← Book details Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 23

Sashe 5

Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya Nura kuwa yana fita waya yabuga, mintuna kad'an sai ga mota nan d'auke da kaya cikin kwalaye, nan ya nuna musu inda zasu saka kayan yafice, da yake sauri yake yayi musu bayani idan sungama subawa mai gadi mukullum, ya fita yabarsu.

Nuratu ce tafe tana 'yan wa'ko'kinta zata shiga gidan kenan taga d'akin waje bud'e, cikin zumud'i ta nufi wajen dan ganin waye aciki kuma ya bud'e, domin tun taso warta d'akin rufe take ganinsa, da isarta le'kawa tayi taga anata bud'e furniture dariya tayi aranta tana fad'in “waye zaiyi aure kuma, ko dai Ya Nura ne?”cikin gidan ta nufa da gudunta batayi zatoba saiji tayi tayi karo da mutum, kafin tawaye da sanin wanda ta bangaza sai saukar mari taji, arazane Nuratu tad'ago taga ashe Haby ce, tsaki Nuratu taja gami da d'an guntun murmushi tayi tsalle tad'auke Haby da marin itama, tawuce ciki aguje ta nufi babban falo wajen Mama.

“lafiya Nuratu?”cewar Aunty kenan da taga Nuratu aguje tafad'a kan cinyar Mama, kafin tayi magana Haby tashigo, har kan cinyar Mama taje tajawo Nuratu, zata mareta Aunty tafizge Nuratu tana fad'in “lallai Habiba rashin kunyar taki takai, kizo har falonnan zaki daki Nuratu agabanmu kome tayi maki kifad'a mana mana, ko kuma kijira awaje kyayi mata rashin kunyar taki”wani mugun tsaki Haby taja kafin tace “sai dai inga wanda zai hanamin karya yarinyar nan wallahi akan namareta shine tasa hannu ta rama, ko ni sa'ar uwar tace?”
Aunty zatayi magana Mama ta tareta da fad'in “ki rabu da ita Auntyn Nura, kinsan dai ba sa'ar yinki bace, Nuratu kuma gatanan ki kasheta kinji 'karewar duka ko, sai insan kin isa rashin kunyar taki takai”Momyn Haby ce tashigo falon tana fad'an “mene haka Habiba, bana son wannan abin ai ba sa'an yinki bane, wuce muje”ta nunawa Haby hanyar waje, Haby tafice tana tura baki, Momy ta juyo tana fad'in “sai kuna ha'kuri kunsan halin yara sai ha'kuri”ta fad'a tana tura d'an kwali gaba, tafice itama tabarsu.
Aunty tazauna ta dafe kai, Mama ta dubi Nuratu kaman zatayi magana sai kuma tafasa, ganin hakan yasa Nuratu fad'in “Mama waye zaiyi aure kuma?”“mai kika gani?”cewar Mama, Nuratu tayi dariya da fad'in “naga d'akin waje ana saka furniture ne”“ohh yayanku ne zai koma nan d'akin, nan kuma Khaleel ne zai zauna”“laahh Mama yaushe Ya Khaleel zai dawo ne?”Nuratu tayi tambayar cikin zumud'i “nan da jibi yace, d'azu daya bugo waya” “wowww Mama, amma naji dad'i wallahi, mun huta da takuran Ya Nura”tafad'a tana fita daga falon aguje, Mama tayi murmushi tana girgiza kai, “Nuratu kenan Allah nuna mana randa zamuga nutsuwar Nuratu”“Amin aini wallahi wataran sai indinga tunanin anya Nuratu ita kad'aice kuwa ?”Aunty tafad'a, tana mai duban 'kofar da Nuratu tafita yanzu, Mama tayi dariya mai sauti “ita kad'aice kima daina wannan tunanin, kawai tsabar 'kiriniya ke cinta da rawar kai”“to Allah dai yakyauta yashirya mana ita”amin dai.

『』『』『』『』『』『』『』『』『』
zaune take falon Ammyn ta da littafi a hannunta tana karatu, domin daf suke da fara exam, sallama yayi fuskarsa d'auke da wannan shu'umin murmushin nasa mai tsada, Nuratu ko d'aga kai batayi ta dubeshi ba, sai ma kwanciya datayi tacigaba da karantunta, sai Ammy ce dake can cikin d'aki, tana shirya kayan gugarsu cikin wardrobe ta fito tana amsa sallamar.
“a'a Nura yau kaine kale'komu kuma? zauna mana katsaya kamar wani ba'ko”Ya Nura yayi murmushi yazauna kan d'aya daga cikin kujerun d'akin yana fad'in“wallahi kuwa Ammy yau ina free ne nace bari inzo mugaisa da Ammyn tawa”“ai kuwa ka kyauta wallahi ”Nuratu tayi tsaki jin yace Ammyn sa “iyayin banza”tafad'i aranta, Ammy ta dubeta tana zama “amma Nuratu baki da kirki, kina jin ana sallama baki amsaba, bare kuma gaisuwa”“to Ammy shinefa yayi sallamar ahankali, kuma ina karatu banjiba”Ammy takai mata duka“kinci gidan, ni da nake d'aki naji sallamar bare ke da kike falon tsabar iskanci”Ya Nura yayi murmushi yana fad'in “kirabu da ita Ammy babu komai”“haba wallahi ni iskancin yarinyar nan har yafara isata anya kuwa kanta 'kalau?”“ha'kuri zakiyi Ammy”cewar Ya Nura, Nuratu kuwa harararsa tayi tana tura baki gaba ta nufi d'aki, Ammy tabita da kallon takaici, shima bin nata yayi da kallo yanajin wani d'aci aransa, afili kuwa murmushi yayi kawai yana girgiza kai.
Ammy tadawo da kallonta kansa tace “kazo a dai-dai d'an gidana yanzun nan na kammala abincin da kake so bari inkawo maka”bata jira mai zaiceba tafice.
mintuna kad'an sai gata tadawo d'auke da flat arufe tami'ka masa takoma, Ya Nura yabud'e wani 'kamshi ya doki hancinsa tuwon shinkafane miyar agushi taji kifi sai tashin 'kamshi take, ya Nura yanason tuwo da miyar agushi sosai har dai girkin Ammy yakan jishi daban dana kowa.
Ammy tadawo d'auke da jug kunun gyad'ane aciki da yaji kwa-kwa da dabino, Ya Nura a'koshe yake, amma bai san sanda yatashi da tuwon da lemon ba, sukai ta dariya shida Ammy, Nuratu najinsu tacika tayi fam, dan ita arayuwa ta tsani ya Nura mugune take cewa.

BAYAN KWANA UKU
[23/11/2017, 21:56] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》🌈🌈🌈Book 1

MALLAKA......QURRATUL-AYN

08

(Godiya mai tarin yawa agareku 'YAN BIYU kyautar Allah HASSAN ATK TANKO & HUSSAINI ATK TANKO Allah yabar zumunci ngd sosai inayinku ko yaushe 😘👍🏻)

*** *** ***
BAYAN KWANA UKU
*** *** ***

“ke haby yakamata ki nutsu, duk wani rashin mutunci ki ajiye gefe wannan akwai lokacin yinsa, yanzu kissa da kisisina zaki d'auka, dole muyaudari mahaifiyar Nura domin musamu amincewarta, dan itama zata iya kawo mana sikas a shirinmu, duk da Alhaji ya amince nasan bazai canja maganaba amma dole kinemi soyayyar surukarki tahakanne zamu cimma gashi”Haby ta rumgume Momy cikin murna da farinciki, tana fad'in “kome kikace inyi Momy zanyi wallahi nidai burina in auri Ya Nura, ina son gayen wallahi yahad'u Momy”Momy tayi murmushi tad'an bugi Haby da fad'in “ko kunyata bakiji kike fad'in saurayinki yahad'u, to dai kada kizurfafa sonsa aranki kizo kina rusa mana plan d'inmu”“haba dai Momy, aini burina kawai in aureshi ko da adaran farko ya butu bazan damuba”suka sanya dariya baki d'aya, gami da tafawa.

Momy ce zaune falon Mama yayin da Haby ke zaune kusa da ita a'kasa, kanta na sunkuye Aunty da Mama suna zaune kan 2siter suna kallon Momy dake magana “Maman Nura munzone ban ha'kuri, ha'ki'ka nagane nayi babban kuskure arayuwa, dan haka naga yazama dole inzo mubaku ha'kuri munyi nadama sosai ni da yarana, nasan hakan kokad'an abinda muke maku babu kyau, kuma ba tarbiya bace, amma kuyi ha'kuri d'an Allah hakan bazata sake faruwaba zamuyi zama na amana da mutunci insha Allahu”.
Mama tayi murmushi tana fad'in “amma gaskiya naji,dad'i sosai da kuka fahimci gaskiya, ai zaman,mutunci da kwanciyar hankali yafi komai, wallahi komai yawuce araina daman banri'ke kuba Allah bamu ikon kyauta tawa juna da ha 'kuri”“amin”suka furta atare, Aunty tace “komai yawuce ai, sai akiyaye gaba”Haby ma dur'kusawa tayi tanemi gafara duk sukace komai yawuce, nan sukaita hira kai kace babu abinda yahad'asu arayuwa nan kuwa ta ciki na ciki Momy da d'iyarta Haby.

yau take ranar dawowar Khaleel daga malesia inda yaje yakaranci Doctor, gida ya cika da hayaniya sai 'kamshi ke tashi kala-kala, asauke a d'ora aikin kenan tun safe, babu wanda yazauna cikinsu Mama ko wanne da aikin da yake Haby ma ba'abarta abayaba har da ita a kitchen d'in, su Nuratu ne dai su a fannin fitina da ci aka barsu, komai aka sauke sai sunci Mama bata hanasu, idan ma za'a hanasu cewa takeyi kada atakurawa 'yan iyalanta abarsu suci, hakan ne yabawa su Nuratu damar yin tsiya kala-kala a kitchen d'in wani abun ma da tsoka sukeyi dan Haby tasa baki, amma ta danne domin hud'ubar Momynta na nan akunnanta.

'karfe sha biyu komai ya kammala, nan aka shirya komai aka gyara ko ina, sannan kowa ya nufi part nasa domin shiryawa, sabida 'karfe d'aya jirgin nasu zai sauka afilin jirgin malam aminu kano.

“idan kunshirya Mama kufito mu tafi, Abba na mota da Momy yana jiranku”cewar Ya Nura kenan, yana mai fita daga falon, Mama tafito cikin wani rantsats-tsan leshinta ba'ki mai rashin ash-silba, ba'karamin kyau tayiba kasancewar Mama farar fata ga kyau ga son gayu, bazaka ta'ba ganewa ita tahaifi Ya Nura ba, sai idan ansanar maka, itama Aunty irin shigar Momy tayi kasancewar dama sun saba duk inda zasuje anko suke shima Abba hakan nayi masa dad'i shiyasa duk d'inki anko yake yimasu.
Abba da Ya Nura ne agaba, sannan Mama da Aunty sai Momy duk abaya suke, Ya Nura ne keyin dreving, su Mama na baya suna hira tsakaninsu abin dai abin ban sha'awa, hakan ba 'karamin yiwa Abba da Ya Nura dad'i yayiba.

Dai-dai sanda jirgin ke sauka, su kuma suna isa filin jirgin, fasinjojin, suka kama layin saukowa, cikinsu har da Khaleel dake sanye cikin ba'kin jeans da farar t.shart sai farin glass d'in dake manne a fuskarsa wanda ya'kara masa kyau ainun, ga kwantaccen gashinsa ba'ki wuluk dayasha kud'i, gaskiya shima Khaleel ba bayaba wajen,kyau sai dai muce masha Allah.

Da murmushinsa ya'karaso waajensu, ya gaida Abba dasu Mama cikin farinciki suka amsa, sannan ya rungume Ya Nura kowa ya cika da farin cikin,yanda suka ganshi yayi kyau abinsa, sannan ya kammala,karatunsa lafiya tare da tarin albarka.
a mota,babu wanda ya fara tambaya,illa Nuratu, Aunty tayi dariya tana fad'in “ai Nuratu tana nan inda kabarta,illa ma abinda ya'karu”Khaleel yayi dariya,“kuce haryanzu kuna nan kuna fama?”“wallahi kuwa sai fatan shiriya,kawak”cewar Mama kenan, Momy kuwa,haushi ya cikata, yarasa wadda zai tambaya sai wata can, bayan ga 'yan'uwansa nan najini, a fili kuwa murmushi kawai take kamar babu komai aranta.
Chapter 5 · 0% Book details