Sashe 4
Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Su Mama na isa hospital d'in waya ta bugawa Hajiiya saude tazo ta tafi dasu d'akin da aka kwantar da Nana, cikin mintuna kad'an sai gata, tayi musu iso zuwa d'akin, har lokacin Nana bata farkaba, tana kwance 'kafarta ta hagu d'aure da bandeji, da alamu anan karayar take,Mama tace “mungode Hajiya, tunda munzo yakamata kuje gida ku huta”“ehh yanzu nake cewa idan kunzo zanje gida daman, nafito babu wanda yasani, anjima zandawo ai”tayi musu sallama, Mama tasake godiya kafin tafice tatafi.
Ya Nura yahau tambayar mai yafaru da ita “Mama tasanar masa iya kacin abinda tasani”“Abba yasani kuwa?”cewar Ya Nura “A'a sai dai yanzu kasanar masa, shaf namance wallahi”Mama tafad'a, “ok ba damuwa bari inyi masa waya ”yafad'a yana fita.
wunin ranar su Nuratu sukuku sukayishi, sai yamma Nuratu ta nufi gida wajen Ammyn ta jiki duk babu kwari, tana shiga falon tafad'a kan kujera takwanta, Ammy,dake zaune 'kasan kafet tana cin abinci ta dube ta, tasan babu lafiya Nuratu tashigo waje takwanta kawai, batayi abin maganaba “ya dai 'yar gidan Mama, lafiya kuwa, mai yafaru?”
“Ammy Nana ce aka kwantar a asibiti wai takarye”Ammy tabarcin abincin tana dubanta tare da fad'in “ta karye kaman ya?”“ehh fad'owa tayi daga kan bishiyar gidan mangwaro, yanzuma tana asibiti har da su Mama”“subhanallahi....!wanne asibitin suke?”“wai Nana Khadija hospital”Ammy tami'ke tana fad'in “banga tazama ba, bari inbi bayansu”“kai Ammy na, kema tafiya zakiyi, su Mamafa da Aunty nacan, duk saiku tafi kubar mu, dan Allah Ammy kizauna”“kinci gidanku inzauna inyi miki mai kuma? mara lafiya nacan kwance sai inzauna tare dake, inzauna inyi miki uban me? ke da kike ficewa kibarni fin sati guda baki le'koba ban damuba, sai ni kice bazan fitaba”Nuratu tashare kwallar idonta, bata sake maganaba, har Ammy tagama shirinta, da yake tasan asibitin sosai nan ake kwantar dasu duka idan basu da lafiya, sai da tafito sannan ta dubi Nuratu dake kwance falo, ta duba taga har tayi barci Ammy dariya tayi da fad'in “yaro yarone, ana mitar bazan fitaba gashi ita kuma baccima tayi abinta”
Ammy tagyara mata kwanciyar tafice tabarta, kai tsaye bakin titi ta nufa ta tsai da kekenapep tahau suka tafi.
[22/11/2017, 01:08] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈QIYAYYA SA GANIN LAIFI🌈🌈🌈Book
1
MALLAKA......QURRATUL-AYN
06
{Da yawa mutane na tambayata wai WACECE NURATU?, abasu tarihinta, sannan yaya ala'kar GIDAJE GUDA BIYU take?, to kuyi ha'kuri dukkan amsarku nanan tafe, kudai kubi QURRATUL-AYN asannu zata war-ware maku ZARE DA ABAWA ina godiya sosai masoyana harma da maqiyana ngd sosai 😘}
*** *** ***
kusan tare Ammy da Abba suka shiga asibitin, bayan sun gaisa Abba ya kira ya Nura yayi musu iso zuwa d'akin da Nana ke kwance, lokacin jiki alhamdulillah, tafarka daga baccin har taci abinci,tana zaune abinta.
Gaisawa suka hauyi, kafin Ammy ta tambayi yanda abin yakasance, Aunty ce ta bata labari kamar yanda Nuratu tafad'a.
Ran Ammy ya'baci sosai tace “haba biri yayi kama da mutu, tunda Nuratu tashiga gida jiki amace da yanda ta bani labari nasan idan anbibiya itace UMMUL-ABA'ISIN faruwar abin ”“A'a kada kice haka Ammyn Nuratu, wannan abin 'kaddarace ko da Nuratu ko babu idan Allah ya'kaddara sai yafaru, amma dan Allah kidaina wannan maganar”cewar Abba kenan yayin da yake niyar fita, yacigaba da fad'in “ni zanje gida nad'anyi wanka ina dawowa, inyaso zuwa bayan sallar isha'i zan mayar daku gida Nura yakwana, da safe kwa dawo”“to Allah kiyaye sai kadawo”suka fad'a baki d'ayansu, ya bud'e 'kofar yafita, Ya Nura yabi bayansa.
“”“”“” “”“”“” “”“”“”
sati guda Nana tayi a asibitin, ranar alhamis likita yasallamosu, a motar
Ya Nura da Aunty Hafsa dake aure a sharad'a phase 1, itama ranar taje tare suka nufo gida, Aunty Hafsa ce tari'ko Nana dake dogarawa da sanda zuwa babban falo, sannan su Momy nazaune falon tare da iyalanta, wani mugun kallo tawatsawa Aunty Hafsa kafin tami'ke zata fice, Haby tasaki wani mugun tsaki tabangaji kafad'an Aunty Hafsa tafice, Aunty Hafsa tayi murmushi tana fad'in “ai daman ance tsintacciyar mage bata mage, kuma d'an kauye idan ya kile yafi d'an iskan binni iya iskanci”
A fusace Haby ta juyo cikin masifa tana fad'in “ehh munji amma ahakan d'an 'kauyen yazo yafi d'an birnin ko mai ta'kama mulki, arzi'ki”“ke rufemin baki, ni ba dake zanyiba kinsan nawuce ajin yi dake sai dai da mahaifiyarku”cewar Aunty dake shirin zaunar da Nana, cikin,'bacin rai Haby tad'aga hannu zata mari Aunty Hafsa, Momy tari'ke hannunta tana fad'in “barta zata san ta zageni, ni bazanyi da itaba sai dai da ubanta, shine dai-dai dani”
Tafad'a dai-dai sanda su Mama suka kawo kai, Aunty Hafsa kuwa tana tsaye tana jiran ta mareta taga yanda zatayi da ita, Aunty Hafsa tayi tsaki tana fad'in“ wannan ke yadama kuma, amma idan banda butulci da cin amana, daga zuwa cin arzi'ki, kuma ba iya cin arzi'kin ba sai da aka had'a da cin amana, aikin banza aikin wufi”“ki rufe bakinki Hafsa bana son kalan fad'a”fad'in Mama kenan, yayin da take 'ko 'karin zama kan kujera.
Momy takama hannun Haby suka fice fuuu Kamal yatake masu baya, Aunty natsaye tana dubansu, batace komaiba, suna fita Ya Nura yashigo da kayan da sukazo dashi ya ajiye afalon ya nufi d'akinsa.
“Da kinbarni Mama na koya masu hankali wallahi, wa 'yannan zuma ne Mama sai da wuta ha'kuri bazaiyi amfani akansu”Aunty tace “wallahi kuwa, ni kaina badon ina tsoron igiyar aure naba da tuni anyi wacce za'ayi”“uhmmm,bazaku gane bane, duk abinda kwanciyar hankali bai bayarba, rashin sa bazai bayarba, rigima bata da dad'i ko kad'an, ha'kuri da addu'a shine yadace akan wad'annan”cewar Mama, Aunty Hafsa tayi ajiyar zuciya kawai, tayi saurin kawo wata hiran, dan ita idan Mama nafad'in suyi ha'kuri ranta idan yayi dubu 'kara 'baci yake.
ko da Abba yadawo Momy da kukanta take sanar masa wai Hafsa tayi mata rashin kunya, ai kuwa fad'a ranar Aunty Hafsa tasha shi, har sai da tayi data sanin zuwa gidan ranar, ha'kuri kawai,tayi ta aikin bawa Abba dan da cewa yayi ta tattara ta tafi tun alokaacin da'kyar ya ha'kura tajira mijin nata yazo
sai dare sannan mijin Aunty Hafsa yazo yad'auketa suka tafi.
Da dare Ammy zata fita 'kara dubo Nana, yayin da Nuratu kezaune kan kafet tana Assingment, ta baje littafai gabanta, Ammy ta dubeta “ni zanje dubo Nana, saura kisa 'kafa kifita daga gidan nan, dan naga tun yamma rawar kan naki tadawo”tafice tabar Nuratu
Nuratu tayi murmushi tacigaba da aikinta, aranta tarasa dalilin da yasa Ammy tad'aure mata fuska yanzu, tun ranar da tadawo daaga asibiti aranar da abin yafaru, baki d'aya Ammy tabar sake mata fusks, ita kanta Nuratu batajin dad'in gidan yanzu, shiyasa take Allah-Allah asallamo su Mama daga asibitin, ai kuwa yau da yamma da Aunty Hafsa tashigo gai da Ammynta take sanarwa Ammy ansallamosu, Nuratu naji ta cika da farinciki, domin ita gani takeyi Ammy na matse mata lamba, tana takurata sosai acan tafi sakewa,tayi dukkan abinda take so.
《》《》《》 《》《》《》 《》《》《》
“uhmmm Alhaji ni kuwa da ina son shawartarka akan,wani al'amari, sai dai bansan yandaa zaka d'au maganarba”Abba dake shingid'e kan kusun yana karatun jarida, ya ajiye yana mai duban Momyn Kamal “fad'i dukkan abinda zaki fad'a nasan alkhairi ne, domin baki bani gur'batacciyar shawara, dan haka kada kiyi shakkar sanarmin komai da bani shawara, zanyi 'ko 'karin ganin nayiwa maganarki kyakykyawar fahimta, ina jinki” Momy tad'anyi murmushi mai sauti na ri'kak'kun 'yan duniya, kafin tace “dama kan batun Nura ne, tunda ya kammala komai yanzu aiki yake, kuma ba'ananba gida ba, yakamata ace ya ajiye iyali ko?”tad'anyi shiru tana duban Abba, tana so tafiskanci idan maganar zatayi tasiri awajensa, Abba yayi murmushi “kinyi kyakykyawan tunani gaskiya, nima sati guda kenan dayi masa magna kan batun aure, to amma ya nunamin bashi da wata wadda yake so yanzu, da alamu ma baya ra'ayin aure yanzu”“haba Alhaji na, ya za'ayi abarshi haka yakamata dai kanema masa, ya za'ayi mubarshi haka kasan yanda rayuwarnan tacanjafa, mai aurenma ya ya'kare bare kuma mara auran”“kinyi gaskiya kam, to nidai ayanzu bani da wacce zan nema maasa, amma idan kin hango wacce ta dace dashi sanarmin”.
Momy tayi murmushi tana wasa da zoben hannunta “to Alhaji mai zai hana kahad'asu da Habiba”“wacce Habiba kuma?”cewar Abba “Habiba ta wajena mana”“ohh Allah sarki amma kuwa Rabi Allah yamiki albarka, naji dad'in wannan hangen naki da ni yamata inyishi gaskiya nagode sosai”Momy tayi masa wani shu'umin murmushi, aranta tana fad'in “ta 'kare maka Alhaji, da kasan abinda wannan had'in yataka da bakayi saurin amince
wa ba”afili kuwa 'yar dariya tayi tana fad'in “haba dai Alhaji kada kadamu babu komai wallahi, Allah tabbatar da alkhairi dai”“amin”cewar Abba daya cika da farinciki kamar ance nasa ga aljannah shiga.
[22/11/2017, 19:54] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》🌈🌈🌈Book 1
MALLAKA......QURRATUL-AYN
07
(Godiya ta musamman a gareki ZEEE-YABOUR, Allah ubangiji yabar 'kauna ya'kara basira da za'kin hannu Amin, Inayinki sosai tawan MISS XOXO, bazan mance dakeba HAFSAT RANO, ZAHRA BUKAR kina raina wallahi Allah ya'kara lafiya yasa kaffara amin ACTION BABY Parrot na gaisheki kyauta😘 )
。。。 。。。 。。。
Safiyar ranar wata alhamis, Ya Nura ne gaban Mama yaje gaisheta da ita“Mama daman shawara nake nema, ko na koma d'akin dake harabar gidannan, na kusa da gaiden ne, inyaso idan Khaleel yadawo sai yazauna nan d'akina, tun da ya kusa dawowa ”ya Nura yafad'a yana mai wasa da mukullayen hannunsa, “ehh gaskiya kam, hakanma yayi, tunda daman idan bakanan inyadawo hutu d'akinka yake sauka, yanzu kuwa yadawo gaba d'aya bazai yiyu kuna d'aki d'ayaba hakan zai zamo takura, yanzu yaushe za'a gyara maka, sannan kasanarwa Abbanku ko?? ”Ya Nura ya sosa 'keyarsa “yasani Mama dashi muka fara magana, zuwa anjima masu gyaran d'akin zasuzo, daman amincewarki nake jira kawai”“babu damuwa Allah taimaka”“amin”
yana fita Aunty tashigo domin gaisawa da Mama, nan Mama take sanarwa Aunty batun komawar d'an gidan nata d'akin waje, Aunty tayi murmushi tana fad'in “ya sanarmin d'azu, shine nace yazo yaji ta bakinki”“au ashema kinsani?, ko dayake namanta kunfi kusa da Nura, ni ina gefe 'yar kallo”suka sa dariya baki d'ayansu, nan sukayita hiransu abinsu, kishiyoyi biyu masu abin sha'awa kenan.