Sashe 13
Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama ce tare da kishiyoyinta, Aunty da Momyn su Haby,sai Ammy tattaunawa suke agame da auren ya Nura da Haby, Nana tayi sallama tashigo zuwa falon, tana d'ingisa 'kafarta, domin yanzu 'kafarta d'aya tad'an nakasa, tun fad'owar da tayi daga saman bishiya, Ammy tad'anyi tsaki data dubi Nana, Mama tace "lafiya kuwa Ammyn Nuratu" Ammy tayi ajiyar zuciya gami da fad'in "a kullum na kalli Nana tausayi take bani wallahi, rashin jin Nuratu baiyiba arayuwa wallahi, haka kawai tajawa yarinya nakasa" Mama murmushi tayi "ki daina fad'in haka Ammy, dama can haka Allah ya'kaddarowa Nana zai faru da ita, ki daina zargin Nuratu akan hakan" Aunty tace "ai daman koba Nuratuba, idan Allah yayi hakan zai faru sai yafaru, dan Allah kidaina saka damuwar Nuratu aranki Ammy" Momy tace "gaskiya kika fad'a Aunty komai ai na Allah" nan kuma suka sauya hiran zuwa shirye shiryen bikin da za'a ga batar nan da sati uku masu zuwa.
komai suna gudanar dashi tare, Momyn Haby bata ware kantaba, ta saki jiki dasu sosai kamar babu komai aranta suma su Mama haka.
"Ango, ango, ango manya" cewar Khamis kenan dake zaune saman kujera yayin da Ya Nura ya kammala waya da gimbiya amaryarsa, ya dawo da dubansa kan Khamis da fad'in "to yaranka?, kai dai kazauna amatsayin tuzurunka, yanzu mune manyanka" Khamis yasanya dariya sosai yana fad'in "to mene a ciki, nudai haryanzu, banga mata taba" ya Nura harara ya watsa masa da fad'in "ai bazaka ta'ba ganin taba, zauna dai sai dai kaji ana kiranmu Abba, kai kuwa sai dai kawu" wannan karon dariya suka saka baki d'ayansu, Khamis yakau da zancen da fad'in "yauwa wai me da me gimbiyar taka tashiryane, haryanzu bata fad'a maka abinda za'a bata ba?" "ehh bata sanarminba tukunna tadaice 'kawayenta zasuzo suyi maganar abinda za'a basu, ita kuma zata sanarmin wanda zatayi anfani dashi, idan tadawo daga school zata fad'i nawa zanbata" Khamis yace "ai gara ayi shirye_shiryen tun da wuri domin rawar kan naku tayi yawa da kai da ita" Ya Nura yajawo pillown kujera ya jefi Khamis da shi yana dariya
su Nuratu ne zaune cikin harabar gidan suna wasa, kusa da d'akin ya Nura, lilo sukeyi abinsu, basajin dukkan abinda akeyi ma, Ya Khaleel ne yazo yazauna a d'aya daga cikin fararen kujerun dake wajen, yana kallon dukkan shirmensu, basu lura da shiba sai can suka kula da mutum awajen, ganin Khaleel ne yasaka suka bar yin lilon, suka nufi inda Khaleel yake zaune suna fad'in "ya Khaleel yaushe kazo kazauna anan?" suka kewayeshi kowa da abunda yake fad'i, yana basu amsa dai-dai da abinda kowannensu ya tambaya, cikin nishad'i, da kaunar yaran da yakeji aransa, domin shi Khaleel ko kusa bai d'au duniya da zafiba, kai kace ba yayan Haby bane, baki d'ayan rayuwarsa ta ban-banta da tasu, halinsa kamar Ammy ce ta haifeshi.
'karar bud'e 'kofar d'akin ya Nura da suka jine yasanyasu juyawa baki d'ayansu, sanye yake da t.shert da jeans masu ratsi tamkar kayan sojoji, sumar kannan nasa kwance kamar wanda yakeyi mata relaxer sai 'kyalli take ba'ka wuluk, sai sajensa daya kewaye doguwar fuskarsa, takalminsa ba'kine sau ciki, a ta'kaice dai Ya Nura ya had'u, dukansu sakar baki sukai suna dubansa, har shi kansa uban gaiyar Khaleel, ya Nura yayi gyaran murya gami da d'a gira yana fad'in "wannan kallonfa?" Khaleel yayi murmushi yana fad'in "kayi kyau ne sosai broda" "nagode" ya Nura yacewa Khaleel, suma su Hilal haka suka hau fad'in "gaskiya kayi kyau Yaya" bai kulasu ba, Nuratu kuwa murgud'a baki tayi, ta bishi da harara, amma mai makon yayi fushi, sai kawai ya girgiza kai yawuce, ya nufi parking space, yashiga motarsa ya tayar, gateman ya bud'e gate yafice abinsa.
Khaleel ya dawo da dubansa kansu Nuratu, yana mai mi'kewa tsaye yake fad'in "kuyi wasanku ko, ni zanshiga ciki ina da wani aikine" bai jira surutunsu na shirmeba yawuce yabarsu.
Nan suka hau wasan guje-guje, Hilal bai saniba ya daki 'kofar d'akin ya Nura ta bud'e, nanfa suka saki baki suna mamakin yanda akai ta'bud'e, basu san cewa mancewa yayiba yana sauri, ai kuwa Nuratu tace su shiga suga abunda yake d'akin, babu musu suka bi bayanta, cikin sand'a suka shiga kamar wasu 'barayi, nanfa suka hau aiki, subud'e nan su rufe nan har cikin bedroom nasa, Nuratu da Rahma toilet suka nufa ta kunna shower wai wanka zasuyi, Nana da Hilal a d'akin suka zauna sunayimasa ta'be ta'be son ranau, sunma mance a cikin d'akin wanda suke.
'karar hon d'in da sukajiyone, da kuma bud'e gate yasanyasu fitowa a guje, suka nufi cikin gida, sai kuma sukaga ba shi bane Hamza ne mijin Aunty Hafsa, hakan yasaka suka mance da batun zuwansu d'akin ya Nura.
suka hau tsallen murnar zuwansa, nanfa suka kafe sudai yatafi dasu wajen auntyn su, kan dole Mama tabasu 1set na kayansu, cike da murna suka ruga zuwa gate, suka shige cikin mota, sai da yagama abinda yake, kafin yafito su tafi.
suna son zuwa gidan Aunty Hafsat ne, domin gidanta babu takura, daga ita har mijinta babu mai takura musu, sunayin abinda sukeso da wanda suka ga dama, domin Aunty Hafsa babu ruwanta kan hantarar yaro da takura masa, hakama mijin nata.
suna tafe a mota suna hiransu, yana biye masu, har suka isa gidan su dake 'Dorayi, yana parking motarsa suka fito da gudu zuwa cikin gidan, lokacin Aunty Hafsa na kitchen tana shiryawa mijinta abinci, sai jitayi kawai an rungume 'kafafuwanta ana ihun kiran sunanta, da sauri ta juto ta sunya zuwa garesu tana fad'in "a'a iyalan Mama, saukar yaushe, waye yakawomin ku zuwan bazata?" sai kuma taga mijinta tsaye bakin 'kofa yana murmushi, itama murmushin tayi tana fad'in "sannu da zuwa amma gaskiya ka shammacenifa, wannan bazata haka" murmushi yayi, kawai ya juya zuwa falo, ita falon ta nufa tare dasu Nuratu, suka zube gaban tv suka hau aikin game, ita kuwa Aunty Hafsa d'akin mijinta ta nufa domin yimasa sannu.
ya Nura kuwa bashi yadawoba sai bayan sallar isha'i, yadawo agajiye, ya sanya key domin bud'e d'akin yajishi a bud'e, ya cika da mamaki, yana tunanin ya akai hakan tafaru, sai kuma ya tuna mancewa yayi, yana sauri.
yana shiga falon ya gunna globe haske ya gauraye falon, yafad'a saman kujera abinsa sabida gajiya, 'karar ruwan daya jiyone yasanyaahi mi'kewa da sauri ya nufi bedroom d'insa, yana sanya 'kafa yaji laima a 'kafarsa, har ruwa nad'an bullowa daga cikin capet d'in, da gudu ya 'karasa toilet d'in ganin shower da famfo yayi nata zuba, toilet d'in ya cika da ruwa, yanata mala lowa zuwa cikin d'akin, da kudu yaje ya kashe ya dawo falo yana tunanin yanda hakan ta faru, yasan dai shi yamance 'kofa a bud'e amma komai na amfani a d'akin akashe yake, nan tunaninsa yabashi may be aikin su Nuratu ne, da sauri yami'ke ya fito zuwa cikin gidan 'kafarsa ko takalmi babu yana kwalawa mama kira
[30/12/2017, 20:47] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book 1
mallaka------QURRATUL-AYN
17
Ko da yashiga falo Mama batanan, hakan yasanyashi nufar d'akin Aunty, da sallamarsa ya shiga tana zaune da waya a hannunta, da dukkan alamu waya ta kammala.
Ya Nura ya dubeta da fad'in "wai ina Mama tashigane?" "tana d'akin Abbanku" Aunty ta bashi amsa, Ya Nura yaja wani d'an guntun tsaki, Aunty tace "wai lafiya kuwa Nura" Ya Nura yakalli Aunty kafin yamai da kallonsa zuwa wani wajen yana fad'in "to mema zance Aunty, dawowata kenan na tadda bedroom zuwa toilet cike da ruwa" "subhanallah, garin yaya?" "wallahi bansaniba, abinda nasani kawai da zanfita ina sauri namance 'kofa a bud'e, ban rufeba kuma su Nana nabari awajen suna wasa" Aunty tad'anyi shiru, kafin tace "kana ganin anya ba yarane suka shigaba, nasan fitinarsu yawa gareta" "ai sud'innema Aunty domin famfo da shower duka kunne nagansu, wai ma ina suke Aunty?" "ai basanan sunje gidan Hafsatu, amma nima zan iya cewa sud'inne domin nagansu sunshigo aguje kuma Rahma da Nuratu jikinsu aji'ke da ruwa" Ya Nura ya gyad'a kawai tare da fad'in "zasu dawo su sameni ai" yayiwa Aunty sallama ya koma d'akinsa, a falo yakwanta har barci yad'aukeshi, yana tunanin abinda zaiyi masu yawuce.
Su Nuratu kuwa ana gidan Aunty anayin abinda aka saba, da gari ya waye tun da asuba sukahau rige-rigen girka indomie, Aunty hafsa bata hanasuba, ta kunna masu risho ma suyi akai, ita kuma ta kunna gas, domin shirya masu breakfast.
haka kowannensu yakwa'ba indomiensa yahau ci, wai dad'i, alhalin ko a ido bata da kyan gani, Aunty Hafsat da mijinta kuwa dariya suka dinga yi nasu, dominsu kwa'bar yaran burgesu take, ko dan basy da yarane haryanzu?.
Ya Nura kuwa gari na wayewa yasanya akayo waje da kayan baki d'ayansu, akai masa moping d'in d'akin, Mama da taga yanda d'akin ya cika da ruwa, al'amarin ya bata mamaki sosai da salon fitina irin tasu Nuratu.
sai bayan sallar maghriba Hamza yadawo dasu gida, bot d'in motar cike taf da tsarabarsu daya biya mall yayi masu, da gudu sukayi cikin gidan, tsarabar ma Hamzane da shida mai gadi suka biyosu dasu, lokacin kowa yana zaune falo, har su Ya Nura da su Khaleel, Haby da Kamal ne kawai basanan, kan cinyar Mama suka fad'a cike da murna.
lokacin Hamza yashigo da sallamarsa, suka amsa masa,ya gaishe da surukansa, yana bawa Ya Nura da khaleel hannu, and'an ta'ba hira dashi kafin yayi musu sallama yatafi, yana mai fad'in "ya'yan Mama ga tsarabar kunan, sai yaushe kuma?" Nuratu tayi saurin fad'in "sai ankwan biyu, idan Mama tabarmu" Ya Nura yad'an bugeta da 'kafa, yanda babu wanda ya lura, Nuratu takalleshi tare da d'an murgyd'a masa baki, shi kuwa d'aure fuska yayi tamau, Hamza yace "to Nuratu Allah kawoku" yafice, ya Nura yataka masa baya.