka ayar tambaya akansu kenan, amma Haby yanzu tana fita 'kasashen waje sosai, london india america germany da dauransu, har nan nigeria tana zuwa da sunan business, amma a sirrance kinsan mai takeyi?" Aunty Hafsat ta girgiza kai "hayar Haby ake akan naira million guda, ga duk wanda yabu'kaci yin harka da ita, tana bin manyan alhazaine, da kuma hajiyoyi" "subhannallah" Aunty Hafsat tafad'a, "kacemin dai Haby mazinaciyace tsan-tsan kuma maci amana,to amma mai takeyiwa hajiyoyin?, shine abinda ban fahimcekaba" Khamis yad'auki cofin lemon daya aje d'azu yad'ansha kad'an, ya ajiye cike da murmushi yace "lesbian mana" "les...me..!?, kace Haby tagama 'kazanta, subhanallah, to yanzu ina cikin dayace tana dashi tahaihune?" Aunty Hafsat tasake tambaya "a'a ai ahalin yanzuma babu ciki agidansa bare kuma d'a ko 'ya" "zubewa yayi to kome?" wannan ne bansaniba, amma nima haryanzu bangama bincike akantaba, mutum d'aya nake nema shine kad'ai zai iya gayamin dukkan sirrinsu da kuma wacece ita kanta Haby d'in, shine Nabeel, to amma su kanshi nemansa suke basu ganshiba har 'kungiyarsu nemansa take"
"wace irin 'kungiya kuma?"
Aunty Hafsat ta tambayeshi, Khamis yace "ai duk abinda Haby keyi 'kungiyarsuce tasanyata, domin sunshiga wata 'kazamar 'kungiyane kawai sabida kud'i, shi kanshi Nabeel d'in Haby tayi harka dashine da umarnin 'kungiya domin wasu biyan bu'katu nata, haka shima Master 'kungiyar amfani take dashi sosai, don biyan wasu bu'katunsu" shiru falon yayi inbanda 'karar famka da AC dake tashi, sai 'karar tv kad'an-kad'an dake kunne, Aunty Hafsat tayi ajiyar zuciya kafin tace "wato dai Haby tazarce dukkan inda tunani zai kai, atunanina bokaye takebi, ashe ita mai gaba d'aya takeyi, da sake wallahi, amma baka tubanin Momynta tasan komai?"
"babu abinda Momynta tasani akanta, asalima Momynta koda gidan boka bata ta'ba zuwaba dasunan wai mallake wani, tana amfanine kawai da makirci, aganinta iya wannan ya isa agun mace, indai tasan kanta, abinda Momy kawai takeso kud'i, akan wannan tarbiyar tad'ora Haby, gashi yanzu tazarce inda take tunani, 'kungiyarsu na sirranta abu fiye da tunanin mai tunani, nikaina ba'karamar wahala nashaba akan samin wannan d'an labarin kawai, duk 'kasar da Haby taje ina biye da ita, nasaka aka had'amin layin Zuly da nawa, bayan nayi basajar had'ata da wani abokina amtsayin zasuyi harka dashi, ta wannan haryar nasamu numberta, to kinji yanda akai"
Aunty Hafsat tace "to yanzu ina kake ganin zamu sami shi Nabeel d'in?"
"ehh to gaskiya wannanne bansaniba, amma inanan ina bincikarsa, ya'buyane sabida 'kungiyarsu Haby domin lokacin cika aiki yayi akansa, bansan ya'akai yagane sirrinsuba shima, domin shi kanshi baisan suwaye suba" "to Allah yakyauta yashige mana, su kuma Allah yatona asirinsu, yanzu haka nasanya anata addu'a, Baffa yatabbatarmin nan da d'an lokaci zamuga Nura acikin gidanmu" Khamis yace "amin Allah yasa, Allah tabbatar mana" suka amsa da "amin" dukansu.
[10/01, 21:32] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book 1

mallaka-----QURRATUL-AYN

28

"amin" suka amsa baki d'ayansu, suka cigaba da tattaunawa akan matsolin Ya Nura da Haby, kafin su kama hiran duniya kuma, Aunty ke tambayar Khamis shi yaushe zaiyi aurene? Khamis yad'an sosa 'keyarsa yana fad'in
"aini baki d'aya aure yaficemin araima Aunty, badan raya sunnaba danace naha'kura, amma ina ganin kezanbawa za'bin matar da zan aura, danni yanzuma tsoron Matan nake" suka sanya dariya Aunty tace "Allah shige mana gaba dai" nan sukaita hiransu, har Hamza yasauko shida d'ansu Hameed aka cigaba da hiran dashi, nan Khamis ya wuni, kafin yayi musu sallama yatafi, tare dayiwa Aunty al'kawarin duk halin da ake ciki zata jishi, ko da awayana.

《MALESIA》

HABY, ZULY, BABY, SHOLY, Zaune suke cikin wani dan'kareren falon, wanda kallo d'aya zakayi masa kasan naira tayi kuka acikinsa, falon shiru kai kace babu wasu halittu aciki, inbanda 'karar fanka da AC dake tashi kad'an-kad'an.
Haby tayi ajiyar zuciya tana bin dukkansu da kallo kafin tace "Ina cikin damuwa sosai, narashin sanin inda NB yake, tsawon watanni uku kenan ko labarinsa babu, gashi 'kungiya ta matsa akan anemoshi, yanzu ni INA ZANGANSHI?"
Zuly ta tauna cimgum d'in bakinta yaba 'kara 'kasss, ta sauke 'kafarta daga karkad'a tan da take kafin ta gyara zama tana fad'in
"abin da mamaki kuwa, domin Nabeel baya tafiyar kwana guda batare daya sanarmana ba, amma bakwa tunanin yagano sirrinmune?"
Sholy ta zu'ki shisha da 'karfi tafurzar da haya'kin yabi iskar wajen yabaje, ta dubesu da fad'in
"mai yasa kuke da saurin karaya da tsorone, kunmance ko da Nabeel yagane komu suwaye, ya kuma gane sirrinmu, 'karyarsa yatona asirinmu"
Haby tace "hakane, amma kinsan dolene mudamu, domin saura sati guda agudanar da aiki akansa, wanda shine cikar dukkan burinmu"
Baby da tunda suka fara magaba bata sanya bakiba, ta dubesu cikin yau'ki, kamar ana mata dole akan magana, tace "ni kuwa ga shawara, mai zai hana murabu da wani batun Nabeel, musamo wani mana, sai kace SHI KA'DAINE NAMIJI?"
Zuly tace "hakane mubi shawarar Baby kawai, aha'kura da aikin yanzu har anemo wani da zai maye gurbi Nabeel"
Haby tace "to taya 'kungiya zata yarda da wannan batun?"
Sholy tasanya dariya tace "kinji halin naki Haby, saurin karaya da tsoro, kece zaki sanarwa 'kungiya komai, domin 'kungiya naji dake kuma anajin maganarki sosai"
Baby tace "kwarai kuwa, ko kinmance Haby kece first lady acikin 'kungiya?"
Haby ta girgiza kai tana dad'in "to shikenan, amma kunsan burinmu bazai cikaba nawannan shekarar, tunda anfasa aiki da Nb, sai dai zuwa shekara mai zuwa,idan ansamu wani"
"ehh to meye aciki, mutara wata shekar mana"

cikin had'a baki suka baiwa Haby amsa.
(kunjifa kai kace sune da rayuwarsu, sun tabbata zasukai anjima ma bare gobe zuwa shekara mai zuwa, Allah kasa mufi 'karfin zukatanmu amin).

Nan Haby da Sholy sukawaisu Zuly sallama suka nufi gida.

*****BAYAN WATA 'DAYA*****(After 1mnth)

《NIGERIA》
***KANO***
Bayan sallar maghriba
Kekenapep ne yayi parking adai-dai 'kofar gidan, Baba mai gadi dake zaune bisa binci dake wajen ya'kurawa napep d'in idanuwa, domin ganin wanda ke ciki, ya ziro 'kafafuwansa yafito, fuskarsa sanye da farin glass, yana sanye da kakin sojoji a jikinsa, ya rataya jakar systerm d'insa, Baba mai gadi yayi masa 'kuri da idanuwa yanayi masa kallon sani, ya zaro wallet d'insa ya d'auko d'aya daga cikin kud'in wallet d'in yami'kawa mai napep, mai napep yayi murmushi yana fad'in
"yalla'bai bansan wannan kud'in bafa" murmushi shima yayi kafin yacw mai "kaje ka canja, wannan guda d'ayan amatsayin dubu ashirin da biyu take, idan kacanja kad'auki dubu goma nabar maka dubu sha biyun kai kayimin sadaka, idan kana tunanin cutarka zanyi kuwa, kaga inda ka ajiyeni dai, nanne idanmu mazo zanbaka irin kud'inku nanan, yanzu banida canjin nigeria ne, wannan kud'in malesia ne" mai napep yawashe baki, yana godiya yakar'ba yayi gaba.
Baba mai gadi yataso da gudu yana fad'in "sannu da zuwa yalla'bai, ai ban shaidaka bane wallahi, sai da naji kayi batun malesia, fatan kazo lafiya?, gida kowa nacike da kewarka"
ya Nura yace " lafiya 'kalau" Baba mai gadi yakar'bi jakar systerm d'in suka nufi cikin gidan.

lokacin kowa nazaune falo suna hira, suka tsinkayi sallama bakin falon, kowa yamai da kallonsa bakin 'kofa, ganin wanda yad'aga labulen ya shigone yasanya duk mutanan dake falon mi'kewa tsaye cike da kad'uwa suka furta
"NURA....!"
Ya Nura ya'karasa cikin d'akin, yaje yarungume Mama siraran hawaye suka ziraro bisa kuncinsa, ganin hakan yasa Gateman aje masa jakarsa yafice, cike da farinciki, Mama tad'an bubbuga bayan Ya Nura, kafin tad'agoshi tana 'kare masa kallo, cike da farinciki ta furta "Alhamdulillah, Allah nagode maka daka nunamin wannan rana, ka dawomin da d'ana, ai daman Allah maji rokon bayinsane, addu'ar bawa bata ta'ba fad'i, zo zauna"
ta zauna bisa,kujera tasanya Ya Nura gefanta, Aunty tace "Nura da gaske kaid'inne kuwa?" Ya Nura yagyad'a kai cike da murmushi a fuskarsa, nan akahau gaisawa, Khaleel yadawo kusa dashi yazauna a'kasa suna hira,Hilal da Rahma ma zagayeshi sukayi suna kallonsa.
jin hayaniya yasanya Nana fitowa daga d'aki tana aikin karatun littafi, tafito hannunta ri'ke da Hameed dayazo hutu, da gudu ta'karaso tana d'ingisa 'kafarta, zuwa tayi tarungume Ya Nura cike da murna, Ya Nura yajanyeta ahankali ya dubi Mama da fad'in "yarannaki sungirma sunyi hankali" Mama tayi murmushi tace "ba doleba shekara uku zuwa hud'u" Hameed ne ya rungumeshi kamar yanda yaga Nana tayi masa, ya Nura yad'aukeshi yana murmushi, yace "wannanfa? nasan dai d'anane, sai dai bansan wanda yahaifaminba"
Ya Khaleel ysce "anbaka gari, kafad'a 'DAN WAYE?" ya Nura ya'kurawa yaron idanuwa kafin yace "kai boy ya sunanka?"
"Abdul-hameed, amma Hameed akecemin" ya Nura yayi murmushi ya dubi Khaleel yace
"nagane yanzu ai, d'angidan Hafsat ne, babban jika muka samu ashe da bana nan" aka sanya dariya Nana tace "bamu yardaba, dama kasan sunan da Aunty keson sanyawa yaronta shiyasa yana fad'a kagane" bai bata amsaba illa murmushi kawai da yayi, Mama sai bin d'annata take da kallo, tasan damacan ya Nura bamaison surutu da hayaniya bane, amma sai taga yanzuma yafi zama silent akan da.

Momy dake zaune cikin falonta ita da Kamal sukaji hayaniya tayi yawa a falon, suka fito dan ganin abinda yake faruwa, ganin Nura zaune cikin falon ya girgizasu Momy tace
"A'a Nura yau kaine a gidan?, ba'kin malesia, ina Haby take kuma?" ya dur'kusa yagaisheta kafin yace "ai ni kad'ai nazo, ita taje london ne" jin haka yasanya kowa sakar baki, tare da tambayar "london kuma?"
"ehh business take, zatazo nan da kwana biyu"
Momy tawashe baki tace "a'a ikon Allah kace Haby anzama hajiya"
Mama kuwa baki d'aya kanta yakulle, Aunty ce dai tayi murmushi kawai na takaici, cike da tausayawa Nura, domin tasan komai Aunty Hafsat ta sanarmata Mamace dai batasan dawar garinba.
Chapter 21 · 0% Book details