← Book details Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 23

Sashe 8

Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

lokacin Abba yataso da batun 'karin aure, dake Mama macace ta gari mai kawaici da sanin ciwon kai, ko kad'an bata damuba saima fatan alkhairi da tayi, domin tasan namiji ma aurin mata hud'une ba biyuba, Inna cema taso tabashi matsala, acewarta dukansu mata d'aya ta ishesu, kaman yanda tazauna ita kad'ai batason tara mata agida, taron rigima, ankai ruwa rana kafin ta amince da auren, domin sai da Yayanta yashigo maganar, sannan ta amince (Innar rigima kenan).
kuma dayake Abba namijine domin baya mantawa da dukkan ha'k'kin dayasan ya rataya akansa, aurensa bai sanya ya sauyawa Mama ba ko kad'an.
Dayake abune namasu hali, ba'awani ja lokaciba akayi bikin domin wata bazawara ce mai suna Habiba ya aura, Mama tacewa su Nura sudinga kiranta Aunty, yaran kuwa na bata girma sosai, kaman yanda take girmama mahaifiyarsu Mama.
suna zamansu lafiya, cikin girmama juna Abba kansa najin dad'in hakan sosai.
[29/11/2017, 03:04] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈QIYAYYA SA GANIN LAIFI🌈🌈🌈Book 1

MALLAKA......QURRATUL-AYN

11

【NURATU nami'ko gaisuwa agareku masoyanta tanayi muku fatan alkhairi, QURRATUL-AYN tana godiya sosai da addu'arku agareta😘】

BAYAN SHEKARU GOMA SHA BIYAR

Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da auren Hafsat da akai tare da wani doctor mai suna Hamza, tunda Hafsat ta kammala scondry school Inna ta matsa akan dole ta fidda miji ayi mata aure, domin ita macace bata son wani zurfin boko akan mace gwanda namijin, cikin ikon Allah kuwa doctor Hamza ya fito da gaske, Abba baiyi 'kasa a gwiwaba wajen bincikar asalibsa ba, bayan gamsuwa dashi da Abba yayi yaga yafito daga gidan tarbiyarne, nan da nan aka sanya rana akasha biki.
har wannan lokaci gidan Abba ko 'batan wata ba'asakeyiba, babu kuma wanda yadamu da hakan, domin sunsan samu da rashi duk na Allah ne.

Ammy ce zaune cikin falonta kankujera mai cin mutum biyu, yayin da wata mace ke zaune kan kujera mai cin mutum d'aya, da dukkan alamu tattaunawa suke akan matsalolinsu, Ammy tad'anyi murmushi tana fad'in “ni kuwa Momyn Haby kina bani mamaki, menene acikin haihuwa kuma, ni da nake nema nizan damu, amma nima nabarwa Allah dukkan lamurana, amma ace ke dakika samu kike wannan maganar”matar da aka kira da Momyn Haby tayi wani murmushi,mai kama da takaici, ta dubi Ammy tana fad'in “ke kike ganin hakan, amma ni nasan wuyar danake sha ahalin yanzu, domin wani lokacin abincin da zamuci ga gararmu yake, banda Allah yahad'amu daku da bansan yanda zanyiba arayuwa”“uhmmm ke kike tunanin hakan, amma Allahn daya baka 'ya'yan shiyasan yanda zai tafi da rayuwarsu, mu namu kawai rainone da tarbiya”Ammy tafad'a cike da murmushi akan fuskarta, Momyn Haby takau da zancen tana fad'in “ni kuwa Abban su Nura nanan, inason yi masa godiya ne, abisa hidimar dayake agaremu”“yana nan, jiyama yadawo daga dubai”Ammy tabata amsa, ta d'an ta'be baki, kafin tace “to ni zanwuce gida, idan munhad'u nayi masa godiyar”Ammy tayi mata rakiya har soro, sukai sallama ta tafi.

Asalin Momyn Haby 'yar barnoce sunanta Rabi'atu, aure ne yakawota garin kano, ita da mijinta ma aikancin gwamnatine,sunansa Safiyanu, yaransu uku, khaleel shine,babba sai Habiba sai Kamal, Khaleel kusan sa'an Nurane, amma nuran ya girmashi da shekaru biyu, sai Habiba da tsiransu da kamal shekara biyar, sannan Kamal tsiransu da Habiba shekaru uku.
Gidansu nanan 'kasan layinsu Ammy, mutuwar mijinta shine asalin had'uwarsu da Ammy, da take bala'in tausayawa rayuwar yaran da ita kanta u
wartasu, kasancewa mijin nata yarasu bai barmusu komaiba arayuwa, hakan yasa Ammy take d'an taimaka musu, tare da Mama, Mamace ma tasanarwa Abba akan ad'inga taimaka musu kamar yanda Ammy takawo kukan hakan.
Ammy ta aminta da Momyn Haby sosai, hakanne yasaka babu wani sirri nata da bata saniba, komai za'ayi a gidan suna tare, sabida amintarsu.
Nura kuwa yadage akan cewa shifa soja yake son tafiya 'kasar malesia, kasancewar ya kammala karatunsa na scondry, Abba da farko 'kin amincewa da hakan yayi, sai da Abba 'karami yasanya baki sannan Abba ya amince aka tura Nura malesia.

Tafiyar Nura malesia da shekara uku, ciki ya baiyana atare da Ammy karkuso kuga murna cikin gidaje guda biyunnan, har dai 'bangaran Mama tafi kowa murna da samuwar cikin, Ammy taga gata domin aikin komai hanata yisu Mama sukai, suke yi mata komai, Abba 'karami kuwa har 'yan aiki yace zai kawo, Ammy ta'ki amincewa da hakan.
Ammy na mamakin Abba ayanzu, shida da baya nuna wata damuwa,akan rashin haihuwarta, amma yanzu yafi kowa damuwa akan cikin nata, idan tatuna hakan sai dai tayi dariya kawai, tasan halin Abba wajen kawaici da zurfin ciki, amma baya nunawa akan cikin nan.

ana cikin hakan kuma Abba ya 'bullo da wani al'amari daya girgiza kowa, ba komai bane illa cewa da yayi zai auri Momyn Haby, al'amarin ya girgiza Ammy da Mama, musamman Ammy har taso sanya abin aranta, yana bara zanar ficewar cikinta, sai da Abba 'karami yanuna jan ido akan hakan sannan tad'an rage damuwa, amma kullum suka zauna ita da Mama zancensu baya wuce batun cin amanar da Momyn haby tayi musu, Aunty cema bata fiye nuna damuwarta akan hakan ba.

Momyn haby tad'auke 'kafa 'bat, daga zuwa gidan, hakan ya'kara tabbatar musu da batun auren da gaske ne.
wata mata dake makwabtaka da Momyn haby ita taje wajen Mama tana sanarmata cewar su tashi tsaye da addu'a domin Momyn haby ba haka tabar Abba ba, har alwashi tayi indai tashiga gidan to babu su ba farinciki, kuma sai daula da mulki sunkoma hannunta sai Abba yadaina ganin kowa sai ita, daman kawai lumbu-lumbu tayi musu.
Mama bata d'au maganar da muhimmanciba, ganinta gulmace kawai ta mata da ba 'arabasu da ita.

*** *** ***

“Ni kuwa Maman Nura mai kike gani akan batun auren nan na Alhaji?”cewar Aunty dake gyaran alaiyahu, a kitchen yayin da Mama tamai da hankali kan tu'kin tuwanta, Mama tad'an dubeta kafin tace “mai kuwa zanyi ayanzu banda abin da yawuce addu'a da fatan alkhairi”Aunty tad'an ta'be baki “nikam abin nabani mamaaki wallahi, yanzu Alhaji baki d'aya hankalinsa yakarkata kan aurennan da zaiyi, bama yabi takanmu”“kidaina sanya damuwar wannan abin aranki, ki dinga addu'a kawai, amma sanya damuwa bashine zai saka yafasaba, saima sanyashi yayi auren da damuwar taki zatayi, amma idan kika watsar da lamarin kika fuskanci abinda yake gabanki hakan zai saka yaji shakkar wani abun, ko kinajin damuwa aranki dannewa zaki dingayi, nasan ai kishi dole ne, domin halittar muce tazo da hakan, amma dai kidinga ha'kuri”Aunty tad'anyi murmushi tace “kai amma nagode sosai Maman Nura, shiyasa nake son zama dake, inajin dadin shawaranki agareni nagode sosai”“karki damu ai anzama d'aya”nan suka cigaba da aikinsu,kamar babu wata damuwa arabsu, domin dama sunsaba,idan kaje gidan bazaka gane wacece da girkiba, komai tare sukeyi.

Abba 'karamine zaune falo, da kwanukan abinci,gabansa yayinda Ammy,kezaune gefansa, da cikinta wanda yafito sosai yana wata na shidda kenan, Ammy tad'anyi gyaran murya tana fad'in “yanzu dan Allah babu wanda zai iya hana Abba wannan auren?”yad'an dubeta yana mai ajiye cokalin hannunsa tare da fad'in “babu mai hana wannan auren ayanzu, d'aurin aure yarage sati guda, Inna ce kawai kuma itama ta amince da auren, to waima menene abin damuwa da hakan?, shi namiiji ai ma'aurin mata hud'une, kuma yana da yanda zaiyine shiyasa zai aureta”“bazaka gane abinda yasaba”Abba 'karami yayi dariya yana fad'in “yaushe kuwa zangane tunda kina taya 'yar uwarki kishine, kika sanima ko nima tare za'a d'aura da,nawa”Ammy wata harara ta watsa masa, wadda batasan tayi taba, Abba yasa dariya yana mai jawota jikinsa tare da fad'in “ke kad'ai kin ishe ni rayuwa”Ammy tayi murmushi kawai.

Cikin satin da Abba zai 'kara auren, yasake gyara gidansa sosai, ya fitar da inda Amaryarsa zata zauna, akai fenti da komai, sannan ya canjawa ko wacce kayan d'aki, kamar yanda yayiwa amaryar tasa komai, sai wani rawar 'kafa yake kai kace yanzune zaiyi auren fari.

Aunty Hafsat dataji wadda mahaifinsu zai aura, taji haushi sosai, har tad'au alwashin ba ita ba zuwa gidan ranar bikin bare tayi kallon kayan takaici.
Nura kuwa nacan malesia asalima baisan wainar da ake toyawaba anan gida nigeria.

Sati na zuwa aka d'aura aure, da 'ker kwarya kwaryan walima, a daran amarya tatare, randa aka kawota su Mama sung
a bariki, ganin idansu, tun daga kan masu kawota har zuwa ita kanta amaryar, tare da yaranta ta tare baki d'aya.
ashema Abba ya mai dasu school baki d'ayansu, dayake da duk ankoresu sabida rashin biyan school fees.

Tun da Momyn Haby tazo gidan abubuwa da dama yacanja, basa rigima amma dai yawanci sai abinda tace za'ayi agidan, ga yaranta basu da kunya ko kad'an, har dai Habiba tun suna yara kenan Khaleel ne shi babu ruwansa, asalima yafi zama d'akin Mama akan d'akinsu, domin shi Allah yayishi da ha'kuri da rashin son fitina
tun zuwan Momyn Haby ta tare d'akin Aunty bini bini suna d'akin ita da yaranta, cikin wata guda Aunty tad'aurewa Mama fuska yaza mana babu shiri tsakaninsu, wata rana ranar girkin Aunty da dare, Abba na kwance yace Aunty tami'ko masa wata jaka tasa, dayazo da ita da safe ya ajiye kud'ine cike aciki na 'yan kasuwarsu abokansa suka bashi ajiya za'aiko masu wasu kaya, ita Aunty batama san da jakarba Abba na bud'ewa yaga kud'in babu bandir uku, Abba ya mi'ke da sauri yana duban Aunty tare da fad'in “kin ta'ba jakarnan ko?”“a'a mai kagani Alhaji ni da kosanin kazo da itama banyiba”Abba ransa ya'baci “kinga banson wasa, kud'ine na ajiya nazo dasu, yanzu na duba babu babdir uku”“wallahi ban d'aukaba Alhaji domin bansan kazo da kud'in bama”“to waye yashigo d'akinan?” “babu kowa dan gaskiya banga wanda yashigoba”.
Chapter 8 · 0% Book details