Sashe 15
Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kashe garima dinner aka sakeyi a hamdala hotel, sai kuma party biyu da aka gudanar a nigh-tell, sanna aka gunar da walima iya mata kawai cikin harabar gidansu, ranar asabar aka gudanar da yinin biki, Amarya tayi kyau sosai ranar, sai shiga takeyi ta alfarma tana cirewa, haka sauran dangi ba'abar su abayaba, ranar lahadi kuma take ranar d'aurin aure, za'a d'aura 'karfe goma na safe ne.
-----RANAR 'DAURIN AURE----
Nuratuce zaune gaban Ammynta tana sanar mata abinda za'a bata ita da su Nana zasuyi nasu parting, Ammy ta dubeta kawai tayi murmushi tare da dafata tana fad'in "haba 'yar gidan Mama, wanne party kuma zakuyi" duk partyn da akasha bai ishekuba, kinsan nifa bana son harkan fitina" Nuratu tad'an turo baki gaba, tana d'an bubbuga 'kafafunta a'kasa tsabar shagwa'ba, Ammy tace "to tunda ke bakisan harkan lallashiba, tashi kificemin ad'aki" ba musu Nuratu tafito a d'akin tana murzar idanuwa, mutanan falon namata magana ko kulasu batayiba ta fice daga gidan, ta nufi wajen Mama, a harabar gidan ta taddasu Nana, suka bita zuwa cikin gidan.
a hanyar shiga gidan tana tafiya da baya da baya tana fad'awa su Nana abinda zasu gayawa Mama domin ta amince ta basu kayan parting, sai ji tayi tayi karo da mutun, cikin zafin nama taji anfizgi gashin kanta tayi baya ta daki bangon wajen da goshinta, kafin ta dawo haiyacinta aka d'auketa da mari, cikin firgici da gigita ga kuma azabar buguwa batasan sanda tahau fad'in "Allah ya isana mugu azzalimi" duk da cewar idanunta basu washe taga ko wayeba, dai-dai sanda yasake kai hannu zai 'karamata wani marin, taji ana fad'in "kai Kamal lafiyarka kuwa, mai tayi maka haka?" Nuratu tad'ago kanta da sauri, sai taga ya Nura ri'ke da hannun Kamal, ashe da Kamal sukai karon.
shine yayi mata wannan mugun bugun, da kyar ta dafa bangon tami'ke, tana binsu da kallo, bakinta na jini, goshintama haka, Ya Nura yasake tambayar Kamal cikin tsawa "nace mai tayi maka?" Kamal da idanuwansa suka kad'a sukai ja, wanda da dukkan alamu abuge yake ya fizge hannunsa daga ri'kon da Ya Nura yayi masa yana fad'in "waini zata buge wannan yarinyar, sannan inhukuntata tazageni" cikin layi yake maganar, Ya Nura ya dubi Nuratu yaga jini duk ya'bata gaban rigarta, ya kamo hannunta suka fito zuwa harabar gidan, bai kuma bi takan Kamal ba, d'akinsa ya bud'e yaja hannunta zuwa ciki, Nuratu kuwa cikinta yagama d'urar ruwa ta sada'kar yau Ya Nura ko bai kashetaba sai ya illatata.
suna shiga har bedroom nasa ya nufa da ita, yaje yad'auko wata 'yar akwati 'karama suka dawo falon, ya zauna akan kujera, yajawo hannunta zai zaunar da ita tafara kuka ta zube agabansa tana magiyar "dan Allah Yaya kayi hakuri, wallahi nadaina rashin kunya da 'kinji, kabarni dan Allah inrayu tare da Ammy dasu Mama" maganganunta sunso bashi dariya sosai, amma sai ya kanne yasake zaro idanuwa yana fad'in "ni bakison kirayu dani ko?, to matsonan" Nuratu tasake ja dabaya tana fad'in "har dakai wallahi inaso inrayu da kai, kayi ha'kuri dan Allah" Ya Nura sai da yayi murmushi, yami'ke yajawo hannunta, yazaunar da ita, bisa kujerar da yake zaune kusa da shi, yasa hannu yashare mata hawayen, yana fad'in "kukan ya isa to" sannan yabud'e akwatin sai taga ashe first aid ce, tasaki wata ajiyar zuciyar da sai da Ya Nura ya dubeta kawai, nan yasanya hydrogien yana goge mata ciwon, ai kuwa tahau ihun zafi, ganin yad'aure fuska yasanyata yin,shiru ammafa har 'kan'kameshi take, duk tabi ta'bata masa jiki, sai da yagama sannan ta lura da 'bata masa rigar da tayi cikin tsoro tahau fad'in "kada kadukeni yaya kawo rigar inwanke maka" Ya Nura yayi dariya yana fad'in "ko ke bakya wanke naki kayan, bare kuma nawa" dai-dai sanda aka turo 'kofar d'akin akashigo, Khamis ne tare da wasu abokansa su biyu, dukkansu cikin bluen shadda da hula d'inkin zamani sunyi kyau sosai .
Khamis ya tsaya daga bakin 'kofar yana fad'in "haba master, kana duba agogo kuwa? daga bari kaje kayi wanka kashirya sai kabarmu tsaye"
Ya Nura bai maganaba illa duba agogo da yayi yaga tara da rabi har da mintuna biyar, hakan yasanyashi mi'kewa yanufi bedroom nasa, Khamis yabishi da kallo, sauran abokan kuwa guri suka samu suka zauna, sannan Khamis ya'karaso zuwa kujerar da Nuratu ke zaune, ya zauna yana fad'in "Nuratun Abba, Mama, Ammy, ko Nuratun Nura zance?" Nuratu ta dubeshi cikin harara ta d'an murgud'a baki, kafin tad'an rage murya tana fad'in "kace dai Nurantun Abba da Mama da Ammy kawai, amma babu wata Nuratun Yaya, mugune infad'a maka" baki d'aya su Khamis dariya suka sanya, har ita uwar gaiyar, Khamis yace "wai lafiya kuwa mai yasameki ne?" Nuratu tad'an ta'be baki, tana fad'in "wani mugunne kuma yaso illatamin fuska ana cikin bikin murna" "wayeshi kuma?" "Kamal mana" Nuratu tabasu ansa, tacigaba da basu labarin abinda yafaru, har chakwakiyarta da Ya Nura bayan yajawota d'akin, su Khamis nata dariya.
'karar bud'e 'kofar d'akinsane yasanya Nuratu yin shiru daga labarin datake bawasu Khamis, yana fitowa wani 'kamshi ya kewaye d'akin, sanye yake cikin farar shadda da malun-malun, tasha aiki blue, takalminsa blue ne, sai hular kansa itama fara mai aikin blue, yasanya farin glass afuskarsa, daya 'kara fiddo da kyawunsa, Nuratu tasaki baki tana dubansa, karo na farko a rayuwarta data ta'ba ganinsa da glass, tsawar daya daka mata itace tayi sanadiyyar d'auke kanta tana murgud'a baki, Ya Nura yace "to parrot tashi kifice, duk inajinku ai, ku kuma da girmanku kunwani biye mata" sum-sum Nuratu tatashi tafice tana 'ku'kuni.
Khamis yace "ai dole mubiye mata Nuratu akwai burgewa" Ya Nura yaja wani mugun tsaki yana fad'in "sai ku tashi mufita ai, saura five minute" ba musu sukayo harabar gidan.
Nuratu kuwa nashiga gidan kowa Nuratu, anayi mata sannu, hakan yasanyata dawowa da kukan da bata samu tayiba, Maman jigawace taja hannunta takaita d'akin da Inna take takwantar da ita, tana ta ta'bara da shagwa'ba Inna na lallashinta.
10:00
aka d'aura auren ya Nura da Habiba akan sadaki dubu hamsim, wanda Abba ne yabayar dasu, nan waje yakaure da kad'e-kad'e da bushe-bushe, jama'a kuwa bila adadin gasunan, sun cika 'kofar gidan fam, babu masakar tsinke domin Abba mai mutane hakama ya Nuran kansa
[04/01, 00:09] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book 1
mallaka-----QURRATUL-AYN
20
Haby nacan cikin d'akin Momynsu anayi mata d'auri, tasha make-up tayi kyau sosai tamkar ba itaba, su Zuly ne cike ad'akin tare da wasu 'kawayensu su biyar, shewa suka sanya baki d'ayansu suna zolayar amarya jin maro'ka nata kirarin an d'aura auren.
Mamace tashiga d'akin Inna neman Nuratu domin tuni su Nana suka kaimata zancen abinda yafaru da ita, ai kuwa Nuratu naganinta ta taso ta rungumeta cike da shagwa'ba, Mama tace "subhannallahi, haka yayi maki da fuska?, ai kuwa sai na sa'ba masa wallahi"
taja hannunta suka fito zuwa part d'inta, toilet ta kaita tayi wanka ita kuma takoma wajen ba'kinta, koda Nuratu tafito su Nana tagani zaune kan gado cikin bluen shadda anyi mata stone work, sunyi kyau sosai, da murmushi Nana tami'ka mata tata shaddar suka fice da sauri, jin anfara d'aukar hotuna, Nuratu agurguje ta shafa mai, tasanya powder da jan baki pink, tad'an gyara giranta, ta taje gashin kanta dake zuba har gadon bayanta, ta sanya under wear, ta zura doguwar rigar shaddarta, ta sanya ribom d'aya takama gashinta, sannan tasake d'aurewa da d'ankwalin shima tayishi kamar ribom, tayi kyau sosai duk da cewa bawani make-up tayi ba(kada kumance Nuratu ruwa biyu ce bafulatana kuma balarabiya).
takalminta ma flat tasanya pink, bata tsaya wani duba mayafiba tayo waje, duk da ciwon dake goshinta hakan baihana baiyanar kawuntaba, ai kuwa,nan akahau jan ta kowa Nuratu tazo suyi hoto, domin Nuratu irin yaran nanne masu shiga rai.
Ango nashigowa aikuwa abokan wasansa suka fara zolayarsa, kasancewar Nura bamai magana bane murmushi kawai yake binsu dashi, Khamis ne da sauran abokai suka sayi bakinsa suke rama masa, lokacin Amarya itama aka fito da ita cikin tata shaddar pink da aikin blue akai mata, ata'kaice dai angon blue da pink akai ranar, nanfa hotuna da videos yakoma kansu, akaita hotuna kamar baza'a dainaba.
kafin angwaye sufice zuwa d'akin ango, nan aka shirya musu abinci mai rai da lafiya sukaci suka gimtse.
kafin zuwa maghriba kuma aka fara shirye-shiryen kai amarya gidanta dake sharad'a phase II, wanda Abba ne yabaiwa Ya Nura shi kyauta, nan zasu tare kafin zuwan tafiyarsu malesia, Ya Nura yasa angyare masa gidan sosai, tamkar a turai, domin damacan Ya Nura d'an son hutune da gayu, kuma gashi yaje yayi rayuwa cikin turawa.
Su Nuratu sunkafe akan sai sunje har da kukansu, Mama kuwa tace ba'kine zasuje su 'yan gida suyi ha'kuri zuwa kashe gari zasuje, nan su Nuratu suka 'karashi kukansu sukai barcin dole dana gajiya, domin sungaji sosai ai.
motoci reras akazo d'aukar amarya, Momynta tayi mata nasiha sosai kamar gaske, hakama Abba da Mama, Innama ba'abarta abayaba, lokacin angama shirya jama'a acikin mota, sannan aka fito da amarya tana kuka kai kace gaskene sai ha'kuri ake bata, aka sanyata amota daga ita sai 'kawayenta kafin su d'au hanya zuwa kaita kuma, kowa yayaba da tsarin gidan da kyawunsa komai abin birgewa ne a gidan.
10:30
goma da rabi dai-dai angwaye sukai sallama cikin falon, lokacin gidan anwatse kaf, sai amarya da 'kawayenta, sunata shewa da zance narashin mutunci, sallamar angwaye ce takatsesu, amarya tayi maza tarufe kanta, suka 'karaso zuwa cikin d'akin.
nan suka bufe wajen da addu'a sukayiwa amarya nasiha da angonta, tare da d'anyin barkonci, sannan suka aje ledojin da sukazo dasu, sukayi musu sallama suka fito tare da 'kawayen nata dan mai dasu gida.