← Book details Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 23

Sashe 18

Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama tayi ajiyar zuciya da fad'in "nidai ancuceni wallahi, Allah ya isarmin" Aunty tace "addu'ar daya ro'ka itace yadace mudinga yimasa ko da yaushe, domin itace kad'ai zata fidda shi daga halin dayake ciki ayanzu" "hakane gaskiya kika fad'a" Mama ta bata amsa, Aunty takau da hiran da kawo wata hiran daban, dan kada Mama tasa damuwa acikin ranta.

Haby ta dubi Momynta dake tsara mata kwar-kwasa da yanda zata janye hankalin Nura akan kowa, tayi tsaki kawai tana binta da kallon wula'kanci, can tayi murmushi tana fad'in "ai ni duk Momy bazan zauna ina wannan abunba akan d'a namiji, domin ni yanzu nagama da Nura bana bu'katar dukkan wad'annan" Momy tace "iyeee kaji yarinya 'yar zamani wai menene sirrinne?" dai-dai sanda Ya Nura yayi sallama falon, wani kallo Haby tawatsa masa wanda yasanyashi rud'ewa da rawar jiki ya'karasa yana bata ha'kuri, awula'kance tami'kamasa jakarta tana fad'in "ungoni maza kaimin mota kadawo bana son 'bata lokaci kuma" cikin tsawa tayi maganar, Ya Nura yakar'ba jiki na'bari yafice, Haby da Momynta suka tafa, MOmy tace "d'iyata taya hakan tafarune?" Haby ta ta'be baki da fad'in "wannan kuma sirrinane, wanda jinsa dai-dai yake da rasa ranki, zamu wuce malesia idan munje zankiraki a sim nawa banson yawan kira kinsan bana son takura" Momy tasaki baki tana duban 'yar tata cike da mamaki koma mafarki takene, Haby ta ajiye mata,bandir 'yan duba akan cinyarta tace "ga wannan akashe nasan shine burinki" tayi murmushi kawai, Momy tace "ah aishikenan kitara mana da yawa, tunyanzu nasamu kyautar wannan bare kuma zuwa gaba" Haby tayi murmushin da iyakacinsa fuska kawai, tana duban Momynta dake lissafin kud'in, tasake zaro wasu rafar tace "ungo kirabawa Kamal da Khaleel" dai-dai sanda Nura yadawo tace "muje ko" suka fito Momy na aikin sanya musu albarka.

ko sallama bata,bari sunkoma sunyiwa su Mamaba tace su tafi, haka yata da Mota yabar gidan, dan ma Allah yasa Abbansa bayanan addu'ar da yaitayi aransa kenan, har suka tawo kuwa baidawoba, sai bayan tafiyarsu ya dawo Mama ce tasanar masa da zuwansa yayi farinciki sosai, domin shi aganinsa alkhairi yahad'a, sai awaya yakira Nuran yayi masa addu'ar fatan alkhairi.

6:00am

shidda dai-dai jirgin Malesia yad'aga, Khamisne ya kaisu airpory, bayan magiya da Ya Nura yayi tayima kan dole yazo yakaisu dominshibaki d'aya yagama tsanar Haby, bayan haka kuma yayarda yakawosune kozai samu makama domin sanin wacece Haby?, sai dai babu abinda yasamu har jirgin nasu yad'aga zuwa malesia, yadawo gida cike da tunane-tunanen ta inda yakamata yafara.

《MALESIA》

Airport d'in malesia fasinjojin tane suke sauka a hankali, garin gwanin ban sha'awa da d'aukar ido, cikin fasinjojin har da Ya Nura da Haby, Haby tasha'ki iskar malesia tare da sauke wata ajiyar zuciyar, motocin sojoji ukune manya ajere sai 'kananu biyu sune sukazo tarbar Ya Nura, abin yabawa Haby mamaki, ashe shid'in wani babbane a sojojin abinda bata ta'ba saniba sai yau, suna saukowa sojojin sukahau sara masa cike da girmama aka bud'e masu murfin motar da zasu shiga, kayansu kuwa d'aya motar daban aka sanya, driver yaja mota, basu tsaya ko inaba sai barrek d'insu, anan akaiwa Ya Nura masauki na musamman gida guda nasa, duk inda suka wuce sara masa ake, gateman kansa sojane banda wad'anda ke shawagi aharabar gidan.

Haby bata 'karatsinkewaba sai da suka shiga gidan, taga gida kamar a film nanfa ta cika da murna da farinciki, har tafara ayyana irin rayuwar da zatayi agidan.

bayan sunyi wanka sun shirya kukune yazo yana sanarmusu angama shirya abinci bisa daining, can suka nufa nanfa Haby taga abinci kala-kala wanima batasan mene ba illa kawai takalla.

ciyar da junansu sukai cike da so da 'kauna, domin Haby jinta take wata daban, auren Ya Nura yaga mata komi, saura cin duniyarta da tsinke kawai, da suka kammala d'aki suka nufa domin yin barcin gajiya.
[07/01, 22:06] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book 1

mallaka-----QURRATUL-AYN

24

《NIGERIA》

Bayan kwana uku da tafiyarsu Ya Nura,misalin 3:30pm
Abbane zaune falonsa bisa daya daga cikin kujerun d'akin, hannunsa ri'ke da jarida, fuskarsa d'auke da wani farin glass wanda da dukkan alamu na 'karin ganine, Mamace tayi sallama tashigo, Abba ya ajiye jaridar hannunsa yana amsa mata, tami'ko mai lemon data tsiyaya awani cup na glass, yakar'ba yana godiya, tazauna bisa kujerar kusa da shi, sai da yasha ya ajiye sannan tafara magana da fad'in
"Alhaji yaronnan kuwa ya kiraka tunda suka tafi shiru babu wani labari, duk nashiga damuwa wallahi" Abba ya d'anyi murmushi da fad'in
"bai kiraniba, amma nasan zaikirani domin inaji ajikina lafiya suke, sai dai idan aikine yari'keshi" Mama tace "to Allah yasa dai lafiyan" amin " Abba ya furta tare da d'aukan jaridarsa yacigaba da karanta, turo 'kofar falon aka sakeyi, cikin sallama, Mama ta amsa, Momyce fuskarta fal murmushi tashigo hannunta ri'ke da waya, ta fara fad'in "Alhaji gashi Haby ce takira waya, tace abaka" Abba yakar'bi wayar yana dariya yakarata bisa kunnansa, yana fad'in
"kuna lafiya dai ko?, to masha Allah ina Nuran yake?" can tabashi amsa da fad'in "yafita office tun safe, idan yadawo nasanarmasa yakiraku" "toto Allah taimaka ki gaisheshi", takashe wayyar.
Abba yami'kawa Momy wayar dake tsaye, ko zama bataiba tafice, Mama tad'anja tsaki aranta kawai, Abba yace "kinga abinda nake sanarmiki ko, nasan ai suna lafiya dama, shid'in aikine yayi masa yawa, kinsan aikin can da nan ba d'ayaba" Mama tace "uhmmm" kawai tama rasa mai zatace, hakan yasanya tami'ke ta koma d'akinta.

"Ammy waike ina 'yan'uwanki sukene? kowa naga 'yan'uwansa nazuwa gurinsa amma bandake, Mama nada nata Auntyma haka, Momyn Haby ma haka, kuma naga ke duk bakwa kama ke kamarku d'aya da indiawa kuma.....!" "ke ya isa, meye haka Nuratu? bana habaki yimin irin wad'annan tambayoyinba?" Nuratu ta tura baki gaba "amma Ammy Allah nidai inason ganinsu, nifa naga bana kama dasu Nana, kuma kowa haka yakece dake da 'yan'uwanki nake kama, wai kyau yayimin yawa sai kace aljana, hakane Ammy?" " ya Ilahi ohhh! ni Amina..!wai ke bakyajin maganane? nace ban saniba" "kinga idan bazaki rufemin bakiba zaki d'agani wallahi" Nuratu tasake gyara kwanciyarta bisa cinyar Ammynta, tana sonyin magana, amma tasan Ammy bazata kulataba, hakan yasanyata yin shiru tacigaba da kallonta.

《MALESIA》

'Dinnn....d'innnn..! 'karar 'kararrawar 'kofar falon ketashi wanda da dukkan alamu ba'kine, Haby dake kwance bisa tafkeken gadonta, cikin wani lallausan bargo tana aikin barci, tafarka cike da barci idonta, ta zuro 'kafafunta tasanya wani takalmi mai taushi, daga ita sai wata guntuwar rigar barci tafito zuwa falon tunaninta Nurane cike da tsawa take fad'in "wai wayene?" "bud'e kigani" Haby tabud'e 'kofa da sauri, jin muryar wadda bata zataba, ai kuwa Zulynce da gaske, su ukune Zuly sai Baby sai wata da bata santaba, suka rungume juna cike da murna, saiga Nabeel tsaye bakin 'kofa, nanfa ta'kara cika da mamaki sosai, shima sund'an cafke irin na ri'ka'k'kun 'yan barikinnan, kafin su zauna kuku yafara yimusu serving d'in abin ta'bawa.

Zuly ta'karewa falon kallo, ta dubi Haby tana fad'in "shegiyar irin wannan daula haka, ai dole kimance da mu" Bby tace "wallahi kuwa, jidai yanda ta'kara kyau" NB yace "duk za'kin sabuwar zuma, tsohuwar zuma tafita" suka sanya dariya baki d'aya, yayin da Nabeel keta bin Haby da wani irin mugun kallo, wanda duk sai da suka fahimci kona menene, nanfa suka fara tsokanarsa Zuly tace "kai malan kamai da maitarka kasan gidan wanda muke dai kada kaja duk aharbemu" Haby tasanya dariya da fad'in "shid'in banza" suka sake sanya dariya, Nabeel yace "ai wallahi naji dadin shirya plant d'in zuwanmu", Haby tace "baku kainiba".
Zuly tace "duk ba wannanba muyi abinda yakawomu, Haby ga Sholy nan, itace wadda nakawo muki matsayin 'yar aiki, kasancewarmu mijinki duk yasanmu ma dinga zuwa, amna itama Sholy 'yar hannuce sosai zakiji dad'in harka da ita" "wowww Wallahi kin kyautamin sosai, daman ina cikin kewa wallahi, har dai idan wancan saunan yafice aiki" suka sanya dariya, Nabeel yace "to ni ya za'ayi dani" Haby tad'an harareshi da fad'in "wuce bedroom muyi magana, sud'an jiramu" Bby tace "ayi haka kuwa?" Haby tayi dariya tami'ke tana fad'in "gobe ko jibi kuma saimu tattauna daku" suka sanya dariya, Sholy ta bud'e jakarta ta fiddo da kayan shaye-shaye tami'kawa Zuly da Bby, Nabeel kuwa da Haby tuni sunwuce bedroom XX, (ohh Allah ka shiryamu, kashirya bayinka irinsu Haby amin, kan gadon mijinka kakai wani katon gardi Allah ya kyauta).

kafin Ya Nura yadawo gida babu kowa kaman ba'ayi zuwansu Zulyba, domin Ya Nura baimasan suna 'kasarba, bare kuma har suzo gidan, agajiye yashigo cikin falon ya yada laptop d'in hannunsa da sauran tarkacen yakwanta bisa doguwar kujera dake falon, can Haby tafito daga kitchen hannunta d'auke da d'an flat da yankakkun kayan fruit aciki tanaci, zuwa tayi tazauna ahannun kujerar dai-dai kansa tafara magana
"Nura...!" tafurta babu kod'an risinawa, Ya Nura yabud'e idanuwansa ahankali yana dubanta, batajira taji mai zaiceba tafara fad'in "daman maganace zamuyi, nasamu 'yar aiki itama 'yar nigeria ce, zata dinga tayani wasu abubuwan, tun da kai naga yanzu bana gaban nasamu mai tayani hira" Ya Nura yami'ke zaune yana dubanta kawai kafin yace "shikenan hakanma yayi, amma batun bana sonki bai tasoba kawai dai ayyuka sukaimin yawa amma insha Allah nan da 2week komai zai zama normal, kinji karki damu" ya'kareshe maganar yana d'anjan kumatunta, murmushi tad'anyi kawai, har yami'ke ya nufi bedroon d'insa, tabi bayansa da harara tare da guntun tsaki tana fad'in "ni dama kadauwa a aikin nahuta nima ai", haka kawai kwanakinan takeji auren da zaman gidan duk ya gundureta.
Chapter 18 · 0% Book details