← Book details Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 23

Sashe 20

Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

tun da Haby tasamu wannan cikin Ya Nura babu zama kullum yana faman aiki akanta, motsi kad'an maitakeso?, baki d'aya yazama busy, ga aiki ga kuma Haby babu lafiya domin irin cikinnan tasamu mai laulayi.

『AFTER 3YRS 』
*****【BAYAN SHEKARU UKU】*****

Aunty Hafsat ce a daining, yayin da mijinta ke zaune bisa dainig, da yaronta dabai wuce shekaru biyuba da rabi, tana aikin serving d'insu, bayan ta kammala ta zuba nata sunad'anci, Hamza ya dubeta cike da kulawa yana fad'in "naga damuwarki ta tsananta akwanakinnan, fatan dai lafiya?" Aunty Hafsat ta ajiye cofin dakw hannunta ta dubeshi "dole kaganni cikin damuwa mana, Mama ta tada hankalinta sosai akan Nura, da muwarta ta tsananta fiye da da" "to mene nasanyawa kanta damuwa haka?, dan baya zuwa kinsan yanayin aikin sauran'kasashen waje da nan bad'ayaba, ba suna wayaba?" Aunty Hafsat tad'anyi murmushi da iyakacinsa le'banta tace "rabon da Mama koma wani yaji muryar Nura da Haby yau shekara uku kenan, tun ina da cikin Hameed nad'an watanni, lokacin bansanma ina da shigar cikinsaba" Hamza yad'an zaro idanuwa waje, can yayi shiru yanata aikin jujjuta tea d'in gabansa, kafin yace "ga shawara mai zai hana muje jigawa gurin Baffa na tsamiya goma, insha Allahu kome ake ciki ko wanne hali yake ciki zamuji" Aunty Hafsat tace "hakanefa, wallahi tsahon shekaru damuwar Mama duk tasanya namance da Baffa" nan suka 'karasa karyawa, Hamza yafice office yana fad'in "idan nadawo zamuyi magana" har bakin motarsa suka rakashi d'ansu Hameed nayi masa,byee-byee.

Nuratu tashiga d'akin da gudu tana fad'in "wayyoo Inna....!" tafad'a bisa cinyar Inna dake zaune bisa sallaya ta idar da sallah, Inna tace "ke ni d'agani, saikin karyani abanza, kullum baki da aiki sai tsalle bisa 'kafata,kin girma amma haryanzu bakibar halin yaraba" Nuratu tatashi tazauna tana fad'in "kaii Inna kullum sai kinmin gorin wannan 'kafar duk 'kashi, kuma wai na girma duka-duka shekara nawa nake?, 13yrs nakefa" "oho kekika santa" Inna tafad'a, Nuratu tasanya dariya tana fad'in "ashefa bakisan turanciba, to shekara goma sha uku nake nufi"
Inna tace "sha uku kuwa angirma, mu'azamaninmu shekara goma muna d'akin mazajenmu" Nuratu tasaka dariya, Nanace ta shigo d'akin tana d'ingisa 'kafarta, hararar Nuratu tayi tana fad'in "nidai dan Allah kibani littafina" Nuratu tajanyo littafi acikin janinta tana karanta sunan "MATAR SO" Nuratu tasanya dariya da fad'in "kowacce mace ai daman matar soce" Nana ta fizge littafin da fad'in "wasu dai ba kowacceba" tafice a d'akin, Nuratu tasake mai da kai kan'kafar Inna tanayi mata tsiya.

Tun bayan da Maman jigawa tayi aure anan kano, ta auri wani Alhaji mai mata d'aya da yara shida, matar mai kirki suna zaman lafiya sosai, yaransa kuwa nabawa Maman jigawa girmanta.
shinefa Inna takafe akan kano zata dawo, Abba yaji dadi sosai, domin dama can bajin dad'in zamanta waje daban dashi yake jiba, nan da nan aka gyara mata d'akinta dake kusa da nashi ta dawo.

su Nuratu kuwa sun kammala J.S, yanzu scondry zasu wuce ita da Nana, Rahma da Hilal ne dai sai nan da shekaru biyu zasu gama, yanzu suna gida abinsu Amma Abba yace nan da sati biyu zasu fara zuwa school, tofa su Nuratu angirma lollz.

"ehhh gaskiya Nura yana cikin matsala sosai, addu'arku yake bu'kata sosai, domin shi ba asiri akai masaba tsafi, domin shi tsafi abune mai wuyar karyewa, sai andage sosai, amma kuma babu abinda yake gagarar ubangiji, domin mu dashi muka dogara" Aunty Hafsat suka dubi juna da mijinta, Baffa yacigaba da fad'in "shima kuma da nasa sakacin baya addu'a kokad'an, sannan yana da sanya son abu aransa sosai, da wannan damar akaci galaba akansa sosai, kuyi ha'kuri zuwa gobe insha Allah zanyi istihara akansa, duk halin da ake ciki zansanar miki awaya" Aunty Hafsat tace "to mungode sosai Allah ya'kara girma" sun shiga gidansa, sunyi salla suka sha fura, kafin su sake d'auko hanya zuwa garin kano, suna tafe suna tattauna maganganun da Baffa yasanarmusu, ana kiran sallar maghriba suka isa kano, kai tsaye gidan Mama suka wuce domin Hameed nacan, acan suka barshi.

Aunty Hafsat tashige gida, shi kuma ya nufi masallaci?, tana shiga Hameed yakama yi mata oyoyo tad'aukeshi suka nufi d'akin Mama, lokacin Mama nakan abin sallah ta idar da sallah, Aunty Hafsat kasancewarta na hutun sallah zamanta tayi bisa gadon Mama, Mama nayi mata sannu da zuwa, nan tafara sanarwa Mama dukkan abinda Baffa yafad'a mata, Mama kamar tayi kuka dan takaici da tausayin d'annata, nanta sake kallon gabas tana sake koro addu'o'i akansa akan Allah ya shiga tsakaninsa da ma'kiyansa yakarkato mata da d'anta zuwa garesu.
[09/01, 22:31] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book1

mallaka-----QURRATUL-AYN

27

《MALESIA》

Abubuwa da dama sun faru azaman Haby da Nura koma ince suna kan faruwa, tunda Haby tasan tariga ta gana da Ya Nura, sai kuma tamai da kai akan harkokinta, yanzu babu 'kasar da bata zuwa dasunan kasuwanci, ayanda ta sanarwa Ya Nura kenan, sai dai abinda bai saniba shine, duk wani shaid'anci da bin maza tanayine ta wannan hanyar, da zaran zuly ta bugo mata waya tana sanarmata, anyi order kayan mata zuwa 'kasa kaza, to wasu hajiyoyinne ke bu'katar harka da ita a'kasar, ko kuma tace mata kayan maza zuwa 'kasa kaza to tasan wasu alhazawanne a'kasar ke bu'katarta.
Haby ta'bud'e tacika tayi fam, kud'i sun zauna mata, yanzu bata kallon Ya Nura amatsayin komai, domin ayanzu bazai nuna mata kud'iba, sabida ana hayar Habyne kan naira mai gugar naira ahar million guda, babu harkar da Haby batayi tun daga kan lesbian har zuwa kan mazan, ga uwa uba babbar 'kungiyarsu data bun'kasa ako ina, domin da bazar 'kungiyar suke taka rawa acewarsu baza'a ta'ba gano sirrinsuba, wannan abubuwan da Haby keyi, duk yana daga cikin umarnin 'kungiyane domin haka harkokin 'kungiyar yake koma waye yake ciki, abinda zaiyi kenan namiji ko mace, Haby tasamu damar fin kowacce mace dake cikin 'kungiyarne, kasancewar dukkan abinda aka sanyata tanabi, kuma sannan ta bawa 'kungiyar had'inkai 100%, kuma tabasu dukkan abinda sukeso.

Ya Nura kuwa haryanzu baisan su Zuly na malesia ba, haka kuma baisan abinda ke tsakanin Sholy da Haby ba, haka kuma baisan gaskiyar cin amanar da Haby keyi masaba.

a halin yanzuma Haby nada motar kanta har guda biyu nakusan million shida-shida, da sunan da kud'in kasuwancinta tasiya.
Yanzu Haby babu ruwanta da Ya Nura taharkar auratayya idan kuwa yana bu'kata sai yabiya, daya gama abinda zaiyi zatace masa barci takeji, da zaran taje d'akinta to sholy zata kira, suyita harkarsu shed'an na'kara kad'a musu gangarsa, domin yariga yagama shinfid'arsa acikin zuciyoyinsu, har takai takawo ko yana zaune afalone sukan shige d'akinta surufo 'kofa suna harkarsu, sukwana tare abinsu, harka da Haby keyi da Sholy ya'kara bud'e idanuwanta sosai, har take ganin su Zulyma 'kananun kwarine, yanzu harya zamana bama tason harka da maza sosai sai mata musamman Sholy, sabida yanzu a'kungiyarsuma ta d'aura musu aure tare, zuna zaman miji da,matane (subhannallaha, astagfirulkah wa'atubi ilaik).

Ya Nura kuwa idan ba wanda yasanshi sosai ba, bazaka iya shaidashi ba, yayi fari sosai yad'ashe, yad'an rame kad'an, sai hakan kuma ya'kara masa kyau sosai loll.
ya Nura yana harkokinsa kawai, amma yamance da yana da 'yan'uwa a nigeria, asalima yamance cewar nigeria mahaifarsace, an mantar dashi kowa da komi, illa aikinsa da Haby sune kad'ai bai manceba.
Haby kuwa bawai tamance da kowa bane, a'a kawai dai aganinta yanzu tafi 'karfinsu, tunawa dasu zai iya wargaza mata duk wani shiri natane, sannan za'a iya fahimtar halin da take ciki, hakanne yasa tayi banza da duk wani nata, tasanya harkokin gabanta kawai takeyi.
(NASAN MASU KARATU ZASUCE INA CIKIN DA HABY KE DASHI?, KARKU DAMU KUDAI KUCIGABA DA BIBIYATA, ZAN WARWARE MAKU DUKKAN ZARE DA ABAWA NAN DA LOKACI KA'DAN).

《NIGERIA》

Tsaye yake cikin harabar gidan, jingine jikin motarsa ba'ka, cikin 'kananun yara blue d'in riga da ba'kin jeans, hannunsa ri'ke da waya yana daddannawa, Hamzane yafito cike da fara'a yabashi hannu suka gaisa, kafin yace "sai dai ban shaidakaba" yad'anyi murmushi kafin yace "Khamis ne abokin Nura, nazo wajen Aunty Hafsat ne" "ohhh Allah sarki, shigo mana" Hamza yace, suka jera da Khamis har zuwa cikin falonsu, yace "bismillah zauna, bari inkirawo maka ita" yahaura zuwa sama, d'ansu Hameed yazo da gudu yad'ane cinyarsa yana fad'in "uncle yakake?" Khamis yace "lafiya, yasunanka?" "Abdul-hameed, amma Hameed akecemin" "woww suna mai dad'i" Khamis yafad'a, Aunty Hafsat tasauko tana fad'in "a'a kace babban ba'kone agidan namu, kazo kahad'u da d'an surutu ko?" Khamis yayi murmushi yana gaishe da ita, Aunty Hafsat ta amsa kafin tace "maza Hameed jeka wajen Dadynka yana kira" yaron yami'ke da gudu yahau saman.

Aunty Hafsat ta kwalawa mai aikinta kira, sai gata da saurin, tace "maza kawowa ba'kona abin ta'bawa" mintuna kad'an sai gata d'auke da 'katon tire taja table gaban Khamis tad'ora ta fita, Khamis yad'an zuba lemo yasha, sannan Aunty Hafsat tace "kaima ka'buya kamar abokin naka" Khamis ya ajiye cofin lemon yana fad'in "nasan dama zakuce haka, amma nidai 'buyana akwai dalili, kamar yanda nayi miki al'kawari, saura kad'an na'karasa cikawa" Aunty Hafsat tad'an dubeshi da fad'in "banganeba, al'kawarin me kuma kamin?" Khamis yad'anyi dariya kafin yace "maganar gaskiya daman nazone domin muyi magana mai muhimmanci" Aunty Hafsat tad'an gyara zamanta kafin tace "to Allah yasa inji alkhairi inajinka".
Chapter 20 · 0% Book details