← Book details Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 23

Sashe 2

Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“wai kuwa Nana yaushe Ya Nura ya dawo?”Nuratu tayi tambayar tana ri'ke ha'barta na mamaki, irin wata babbar nan, Nana ta d'an ta'be baki tana fad'in “nima muna tashi da safe muka ganshi zaune a daining, bakiga masifar da mukashaba da Abba yace yakawomu school, shinema yace bazai jirakiba " “mugu kawai ni wallahi har bana so yadawo idan yatafi, duk yazo yahanaka sakewa”Hilal yafad'i yana tsaki, Nuratu tace “kaima dai kafad'a ai yau nasha wuya, banda Allah yasoni da tuni a'kafa zanzo tun daga gida”“zuwa nan school d'in???”Nana da Hilal da Rahma suka had'a baki wajen fad'a, Nuratu tayi dariya “bari in baku labari”nan Nuratu ta basu labari kaf, sunji mamakin abinda Nuratu tayiwa Yayan nasu, Hilal dayake shine 'karaminsu gashi yafisu tsoro sai zare ido yake, hakan yasanya dariyar tadawo kanga, 'kararrawar komawa class da aka buga itace tayi sana diyan tashinsu daga hiran kowa ya nufi class d'insu, kasancewar ba class d'aya sukeba, Nana da Nuratu ne suke class guda, Hilal class d'insa daban Rahma ma haka.
[19/11/2017, 23:33] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》🌈🌈🌈Book 1

MALLAKA......QURRATUL-AYN
03

*** *** ***

Yana parking motar cikin harabar gidan suka fito aguje zuwa ciki, kai tsaye babban falo suka nufa suna shiga suka hau wurgi da jakar makarantar tasu tare da ciccire unifoam d'in, ko wanne acikinsu yazauna dagashi sai best da pant wanda bai kai gwiwaba, babu batun sanya d'an kwali ko hula, illa gashinsu da ya zuba bisa kafad'unsu, dan su Allah yahore masu yalwar gashi, Hilal kai tsaye d'akin Mamansu ya nufa yana kwala mata kira, su kuwa zama sukayi suka kunna kallo.

idanun Nuratu yasauka akan wayar dake jone jikin chaja afalon, ta dubi Nana “Lah Nana kinga wata waya mai kyau”tafad'a sanda takai hannu tana d'aukota, tadawo kusa dasu tazauna tana dariya, “kunnata mugani ta wace, ammafa tayi kyau wlh kinsan tafi ta su Mama”cewar Rahma, Nuratu takunna waya 'kirar Iphone6 suna ganin babu password ai kuwa suka hau kokawa kowa nafad'in abashi ya gani, Nuratu kuma ta hana, har abin yakai kaman zasuyi fad'a basuyi auneba sai ji kake tasss, 'karar fad'uwar wayar, da sauri Nuratu tasunkuya tad'auko wayar gaba d'aya screen d'inta yafashe, gaba d'aya suka zaro idanuwa, tsaki Nuratu taja tana fad'in “gashinan kunja tafashe, ko gani bamuyiba, gashi bamusan ko ta wace bama....”tayi shiru tana duban waya “mu mayar jikin chajin mugudu kawai, kuma kada wanda ya nuna yasan tafashe acikinmu”Nana tafad'a, Nuratu tace “good idea”ta mayar jikin chajin da gudu suka kwashi kayansu sai d'akinsu suna dariya, kan gado suka fad'a.
“yanzu idan ta Ya Nura cefa”fad'in Nuratu, Rahma tazaro ido tana dafe 'kirji “munshiga uku ai yau sai yakusa kashemu, dan kinsan sojoji basu da imana”Nana tayi ta gumi jin abinda Rahma tafad'a Nuratu tace “ku daina majin tsoro ai babu wanda yasan mu muka fasa, kuma sarkin tsoro Hilal baya nan”jin hakan yasanya suka saki jikinsu suna harkokinsu.

Dawowarsu kenan daga islamiyya, suna tafe akan hanya kasancewar islamiyyar tasu babu wani nisa tsakaninsu da gida, wata yarinya tazo zata wuce takusa da Nuratu itama da alamu daga Islamiyyar take dan kalan unifoam d'insu d'aya, doguwar riga koriya da farin hijab, cikin zafin nama Nuratu tajawo yarinyar tana fad'in “ke ummi kike kowa?, d'azu wakike cewa aljana?”“nifa ba dake nakeba”yarinyar tafad'a, Nuratu tasa hannu tad'auketa da mari, Rahma da Nana suka 'kara mata wani, dai-dai sanda yayun yarinyar maza suka kawo kai su biyu, nanfa fad'a yakaure, kasancewar unguwar babu jama'a sai 'yan makarantar kawai dasuka zagayesu suna kallo, ana masu wa'kar su sasu, cikin fad'an yayan yarinyar d'aya yad'au dutse ya bugawa Rahma agoshi nan kuwa jini ya'balle, cikin zafin nama Nuratu tana fad'in “wallahi sai munrama”tad'auki dutsen itama tarotse kan d'aya yayansu shima sai jini kuwa, tana niyar bugawa yarinyar taji anri'komata hannu bata jutaba takalli kowayeba tahau fizgewa tare da fad'in “ni cikani wallahi duk sai na fasa musu kai”jikake tasss and'auketa da mari da sauri ta juyo taga Ya Nura cikin 'bacin rai nan tayar da dutsen tana kallonsa, hannuwansu yahad'a baki d'anyansu yazubasu amota har su Ummi d'in, kai tsaye clinic yanufa dasu aka wanke masu ciwon tare da basu magunguna, duk suka had'a ido da Nuratu wani mugun kallo yake watsa mata, wanda yake sanyawa hanjin cikinta 'kullewa.

sai da yakai yaran gida tare da bawa iyayen yaran ha'kuri, duk da dai bai tambayaba amma yana da tabbacin Nuratu ce da laifin komai, sannan suka nufi gida, lokacin an idar da sallar maghriba ma, Mama da Aunty da Abba sunyi jugum-jugum a babban falo, Aunty Amarya tashigo tana wani yau'ki da taunar cingum d'aurin d'an kwalin kanta irin wanda ake kira (gobarar mata ne), kusa da Abba tazauna tana fad'in “lafiya dai Alhaji na, yau duk nayi kewarka amma kazo kazauna anan kasanfa ruwan wanka da abinci nanan na jiranka”yanda take maganan da wani shishshige masan da take yasanya Mama da Aunty kallon juna, Abba yad'an matsa kad'an cikin jin kunya, tare da fad'in “ai kinsan ina kan hanya, nazo natarar da yarana har maghriba basa gidane, wai fad'a sukayi har da fasa kai ”cikin salo na kissa Aunty Amarya ta dafe 'kirji tana mai fad'in “subhanallahi waye yakawo maka wannan mummunan labarin Alhaji na?”“gashinan Hilal ne”Aunty Amaryar tahau matsar kwalla kamar gaske tana rarrashen Abba wai ita adole mai miji, su Mama kuwa sai suka zama 'yan kallo, tama nuna tafisu damuwa, Mama kai kawai ta girgiza tare da d'an guntun murmushi daya tsaya iyacin le'banta, Aunty kuwa harara taketa aikin aikawa Aunty Amarya zuciyarta na 'kuna.

Da sallama yashigo falon, baki d'ayansu suka amsa masa, yayinda su Nuratu suka rufo masa baya ga Rahma goshi afashe, suka zauna Abba yahau tambayarsu “ya akai hakan rafaru”“sai dai ka tammbayesu Abba, nima akan hanya nagansu Nuratu d'auke da dutse a hannu”Abba yakai dubansa gun su Nuratu yana tambbayarsu, Nuratu da dai niyarta tashirga masu 'karya amma sai tasamu kanta da kasa yin hankan, nan tafad'i gaskiiyar abinda yafaru, nan fa ran Ya Nura ya'kara 'baci yahau fad'in “dan ankiraki da aljana sai me daman ai dasu kikafi kama, wawuya maraji kawai wallahi sai in'ballaki kowa ya huta 'yar kauye”“kai Nura ya isa haka agaban nawa, kada kasake yi mata irin wannan”cewar Abba, ita dai Mama ta rungume Rahma tanajinsu kawai, batace komaiba hakama Aunty, Abba yace “tunda Allah yatsai da abin haka shikenan kada insakejin anta da zancen, ita kuma uwata Allah bata lafiya, kowa yaje yayo sallah”Abba ya mi'ke zai fita, Aunty Amarya tami'ke tabi bayansa tana kwarkwasa, Nuratu taja wani mugun tsaki da har sai da yasa Aunty Amarya juyowa ta zabga mata wata uwar harara, Ya Nura yabugewa Nuratu baki, ta murgud'a masa bakin tare da fad'in “Allah ya isa na”tayi d'akin Mama da gudu, zai bita Mama ta dakatar dashi tana fad'in “ka wuce masallaci kada kabi yarinyar nan”Ya Nura ya dubi Mama kawai yajuya yafice.

“Gaskiya Yaya ke kike 'kara sangarta 'yar nan wallahi”cewar Aunty, Mama tayi murmushi “kema dai Auntyn Nura, kin mance wacece Nuratu ne, kinsan dai ko kasheta zaiya Nuratu baza fasa fad'in Allah ya isa ba, tare da rashin kunya, da ace Nuratu zata daina rashinji da tuni ta daina, ni kaina wani lokacin Nuratu tsoro take bani wallahi, addu'ar shiriya kawai zamu dinga yi mata”“to Allah dai yashirya mana, bari inje inyi sallah”cewar Aunty tana mi'kewa, Mama tace “amin dai nima tashi zanyi yanzunnan”Aunty amarya tafice daga falon.

Mama....mama..! Ya Nura ke kwala mata kira yana mai niyar shiga d'akinta, sai gata itama ta fito tana fad'in “lafiya kuwa Nura?, wannan kira haka?”“kalli wayata Mama daga jonawa achaji, mancewa nayi da ita nafita wallahi, nasan aikin yaran nanne”Mama tari'ke baki ganin screen d'in waya akwankwatse, suna tsaye sai ga Hilal yakawo kai zai nufi d'akinsu Nuratu, Ya Nura yari'keshi yana tambayarsa, Hilal har da kukansa yana fad'in bashi bane, kuma bai san wayeba, ganin hakan yasa Ya Nura rabuwa dashi dan yasan Hilal da tsoro da tuni yafad'a masa gaskia, “tashi jeka kiramin su Nana”Hilal yatashi da gudu yatafi kiransu, Ya Nura yazauna a kan d'aya daga cikin kujerun falon yana kallo, sai gasu sun fito jiki babu kwari, suka zube agabansa tare da fad'in “gamu yaya”wani mugun kallo yawatsa musu, gami da harara bai ce musu komaiba hannun Nana yakama yanufi d'akinsa da ita, nanfa 'yan hanjinsu tafara 'kullewa, sai da yaje dai-dai bakin 'kofar sannan yajuyo yana fad'in “idan nafito naga kintashi daga inda kike zaki sani”yashige cikin d'akin yana mai jan hannun Nana, Nuratu tabisu da kallo tana addu'a aranta.

mintuna biyar sai gasu sunfito fuskar Nana hawaye sha'be-saha'be, suna had'a ido da Nuratu ya buga mata wata uwar harara, ta sunkuyar dakai da sauri, ya dubi Nana “maza wuce d'aki kiyi barci, zanzo d'akin ingani idan baki barcinba”Nana tawuce da gudu, yazo kan Nuratu yatsaya kafin yasa hannu yari'kota itama, d'akin nasa ya nufa da ita, yana shiga ya mai da 'kofa ya kulle, hakan yasaka hankalin Nuratu 'kara tashi matu'ka, kai tsaye gefan tamfatse tsan gadonsa yazauna, ita kuma ta tsuguna agabansa kanta a 'kasa, “ke”yakira sunanta, da sauri tad'ago idanunta, wata 'karamar bindiga ta gani ahannunsa nan Nuratu ta 'kara fiddo da idanuwanta daman ita ga ido tubarkalla, dubanta yatsayayi sosai kafin yafara magana “yau laifinki uku ne aguna, amma babban laifin fasamin wayata, mai yasa kika fasa?”“bani kad'ai nafasaba wallahi Yaya”Ya Nura ya watsa mata wani kallo kafin yace “nasan bake kika fasaba, amma kece sila, ba daman nace laifi uku ne akankiba, kuma yazama dole na hukuntaki akansu”
Chapter 2 · 0% Book details