Sashe 6
Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
suna isa gidan kai tsaye babban falo suka nufa da gudu Nuratu ta she'ko tarungume Khaleel tana “oyoyo yayanmu”Hilal da Rahma ma suka rungumeshi, Nana tataso da 'kyar tana dogara sandarta zuwa wajensa, Khaleel yajanye su Nuratu ya'karasa gareta da sauri yana fad'in “mai yasameki haka kuma Nana?”“ciwo naji”tafad'a tana 'karasawa,gareshi, Mama tace “ai yanzu,jiki alhmdlh taji sau'ki sai 'karashe kuma”duk sai yaji babu dad'i a ransa afili kuwa fad'i yayi“Allah 'kara lafiya”sukace “amin dai”.
Haby ma zuwa tayi ta rungume d'an uwan nata tana murna, shi kunya ma sai takamashi, duk da 'yar uwace ta jini, amma yasan hakan da kunya domin ai tawuce yin hakan a addinance, ita kuwa ko ajikinta, awajenta waye wace da cinyewa hakan, Khaleel yajanyeta yana mai amsa sannu da zuwan Kamal dayake yi masa, kafin kuma ad'unguma zuwa daining table baki d'aya, sannan Kamal yakai masa kayansa d'akinsa, shima yadawo yazauna dan bawa ciki ha'k'kinsa.
Dawowarsa kenan ya shiga cikin gidan domin kaiwa Aunty aikenta, “Mama daman ashe Ya Nura d'an iskane...?”Mama ta dubeta “mai kike cewa?”Nuratu tafito da wasu,fefan cd guda biyu tana nunawa Mama, yayin da Rahma da Hilal suka hau fad'in “a cikin d'akinsa muka gani wallahi Mama, duba ki gani”dai-dai sanda suke nunawa, sannan Ya Nura yakawo kai zai wuce, Mama duba d'aya tayiwa caset d'in tad'auke kai, “innalillahi wa'inna ilaihi razee'un”Ya Nura yafad'a yana mai fizge caset d'in yad'auke Nuratu da mari da sai da tayi,kaman zata fad'i, Mama ta tarota kallon datayiwa Ya Nura ne yasanyashi sunkuyar da kai 'kasa yana fad'in “kiyi ha'kuri Mama, Amma wallahi wannan ba nawa bane, a d'akin Kamal nad'aukeshi randa Abba yace inkirashi nataddashi yana kallo shima sai da na zaneshi, shine nad'auke nakai d'akina da zummar zan 'kona kuma namance”Mama tayi shiru kafin tace “kaji jeka yawuce”Ya Nura baiji dad'in yanda Mama tayi masaba, koba komai tafi kowa sanin wayeshi, tafi kowa sanin halinsa, har Aunty yasama yasanar mata akan tabaiwa Mama ha'kuri, Mama kuwa sai ta d'aurewa ya Nura fuska kullum yazo gaisheta sai yayi aikin bawa Mama ha'kuri, duk sai yake yaji gidan babu dad'i, hakan yasa tsanar Nuratu ta'kara yawa aransa, gashi Mama tahanashi ya hukuntata koya huce.
『』 『』 『』『』 『』 『』
BAYAN KWANA BIYU
Zaune suke baki d'ayansu a babban falo, Abba zaune kan kujera yayin da Mama,Momy,Aunty,Ammy kowan nensu nakan kujera, sai Ya Nura da Khaleel,sai Kamal da Haby zaune duk suke 'kasa kan kafet, Aunty Hafsa ma tazo, da dukkan alamu maganace mai mahimmanci tahad'an family guda waje d'aya, yara ne kawai,babu su, asalima suna gidan Ammy suna wasansu basu san wainar da ake toyawaba.
Abba yabud'e taro da addu'a,kafin yafara magana “nasan duk zakuyi mamakin tarakun da nayi ayau duk da dai ba abin mamaki bane”Abba yad'anyi shiru yana binsu da kallo kafin yad'ora yana murmushi,“taron yau ba akan komai bane illa kai Nura”Abba yafad'a yana mai nuna Ya Nura, kowa yasha jinin jikinsa,yad'auka wani laifi Ya Nura ya aikata Abba yacigaba da fad'in “Nura kwanaki nasha yimaka batun aure amma sai dai bana samun gamshash-shiyar amsa naga kuma kai kamar auren baya gabanka ayanzu,dan haka nayi shawara na kuma yanke hukuncin had'a aurenka da Habiba”dammmmm gaban ya Nura yafad'i, yad'ago kai ya dubi Mama, yaga ko kallon inda yake batayiba, tunaninsa yatsaya akan ko abinda yafaru kwanakine yasanya Mama sanarwa Abba yayanke wannan hukunci, daman yasan tunda Mama tayi fushi dashi haka yana iya fuskantar ko wanne irin hukunci jiran tsammani yake dama.
tunaninsa yadawo adai-dai sanda yaji Abba nafad'in “mai kayanke akan hakan Nura, dan bazan takura makaba”ya Nura yahad'iye wani yawu mai d'aci abakinsa,kafin yace “duk abinda kuka yanke akaina dai-daine Abba, ni mai biyayyane agareku”“to alhamdulillahi, ke kumafa Habiba? ina sonjin ta bakinki”cewar Abba “nima dai babu komai awajena zanyi biyayya insha Allah”Haby tafad'a kanta a'kasa, Abba yace su Mama ko suna da abin fad'i kowacce tace babu,sai fatan alkhairi, Abba ya rufe taro da addu'a kowa ya watse .
“wai kai da gaske kake fad'a master za'a had'a aurenka da Haby ta gidanku?”Ya Nura yayi tsaki yana mai kur'ban lemon dayake sha cikin kofin glass, ya ajiye yana fad'in “na ta'ba yimaka 'karyane Khamis? wallahi nima zancen kawai naji daga sama kuma wannan aljanar yarinyar itace tajamin komai na tsani Nuratu Khamis na tsaneta”Khamis yayi dariya “kaga Master zancen tsana bai tasoba, ni banga laifin Nuratu ba anan, tunda ba ita ketsara maka dukkan rayuwar kaba, kad'au wannan matsayin 'kaddara,kuma haka Allah yatsara maka, amma ni abinda yake bani mamaki daman wai Haby ba'kanwarka bace?”Ya Nura ya furzar da wata iska daga bakinsa mai zafi yana fad'in “ba 'kanwa bace”“to idan ba 'kanwarka bace ya kuke da ita?”.
ya Nura ya'kurawa Khamis ido jin tambayar daya watso masa, kafin yakwantar da kansa saman kujerar dayake zaune 'kasanta yarufe idanunsa kamar mai bacci
SHEKARUN BAYA CAN DA SUKA WUCE
ASALIN LABARI KENAN
[25/11/2017, 01:05] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》🌈🌈🌈Book 1
MALLAKA.....QURRATUL-AYN
09
【【SHEKARUN BAYA DA SUKA WUCE】】
(Farkon labari kenan)
*** *** ***
Malam Salisu Ibrahim haifaffan jahar jigawa ne cikin garin ringim, bafulatani ne tsan-tsa, kuma babban malami da malanta takawoshi garin kano, ya tare a unguwar rijiyar zaki d'orawar 'yan kifi trasformer ta......( bari dai indakata anan kada inbada full address 'yan tsurku suje sa eyes 😜musamman MISS XOXO da HAFCY RANO,😏)shine mahaifi ga Abba, su uku ne kawai ya haifa a duniya tare da matarsa mai suna Aisha da suke kiranta INNA, Aminu shine babba wato (Abba) sai mai bi masa Auwal (mahaifin Nuratu kenan) sai kuma 'kanwarsu wato auta mai suna Suwaiba, su kad'ai Allah yabasu sun tsaya tsayin daka wajen tarbiyar yaransu, malam Salisu baiyi 'kasa a gwiwaba wajen sanya yaransa karatun boko, sai da Aminu yakai matakin digree sannan yakama harkar kasuwanci dayake fannin business yakaranta, hakan yasa ragamar kula da gidan tadawo hannunsa sabida rashin lafiyar da mahaifinsu malam Salisu ke fuskanta, yau ciwo gobe lafiya, cikin ikon Allah Aminu kasuwanci yafara ha'baka, hakan yasanya malam Salisu tayar masa da maganar aure, shima dayake kamar kad'an yake jira, nan da nan ya gabatar da wadda yake so mai suna Zainab, d'iyar mai gidansace, mahaifinta ko dayaji batun yayi murna sosai, domin yasan Aminu da mahaifansa, mutane ne da kowa zaiso had'a zuri'a dasu, ba wani 'bata lokaci akai auransu, ya sanyata awani 'bangare na cikin gidan daya gyara, domin gidan babu laifi akwai girma.
Zainab asalinta shuwa arab ce, kasuwanci yakawo iyayenta nigeria, kuma Allah bai nufesu da komawaba, itace ta biyu a gidansu, tana da 'kanne uku duk maza, bayan yayanta namiji ita kad'aice mace kenan a cikin gidansu, ba acika wata guda da auransuba Zainab tasamu ciki, karkuso kuga murna wajen Malam da Inna kamar su d'au keta su goya, hakama wajen Auwalu da Suwaiba, cikinta na wata biyar akai bikin Suwaiba ta tare a can jahar jigawa ta auri wani malamin makaranta dake koyarwa a dutse, shi kuma Auwal Malam yaso ya cigaba da karatun boko shima kamar Aminu, amma shi yanuna yafison karatun addini akan na bokon, babu takura a'bangaran Malam, bai takura masaba haka yabarshi yana neman ilminsa, da Aminu yaji nan ya had'a masa kud'ad'an dayake tarawa ya turashi Saudia, domin yin karatun dayake so, Malam yaji dad'i sosai yayita sanya masa albarka.
Bayan tafiyarsa da watanni hud'u, Zainab ta haifi d'iyarta mace,mai kama da mahaifiyarta sai dai takwaso wani 'ban gare na kyawun mahaifinta, gida ya cika da murna, nanfa 'yan barka sukayi ca agidan, Suwaiba tanaji kwana uku da haihuwar sai gata agarin kano, Inna tayita fad'an mai makon tabari ana igobe tazo, tace ita dai bazata iya bari bane, ranar suna yarinya taci suna Hafsatu, Inna tayita fad'a akan me bai sanya sunan ta ba, sai da Malam yasanar mata cewa shine yarad'a sunan da kansa ai, sannan aka samu lafiya, domin Inna babu laifi akwai fad'a idan kata'bota.
yarinya ta taso cikin gata da so, ta kowanne fanni, cikin ikon Allah kuma dukiyar Abba sai 'kara ha'baka take, kasuwanci na'kara bud'ewa tako ina.
BAYAN SHEKARU HUD'U
shekarun Auwalu hud'u a saudiya yadawo gida ya kammala karatunsa lafiya da taimakon Allah da kuma Aminu yakaranci Qur'anic science, sunyi murna sosai ranar da akace Auwalu yadawo, har da Inna da Malam babu wanda yakaisu murna, domin tun da yatafi basu sake ganinsaba, sai dai dayake Aminu nad'an zuwa domin kasuwancinsa nakaishi sauran 'kashashen 'ketare, sai dai daya tashi zuwa yazo musu da abin mamakin daya girgiza kowa, bakomai bane illa ganinsa da sukayi tare da wata balarabiya shine ya girgiza kowa, amma kuma babu wanda ya nuna damuwarsa afili, har sai da sukaci abinci suka huta, sai zuwa kashe gari, sannan Malam yatarasu baki d'aya a falonsa, dayake Abba yasake gyara gidan babu laifi, yayi ginin zamani na wancan lokacin.
Malam yana kishingid'e dayake baya iya zama sosai jikin ya'kara rikicewa, bayan bud'e taro,da addu'a, Malam ya bud'e,baki da 'kyar da muryarsa da bata fita sosai“Auwalu munyi farin cikin kammala karatunka asa'a, sannan mun godewa Allah daya dawo mana da kai gida lafiya, sai dai wani hanzari ba guduba, kazo mana da wani abin mamaki da muka damu akansa, bakomai bane illa muna so musan wacece wannan dakazo tare da ita?”Auwalu yayi shiru kansa a'kasa, kafin ya d'ago ya dubi yayansa Abba, Abba ya gyad'a kai alamun yayi magana, ya gyara zamansa yana mai duban Inna data tsareshi da ido, ya sunkuyar da kai yana fad'in.