← Book details Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 23

Sashe 10

Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Garararrrffff aka turo gate aguje tashi go, yayin da wasu garada su biyu suka biyo bayansu, Gateman ne yayi saurin ri'kota, sukuma garadan suka ja birki suka tsaya, ganin hakan yasanya Ya Nura mi'kewa da sauri ya nufi bakin gate d'in, Nuratu sai wani fiffi'kewa takeyi zata gudu, mutum d'aya daga cikin mutanan yana fad'in “kaga Baba kabarmu mu fyed'eta kawai, harmu zatayiwa rashin kunya”cikin maye yake fad'in hakan ga kuma wu'ka a hannunsa, Ya Nura nazuwa ko kallon inda Nuratu take baiyiba, yahau tambayar samarin mai yafaru d'aya daga cikinsu yace “muna cikin tafiyane yalla'bai,kawai sai ga wannan sikar tazo, shine tahaucewa 'yan maye masu warin kashi, 'yan maye basa wanka, 'yan maye masu kwanan bola, aka cemata mu sa'annintane eyee, kawai Baba kabamu ita muje mufyed'e muyi kilishinta kawai 'yar banza, yalla'bai kada kace komai”“wallahi 'karya yake, 'karya sukemin Allah ya Nura”cikin d'aga murya Nuratu take fad'in haka.
Abba ne ya'karaso da sauri shi da su Mama da Khaleel suna tambayar “lafiya Nura nakejin haya niya?”Samarin suka sake mai-maita abinda Nuratu tayi musu, Aunty da Mama ri'ke baki kawai sukayi, Abbane yatsaya basu ha'kuri suna rashin mutumci, hakan yasanya ya Nura fito da I.D card nasa, sai gasu sunzube bisa gwiyoyinsu, suna bashi ha'kuri, Nuratu kuwa sai dariya take ri'kewa tanayi musu gwalo, Ya Nura yace sutashi sutafi, amma kada su sake yawo da makami suna fad'in zasu kashe mutum, tuni suka cika wandonsu da iska sukayi waje.

Abba yakama hannun Nuratu sukayi cikin gida, Ya Nura ma baikoma wajen Haby ba, dake can zaune tana kallonsu ta cika tayi fam, aganinta Ya Nura ya wula'kantata, akanme zai tafi wajen Nuratu yabarta, aganinta yabarta kawai su nakasata.
Abba falonsa yawuce da ita, baki d'ayansu suka bishi, illa Khaleel daya nufi d'akinsa, domin yana da aikin yi, Abba ya zauna kan kujera Nuratu nakusa da 'kafarsa, Mama da Aunty ma kan kujera suka zauna, ya Nura shima 'kasa yazauna, domin girmama mahaifansa.
Abba yace “Nuratu tawa, Nuratun Ammy”Nuratu tayi dariya tana fad'in “na'am Abba”Abba ya cigaba da fad'in “mai yasa kuka barta tafita adarannan?”Mama tace “nifa cewa tayi dani wajen Ammyn ta zataje, yau acan zata kwana”“to kuma sai kibarta tafita, kuma ita kad'aima awannan daren, yanzu da wani abu yafaru da itafa?”cewar Abba cikin fad'a, Mama tad'anyi murmushi “Allah dai yakiyaye Alhaji, amma kai kanka kasan halin Nuratu, idan taso abu kamar d'a yaso fitowa daga cikin mahaifiyarsa, to yakake so nayi da ita?”“babu yanda zakiyi da ita, amma dai kada kimance Nuratu marainiyace, kada ganin mahaifiyarta da kuke yasanya kumanta, kusan ri'kon maraya sai da ha'kuri, kuma gata yarinya 'karama, ni kuma dubata ko sunyi mata wani abu, domin hankalina bai kwantaba”“Nuratu ta, ko sunyi maki wani abune?”ya tambayi Nuratu, Nuratu tad'an tura baki cikin shagwa'ba “A'a Abba basuyimin komai ba, ai gudowa nayi kasan na iya gudu, kawai dai nad'an buge a'kafane kuma ya Nurane yabugamin takalminsa”tafad'a tana kallon Ya Nura da shima ita d'in yake kallo cike da mamaki da takaici, ya kuwa watsa mata harara mai d'auke da inkiyar zaki gane kurenka “to shikenan rabu dashi 'yar gidan Ammy, amma kidaina fita da dare, kuma kirage tsokana”“to Abba”tafad'a fuskarta d'auke da murmushi, “Abba kagafa hararata yake, dukana zaiyi Allah idan baka nan”ta sake fad'i, Abba yace “a'a kar naji kar nagani, laifin me tayi na duka, bafa nason doke dokennan, kaji ko?”“to Abba”ya Nura yafad'a kansa a'kasa.

Nan kuma suka shiga wata hiran, har Nuratu tayi barci kanta nakan cinyar Abba, sai da kowa yatashi zai nufi d'akinsa, Abba yace ya Nura yad'au Nuratu yakaita d'akinsu, babu yanda ya iya akan dole ya d'auketa, akad'arsa yad'orata, ya nufi d'akinsu da ita, suna shiga d'akin nasu, ta sakar masa wata uwar tusa mai shegen wari dai-dai salansar hancinsa, ai kuwa ya Nura bai san sanda yasake taba, Allah yasa yaje dai-dai kangadon tafad'a kan gadon ruf da ciki, ya Nura yayi tsaki yafice da sauri, Nuratu tami'ke zaune tana dariya har da ri'ke ciki.
ashe tun sanda yad'auketa tafarka amma tayi masa likimo.🤣😘❤
[01/12/2017, 15:16] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈QIYAYYA SA GANIN LAIFI🌈🌈🌈Book 1

mallaka.....QURRATUL-AYN

13

Tafiya yake cikin motarsa, yana tu'ki cikin kwarewa irin tasa, fuskarsa d'auke da murmushi, wanda da dukkan alamu na farin ciki ne, gefe guda kuma abokinsa Khamis ne yana ta danne-danne awayarsa can yad'ago yana duban Ya Nura “kai amma gaskiya Master natayaka murna wallahi, yanzu malesia ce kenemanka domin yi masu aiki tsawon shekaru bakwai?”“yes...nan da wata uku sukeson najema, domin da wata guda sukace, ni na nace akan subani wata uku”“to mudai fatan Alkhairi Allah yataimaka yasa aje lafiya adawo lafiya”“amin...”wayarsa dake hannun Khamis itace tayi 'kara, alamun tana neman agajin gaggawa, Ya Nura yace “d'aga mana” “a'a kadai d'aga master Abba ne”“ok”yafad'a yana kar'ban wayar, yakarata akunnansa, Abba ke fad'in “kana jina Nura?, kaje makarantar su Nuratu, uncle d'insu yakirani yana nemana, to nariga nashiga meeting ne yanzu, kaje kaji lafiya?”“to Abba babu damuwa, kahuta lafiya”Abba yakashe wayar, Ya Nura ya ajiye wayar, yana mai jan wani uban tsaki, Khamis yace “lafiya dai master?”“inafa lafiya?, yanzu haka waccan mai ba'kin kunnance tayi wani abu a school nasu,Abba yace inje inji komenene”“to maza mujuya ko? Allah yasa dai lafiya?”cewar Khamis, Ya Nura yayi guntun tsaki, yana dukaan sityarin motar, yajuya suka koma, domin da suna hanyar zuwa (gadon gaya ne, school d'in kuma kuntau take).

zaune suke kan kujeru cikin office d'in principal a school d'in gefe guda kuma Nuratuce zaune, tare da wata yarinya kusan sa'ar Nuratun goshinta afashe and'aure da d'ankwalli sai jini duk yaji'ke d'an kwalin, sai kuma Uncle d'insu dake tsaye gefe guda, principal yaace yarinyar ta mai-maita abinda yahad'asu da Nuratu, cikin kuka tahau fad'in “wai akan jiya batayi note ba, to ni nayi shine tace in ara mata book d'ina, na aramata tayi shine naga ta yagamin, kuma ba'ayage nabataba, dan nace mai yasa ta yagamin shine tahauni da kokawa ta bugamin goshi abango, wai mai yasa zance ita tayagamin, tayaga inyi abinda zanyi”principal yace “to kaji dai, Nuratu bataji wallahi fitinarta tayi yawa, kusan kullum saimun kashe case nata, abunne yake yawa yasaka bama sanarwa mahaifinta, domin shi babban mutum ne kuma yana da daraja awajenmu”Ya Nura dai kasa cewa komai yayi sai Khamis ne ya ari bakinsa da fad'in “ayi dai ha'kuri yalla'bai, kunsan sha'anin yaro sai da ha'kuri, a gidama haka muke fama da ita, idan dukanne sai dai mugaji amma bata daina abinda tasaba, yanzu dai ga wannan awanke ciwon”Khamis ya d'auko wallet d'insa yazaro 5k (dubu biyar) yami'kawa principal, suka bawa yarinyarr ha'kuri tare da sallama suka fito, sai sannan Ya Nura ya dubi Nuratu yana fad'in, “zakizo kisame ni agida yarinya”suka fice.

Kafin su'karasa inda sukai parking motarsu, Khamis ya dubi Ya Nura “wai ya dai naga kakasa cewa komaine?”“to mai zance Khamis, kasan idan dukan yarinyar nan zanyi, Allah sai inkasheta abaanza, inda zuciya takawomin wuya shiiyasa nayi shiru kawai, domin shirun shiyafi alkhairi”“to da babu ni kuma fa?”Ya Nura jin tambayar da Khamis yayi masa yasashi murmushi wanda iyakacinsa le'bansa, kafin yabashi amsa, sai ji yayi anrungumeshi ta bayansa, ya juyo dan ganin waye, Nuratu tayi maza ta zube 'kasa tari'ko hannunsa gam, tana fad'in “kayi ha'kurri ya Nura, nadaina bazan kuma ba, kada kadokeni dan Allah....”ri'kon da tayiwa hannunsa, da abinda yakeji na daban akanta, wanda ko Haby ce tari'ke bayajin hankan,yasanyashi janye hannunsa ahankali, jikinsa yaji ya mutu, amma mai makon yaji tausayinta saima tsanarta daya sake ji, wani mugun kallo ya watsa mata kafin yace “tashi kibani waje, kuma da kin dawo gida kije d'akina kisame ni, zaki gane kuranki yau” Nuratu tami'ke da sauri, ta murgud'a masa baki kafin ta juya tana 'ku'kuni.

Ya Nura yabita da kallo kawai, yana tunanin abinda zaiyi mata, wanda zai saka ta nutsu, yarasama irin horon dazaiyiwa Nuratu, Khamis kuwa dariya yasa, har da ri'ke ciki, hakan yasanya ya Nura 'kara 'kulewa, ya wuce abinsa yashige mota, ganin da Khamis yayi ya Nura nashirin tafiya yabarshi, yasanyashi 'karasawa da sauri yashige motar, har lokacin bai daina dariyarba, sai da yayi mai isarsa, kafin yace “kayi ha'kurifa master Allah abubuwan yarinyar nan yana bani dariya da mamaki, har dai idan kuna wata dramar sai inji kamar inyi maku video”ya Nura yayi tsaki yana fad'in “da yake film muke ko? kaga bana son rashin mutumci wallahi”Khamis yasake dariya “dad'ina da kai d'aukan zafi, ko dayake aikai sojane, soja kuwa sai aslow, amma kana ganin yarinyar nan anya bata da aljannu?”ya Nura yayi tsaki, ganin da yayi Khamis nata 'kara masa 'bacin raine, yasa yayi shuru, bai sake tanka masaba, Khamis keta zubarsa shi kad'ai, domin mutum neshi mai surutu, har suka isa inda suka nufa, ya Nura bai cemasa komaiba shi adole yaji haushi.

WEEKEND
8:00Am

kwance yake kan doguwar kujera, da dukkan alamuma barci yakeyi, sanye yake da farar best da gajeran wanda wanda iya kacinsa gwiwarsa shima farine, dake shi dogone amma ba canba 'kafafuwansa, har sund'an haura kujerar, kansa kuma nakan hannun kujerar yasanya pillow, fuskarsa watsai, ma'abocin kyawun fuskane doguwa tana tafene da tsayin jikinsa, ba siriribane amma bazaka kirashi mai 'kiba ba, ga wani saje dayayi 'kawanya afuskarsa ba'ki wuluk, sai siririn hancinsa dake 'karawa fuskarsa kyau, bashi da manyan idanuwa amma kuma ba 'kananu bane gasu farare tas, ba'kin ciki kuwa har yafi sumarsa ba'ki, kannan nasa masha Allah gashin kan akwance luf, kai kace yana shampoo ne, sai zara zaran gashin gira dana idanu dake 'kara fito da tsan-tsan kyawunsa, gashin giransa harya kusa had'ewama, sannan ma'abocin dogwayen yatsune fes dasu abin sha'awa, ma'abocin faffad'an 'kirjine da gashi yakwanta luff ba'ki dashi.
A gaskiya dai duk inda namiji kyakykyawa mai jini ajika yakai to ya Nura yakai, domin irin mazan nanne da kowacce mace zataso ace yazama maallakinta, kuma tayi tin'kaho da nunashi aduniya matsayin mijinta.
Chapter 10 · 0% Book details