Sashe 3
Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yayi shiru yana dubanta kafin yad'ora da fad'in “za'bi d'aya gareki, ko dai in harbeki yanzu ki mutu ko kuma ki kwana azaune babu barci”jin hakan da Nuratu tayi shiyayi sanadiyya zubowar fitsarin dake ri'ke a mararta, matsowa tayi tari'ke 'kafarsa 'kam tana fad'in “kayi ha'kuri Yaya wallahi bazan sakeba, nidai banaso in mutu yanzu inbar Ammy na dasu Nana da Abba da mama”maganar taso tabawa Ya Nura dariya amma sai ya matse abinsa, ya dubeta dakyau, ya'kara tabbatarwa Nuratu yarinyace sosai, wani guntun murmushi yayi yana fad'in “saifa kinza'ba ”Nuratu tayi shiru tana sharar 'kwalla kafin tace “naza'bi inkwana azaune, dan bana so in mutu yanzu”yanda tayi maganar da abinda tafad'a sai da yasanya Ya Nura murmusawa, yace “is ok, yanzu saiki tsugunna kid'aga hannuwanki sama, ahaka zaki kwana”ba musu tayi abinda yace mata, dan duk atsorace take gani take kaman zai iya harbeta koyaushe, shi kuwa kwanciya yagyara ya'dora bindigar akan 'kirjinsa yakashe hasken d'akin yaja bargo abinsa yabarta nan tsugunne, motsi kad'an idan tayi sai taji yace “ina kallonki idanma guduwa zakiyi bismillah.”
[20/11/2017, 18:18] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》🌈🌈🌈Book 1
MALLAKA.....QURRATUL-AYN
04
Barcinsa yake shi hankalinsa kwance abinsa, jin da yayi anta'bashine yasanyashi farkawa, ganinta yayi tsugunne bakin gadon kanta kuma nakan hannunsa dake gefan gado tana baccinta, ya kunna globe d'in d'akin haske yagauraye amma ko kusa bata farkaba, domin baiyi kwakw-kwaran motsin dazata farkaba, duban agogon dake manne jikin bango saitin gadonsa yayi, yaga uku da mintuna goma lokacin, ajiyar zuciya yayi kafin yadawo da kallonsa kan Nuratu, gashinta kwance bisa fuskarta, tana sanyane da wata guntuwar rigar bacci, mai 'karamin hannu iyakacinta gwiwarta, yasa d'anyatsansa d'aya yajanye mata gashin daya rufe mata fuska, yana bin ilahirin fuskar da kallo, kafin yayi tsaki mai tsayo yakoma yakwanta, amma bai kashe hasken d'akinba, yanajin tsanarta sosai aransa, shi dai yarasa dalilin dayasa yatsani Nuratu duk da tana 'yaar'uwa agareshi, amma yatsaneta shi ko kyawunta da yakanji mutane nafad'a har da abokansa shi dai baita'ba ganiba, mai makonma idan yakalleta yaga kyawun sai dai kawaai yaji tsanarta nabin dukkan jikinsa, “meyesa natsaneta?”yayi tambayar kusan afili, wani gefe nazuciyarta yabashi amsa “sabida rashin kunya da raashin ji mana”yayarda da amsar da zuciyarsa tabashi, tsakin dai yasakeyi yana mai janye hannunsa da 'karfi, hakanne yayi sanadiyar buguwar goshinta jikin katakwan gadon, a gigice tafarka tana goga wajen, ta turo baki gaba yayin da take murza idanunta, firgigit ta koma ta tsuguna sabida tunawa da tayi a cikin d'akin wanda take, shi kuwa ya kafeta da shanyayyun idanuwansa, yana binta da kallo, tsoro ya'kara kama Nuratu sosai “kayi ha'kuri Yaya, nadaina insha Allahu bazan kumaba, dan Allah kabarni inje inkwanta.....!”ta'karashe maganar tana mai share kwallar dake shirin zubo mata.
Ya Nura yayi murmushi kafin yace “kwanta nan inda kike, kuma bana son wannan kukan ”Nuratu tagyad'a kai, takwanta ta takure waje guda, ko mintuna biyu da kwanciya ba tayiba barci yad'auketa.
ko da tafaarka da asuba ganinta tayi anrufeta da tattausan bargo, sai tashin 'kamshi yake, har tasake juyi sai tatuna da abinda ya faru jiya, ta mi'ke da sauri jin motsin ruwan da tayi a toilet yasa ta nufi 'kofa tana sand'a, tana zuwa tafice da gudu sai d'akinsu.
。。。after 1 week。。。
“Ammy wai dan Allah mai yasa Ya Nura baya sonane?, yana takuramin wallahi, ni duk natsaneshi....y”buge mata bakin da Ammyn tata tayine yasanya Nuratu dakatawa daga abinda take shirin fad'i.
“in kumaji kince kintsaneshii, d'an uwan naki guda, kina da wanda yafishi ne?, sakarya kawai to ba dole kowa yadinga jibgarkiba tunda kinza'bi hakan Nuratu, ni aduniya nata'ba ganin yaro maraji irinki, idanshi baice yatsaneki ba ke har kina da bakin fad'ar hakan, tashi ki bani waje, na kuma jin bakinki yafurta hakan”.
Nuratu tatura baki gaba tana fad'in “ni wallahi Ammy dan bakisaan abinda yakemin bane, cewafa yakeyi zai kasheni da bindigarsa”“to yakashekj mana ina ruwan wani, kowama ya huta”jin abinda Ammy tafad'ane yasanya Nuratu 'kulewa, tami'ke daga wajen Ammy dake yankan farce, mai makon tayi d'aki sai tayi waje abinta.
Tana fita gidansu Nana ta nufa, domin rabonta da gidan tun randa Ya Nura yasata baccin zaune, tana shiga gate d'in ta gamu da Nana da Hilal da Rahma suna wasa, ta 'karasa wajensu da sauri tana,harararsu “shine sati guda banzoba kuka 'ki zuwaa gidanmu ko?”cewar Nuratu tana kallon Nana “ya Nura ne yahanamu zuwafa”Rahma tafad'a, Nuratu tazauna akan ciyawar wajen, duk suka kewayeta, kamar wata sarki da mu'karrabansa, “kunsan wani abu?”“A'a”suka fad'a atare, “yau lambun gidansu zainab nake son zuwa musha mangwaro, kuzo muje”Nana ta dubeta ad'an tsorace tana fad'in“A'a kin mance karan gidan ko?”“ke dallah d'azu naga anfita dashiifa ya mutu”“Allah to muje daman inason shan mango na gidan yafi nanan dad'i”inji Rahma.
suka fice baki d'ayan su, suka nufi bayan gidansu, ashe nan ne gidansu Zee d'in.
suna zuwa suka tura gate d'in Nuratu ce kan gaba, tagama le'kenta babu kowa mai gadi yana band'aki, hakanne yabasu damar shiga gidan, kai tsaye cikin lambun suka shiga, sai ga Nuratu akan bishiyar mangwaro kamaan wata biri, sannan Nana tahau da gyar Hilal da Rahma na kwashewa idan sunjefo, basuyi auneba saijin,haushin kare sukayi, Rahma da Hilal sukai tsuru-tsuru, ganin karen da sukayi yana nufosu ne yasanyasu zubar da mangwaron suka kwasa da gudu, Nuratu ta diro aguje itama, Nana garin saukowa tafad'o kan 'kafarta ta kwala wata uwaar 'kara data janyo hankalin mai gadi zuwa wajen, su Nuratu kuwa tuni sunyi waje aguje.
ko da mai gadi ya'karaso sai ganin Nana yayi akwance karen nata faman zagayata, yana kad'a wutsiyarsa, mai gadi ya kori karan ya tsuguna agabanta ya ta'bata yaji babu ko alamun numfashi a tattare da ita.
[21/11/2017, 13:05] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》🌈🌈🌈Book 1
MALLAKA.......QURRATUL-AYN
05
Mai gadi yatashi arud'e zuwa cikin gidan, da shigarsa kaitsaye falo yashiga, Hajiya Saude mahaifiyar Zee nazaune falon ta amsa masa sallamar, ganin sa da tayi arud'e yasanyata watso masa tambayar “Lafiya kuwa malam Badaru?”“ba lafiyaba dai Hajiya, domin wata yarinya na cikin lambu akwance cikin suma ko mutuwa”mai gadi yabata amsa “subhanallahi...! muje ingaanta, garin ya hakan tafaru?”tafad'a tana mai d'aukan hijabinta dake kusa da ita, tayo waje mai gadi yabiyo bayanta yana fad'in “wallahi bansan ya akai hakan tafaruba Hajiya, kawai ina zaune najiyo ihu, ina zuwa naga kare nazagayata ita kuma babu alamun numfashi atare da ita”ya 'karashe maganar dai-dai sanda suka isa wajen.
Hajiya ta sunnkuya ta d'ago Nana tana mai ta'ba wuyanta, kafin ta dubi mai gadi da fad'in “Nana ce da alamu suma tayi, to me yakawota nan? yi maza malam Badaru, kiramin Naseer ad'akinsa, kace yad'auko mukullin mota”“to Hajiya”.
mintuna kad'an sai gasu sunfito, aka sanya Nana amotar domin kaita asibiti.
Duk kan abinda yafaru akan idonsu Nuratu, suna ganin sunfita da ita, suka nufo gida da gudu suna kuka, suna shiga da Aunty sukayi karo ta tsai dasu tana tambayarsu “ku lafiya dai, mai kuma yafaaru? naganku duka kuna kuka” “Aunty Nana ce, Nanaa ce”cewar Rahma data kasa fad'in abinda yafaru, Aunty cikin kad'uwa tahau fad'in “mai kuma yafaru da Nanan?”hakan yasanya hankalin 'yan gidan baki d'aya dawowa wajensu, Mama takama hannun Nuratu tana tambayarta “mai yasamu Nana? Nuratu”Nuratu cikin kuku takama fad'in “ta mutu Mama, Nana ta mutu”.
Ganin da Mama tayi duk arud'e suke yasa taja hannunsu zuwa falo, kowa binsu yayi amma banda Aunty Amarya da tanajinsu tad'akinta tayi shiru abinta, tana addu'ar Allah yasa gaskiyane ta mutum.
Mama tazauna tana rar-rashinsu, sai da taga sunnutsu, sannan tasake tambayar Nuratu “yanzu Nanan tana ina?”“tana gidan mangwaro, amma sunsakata amota sunfita”“gidan mangwaro mai yakaiku gidan mangwaro kuma?”cewar Aunty, Hilal ne yabada wannan amsar yana fad'in “yaya Nuratuce da Nana sukace muje mutsunko mangwaro”wayar Mama dake gefantace tayi 'karasa, yasa kowa ya mai da hankalinsa kanta, ganin number Hajiya Saude da Mama tayine yasanyata d'aukan wayar da sauri.
“kuna ina yanzu Hajiya”cewar Mama, basuji amsar da aka bayarba sai dai Mama da tace “to shikenan gamunan zuwa”Mama takashe wayar, tana mai sake kiran Number takara wayar akunnanta “hello Nura kana ina? ”“ina kan hanyar zuwa gidan na kusa 'karasowa ma, da wani abune Mama?”“to kayi maza kazo babu lafiya, ankwantar da Nana a asibiti ne”takashe wayar.
falon yad'au shiru kafin Mama tace “wai suna Nana Khadija hospital, anbata gado, karaya tayi a'kafa, amma jikin da sau'ki, inji Hajiya saudan”Aunty tayi ajiyar zuciyar tana fad'in “to Allah 'kara kiyayewa yabata lafiya” dai-dai sanda Ya Nura yayi sallama yashigo “daman kai muke jira Auntyn Nura tashi muje ko”mi'kewa sukayi baki d'ayansu, da yake kowacce da mayafita kai tsaye waje suka nufa.
su Nuratu suka bisu da kallo babu wanda yayi gigin fad'in zai je sabida sunga Ya Nura ne zai kaisu.
。。。 。。。 。。。
“ni wallahi Momy dama zata mutum mufara rage banzaye”cewar Kamal d'a na biyu awajen Aunty Amarya, “ni duk ba wannan ba nafison wannan yarinyar mai kama da 'yayan aljanun ta mace wallahi, aduniya babu wadda natsana irinta”fad'in Habiba kenan, wadda Kamal ke bi mata, Aunty Amarya tayi murmushi tana fad'in“kudai kusha kuruminku, ku kwantar da hankalinku kowanne acikinku sai burinsa ya cika, barinma dai ke Habi na”Habi tayi murmushi “Momy ya kamata dai yanzu kisanarwa da Abba batun aure na da Ya Nura, Allah ji nake idan ban aureshiba mutuwa zanyi”“kai Aunty Habi, soyayyar har takai haka?”Habi tayi dariya tana duban Momyn tasu, kafin Momyn tace “kai ai soko ne, duk wani plant mungama shiryawa, ya kake ganin idan Habi ta auri babban d'an gidan nan, tahaifo jikoki duk maza, kasan cewa arzi'ki namune ”suka tafa tare da Habi, Kamal yari'ke baki “Momy yaushe kukayi wannan tunanin? ammafa abin gaskiya yayi”“ai kaine baka da sirri saura inji zancen wajen Yayanka, kasan cikin satinnan zai dawo”“haba dai Momy ai ko kusa bama zaijiba domin kinsan shi baya cikin jam'iyyarmu, yana jam'iyyar 'yan adawa”suka saka dariya baki d'ayansu, haka suka shafe awanni, su'kulla wannan sukwance wannan, duk zancen babu abin arzi'ki sai na tsiya.