← Book details Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 23

Sashe 16

Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya Nura har bakin motocinsu yarakasu sannan yadawo yarufe ko ina, ya koma cikin d'akin daya bar Haby, koda yakoma harta zanye mayafin kanta tayi kwanciyarta, da sallama yashiga d'akin amma ko kulashi batayiba, ya d'an jima yana kallonta fuskarsa cike da murmushi, amma kuma yanajin wani irin fad'uwar gaba azuciyarsa, sai ya d'auki hakan amatsayin kawai dan yaune karo na farko arayuwarsa da zaiyi kwana d'aki guda da macene.
'karasowa yayi haryanzu bakin gadon, yazauna agefanta yad'an juyo da ita, tabud'e idanu ahankali tana dubansa, Ya Nura yayi ajiyar zuwa had'e da murmushi kafin ya furta "gajiya ko amaryata?" gyad'a kai tayi tad'anyi masa murmushi, hannunta yakamo yasanyashi cikin nata yana d'an murzawa ahankali, duk da Haby maza sunsaba ri'ke hannunta, amma sai taji wannan ri'kon daban, taji wani yarr ajikinta, wanda yasanyata dubansa ahankali, ya Nura yasa hannu yatasheta zaune yana fad'in "tashi yau ba ranar barci bace, kitashi mugodewa Allah" Haby tad'anso yin gardama, amma sai tayi tunanin kada tabayar da kanta awajensa tun ranar farko, hakan yasanyata mi'kewa zuwa toilet tayo alwala tafito, sannan Ya Nura yashiga mintuna kad'an shima yafito d'aure da alwala.

ya shimfid'a musu sallaya, tasanya mayafinta ita kuma, sannan yaja musu limancin sallah raka'a biyu domin nuna godiyarsu ga Allah, yakama kanta yayi mata addu'o'i kamar yanda addini yakoyar, sannan yami'ke yafita mintuna kad'an yadawo d'auke da flat da spoon sai cup, ya ajiye agabanta, sannan yad'auko ledojin da sukazo dasu yabud'e, ya fiddo da wasu kaji biyu gashashsu, ya zuba madarar holandia a cup d'in, yace mata "bismillah matso" ba musu tad'an matso gareshi, yafara bata naman abaki, yana bata madarar sai daya tabbatar ta'koshi, sannan yaci nasa yatashi yamai da kayan kitchen, ya wanke sannan ya dawo.

wardrobe ya nufa ya fiddo da jallabiya fara 'kal ya ajiye gefan gadon, sannan ya kuma aje wata daban kalar ja, ya mi'kawa Haby da fad'in "ungo kirage kayan jikinki sabida zafi kisanya wannan" yami'ka mata takar'ba, shi kuma ya nufi toilet.

yana shiga tami'ke taware rigar duka-duka bazata wuce gwiwartaba, shara-shara ce, sai wasu siraran igiyoyi a wuyan rigar, rigar tayi kyau sosai sai 'kamshi take gata mai taushi, bata jira komaiba tasanya, ta tsaya a gaban mirrow tana duban kanta domin gaskiya tayi mata kyau sosai.
can shima yafito jikinsa ji'ke da ruwa da dukkan alamu wanka yayi, kallon Haby yatsayayi yana kallon irin kyawun datayi, ya tako zuwa gareta ya rungumota tabaya, yasanya kansa bisa kafad'arta yana rad'a mata wasu irin kalamai, dabanji mai yake cewa ita kuwa murmushi kawai take.
can yasaketa yahau shafa mai ajikinsa, yafeshe jikinsa da turaruka, lokacin takoma gedan gado ta zauna tana dubansa kawai, harya sanya jallabiyarsa sai kuma yacire yasanya 3quarter da best, yazo ya hure mata idanuwa yana fad'in "wannan kallonfa, kamar ance maki za'a saceni, yau ai ranarkice kece da Nura" Haby tayi dariya, Ya Nura yajanyota tafad'o zuwa jikinsa, suka saki wani sassanyan nunfashi atare, tare da 'kurawa junansu idanuwa nanfa Ya Nura yaji yakasa d'aure kallon, yakai bakinsa bisa nata yafara kiss tamkar yasamu sweet mai dad'i daya dad'e bai shaba kafin kace mai labari yacanja, sai ganin duhu nayi yamamaye d'akin XXX, hakan yasani yin waje.

ASUBA TA GARI NUR-HABY
[04/01, 18:57] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book1

mallaka-----QURRATUL-AYN

21

Bugun 'kofar da akene yayi sanadiyyar farkawarsu daga nannauyan barcin da suke, Ya Nura ya duba agogon dake manne bisa bangon d'akin, yaga 11am harda mintuna, salati yayi yana mai saukowa daga bisa gadon, sanye da farar jallabiya ajikinsa, domin tunda yayi sallar asuba yakoma bai farkaba sai yanzu, itace dai uwar garin ko sallar ma batayiba, daman kuma bata dametaba, anata ganin yin sallama takurawa kaine kawai.
yana fitowa Haby tabiyo bayansa, ko zani bata nemaba bare kuma hijab, hakanan tafito sanye da guntuwar rigar barcinta, Ya Nura yace "waye?anazuwa" yaji ance "hafsat ce" hakan yasanyashi bud'ewa da sauri fuskarsa cike da murmushi, yana bud'ewa su Nuratu suka danna kai ciki, suna rige-rigen shiga, Aunty Hafsa tasanyo kai hannunta d'auke da basket na kulolin abinci, ya Nura yakar'ba yawuce daining dasu, su Nuratu nashiga falon sukaga Haby tsaye bakin 'kofar bedroom cikin wannan rigar da duk surorinta waje, gashi babu komai jikinta banda ita d'in, sakar baki sukai suna dubanda kawai cike da mamaki, Aunty Hafsat ce takai dubanta wajen, dai-dai lokacin da Haby ta tako ta nufi wajen Ya Nura tawani rungumeshi ta baya kamar babu kowa a falon da sauri ya Nura yajanyeta daga jikinsa yana fad'in "haba haby bakiga Aunty Hafsat da yara bane" tsaki Haby tayi sannan cikin shagwa'ba tafara fad'in "haba dear sabida mutane sai mu kasa jindad'in rayuwar aurenmu, su mai yakawosu gidan amare da safiya haka, ai sunsan abinda zasuzo sutarar" ta'karashe maganar tana hararar Aunty hafsat, cikin takaici Aunty Hafsat ta dubesu, tama rasa abinda zatace hakanne yasanyata tattara hannuwan su Nana tafito daga cikin falon da sauri, Ya Nura yabiyo bayanta, kafin yazo har takai cikin harabar gidan tabud'e motarta tasanyasu, cike da magiya Ya Nura ke lallashin Aunty Hafsat kamar zaiyi kuka, Aunty Hafsat tace "kada kadamu ba laifinkabane laifinane nazuwa gidanku da safe kagane muhad'u a gida kawai" tafad'a tana mai tada motarta tafice daga cikin gate d'in.

Ya Nura yajima,nan tsaye cike da takaici, yana tunanin hukuncin da zaiyiwa Haby idan yakoma, a zuciye ya koma cikin gidan, ko da yashiga falon tana nan cikin shigar daya barta, sai ma zama da tayi bisa d'aya daga cikin kujerun dake falon, ta kunna tv tanata karkad'a 'kafa, Ya Nura nashigowa zaiyi magana kenan ta dubeshi ido cikin ido fuskarta d'auke da wani irin mugun murmuahi, sai gashi yama mance da abinda yafaru, ya'karasa bisa kujerar datake zaune yazauna, yad'ora kansa bisa kafad'arta takama wasa da gashin kansa kamar wani yaronta.
Ranar kashe wayoyinsa matayi, ta kuma hanashi fita, shi kuwa duk abinda tace babu musu, koda yaso yin musu da sunhad'a ido zai saduda, yinin ranar sunyitane cikin gurzar amarci, acewarta itafa bata gajiya dan haka sai dai yayi ha'kuri da ita, sai ta zama angon ya koma amaryar (TAB...! DA MAMAKIFA WAI MENENE SIRRINNE?, BAZAKU TAMBAYABA?, KO DAYAKE KUBIYONI DAI).

ko da Aunty Hafsat ta isa gida cike da takaici tafito daga motar tashige gidan, kai tsaye falo ta nufa, tunawa da tayi akwai ba'ki agidan ashine yasa tasaki fuskarta ta wuce cike da murmushin ya'ke, taja hannun su Nuratu zuwa d'akin Mama domin babu kowa takora musu gargad'in kada taji wanda yayi maganar abinda yafaru, sannan tafito ta nufi d'akin Inna anata tambayarta yata barosu fatan dai lafiya tadawo da wuri haka, sai tabasu amsa da lafiya kawai, sannan tami'ke tanufi d'akin Aunty nanne babu kowa, su Nuratune azaune falon suna game, bedroom nata tashiga takwanta tana kallon cilling, tunanin abinda yafaru kawai take, tausayin d'an uwanta yakamata sosai, domin tasan akwai aiki agabansu, shiyasa ita tunfarkon maganar auren abin bai kwanta mata araiba, kawai tayi shirune kasancewarta bata da 'yancin yin wani abu akai.
har Aunty tazo d'akin tazauna bisa gefan gadon kusa da ita amma Aunty Hafsat bata saniba sabida nisan da tayi a tunani, sai da Aunty ta dafata sannan tafarka firgigit tami'ke zaune, had'e da dafe kanta dataji yasara mata.
Aunty tace "lafiya kuwa Hafsatu?, kinsan dadewata zaune anan? tunanin mai kike haka?" Aunty Hafsat tad'ago kanta tare da ajiyar zuciya tana fad'in "wallahi Aunty wani abune ya girgizani yau agidan Nura, al'amarin yabani mamaki da tsoro sosai"
Aunty tace "kamarya fa, ban fahimcekibafa?"
Aunty Hafsat tayi ajiyar zuciya, sannan tafara bawa Aunty labarin dukkan abinda yafaru, Aunty tayi shiru itama kanta yakulle sosai, can Aunty tayi ajitar zuciya tana fad'in
"al'amarin da mamaki da d'aure kai, amma dai koma menene addu'a itace mafita, ki cire komai aranki, kuma shawara kada kisanarwa Mamanku, kada hankalinta yatashi kinji, hakan zai iya jamata damuwa, ace daga kai amarya jiya anfara samun sa'bani, kije tana nemanki tund'azu, nima banzaci kinananba" tafad'a tana mi'kewa ta sake duban Aunty Hafsat, "kiyi 'ko'karin danne zuciyarki, amma nima wallahi tunkafin yau nadad'e ina kokwantan wannan had'in, amma babu yanda zamu iya da tsarin ubangiji, domin komai na Allah ne kitaya d'an uwanki da addu'a kawai" Aunty Hafsat ta gyad'a kai, ita kuma tafice daga d'akin.

Aunty hafsat tad'an jima azaune, kafin ta fito daga d'akin ta nufi d'akin Mamansu jikinta duk babu kwari, amma hakan yasanyata tadaure ta saita kanta domin kada Mama ta fahimci halin da take ciki.

koda tashiga d'akin Mama na zaune gefan gado da waya ahannunta, Aunty Hafsat ta 'karasa tazauna kusa da ita, Mama tace "wai yanaga kundawo da wuri haka?, ko wani abunne ya faru? naganki kuma cikin damuwa" Aunty Hafsat tayi murmushi tana fad'in "babu komai Mama, lokacin da mukaje sannan suka tashi daga barcine shiyasa kawai muka dawo" Mama ta gyad'a kanta kawai tana fad'in "neman wayarsa naketayi tundazu akashe, amma tunda naji kince lafiya suke shikenan, kije can d'akib Abbanku Hamza na nan yana jiranki, wai yakira wayarki baki d'agaba" sai lokacin Aunty Hafsat ta tuna da wayartama, murmushi tasakeyi tace "ayya namanceta a cikin jaka wallahi, natafi d'akin Aunty nakwanta nagajine" to kifita kije yanzu" Mama tafad'a tana mai ficewa daga d'akin.
Aunty Hafsat tayi ajiyar zuciya, sannan ta nufi mirrow ta gyara fuskarta, kafin ta nufi wajen mijinnata.
[06/01, 17:53] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》Book1

mallaka-----QURRATUL-AYN

22

*****KASHE GARI*****

Har kashe gari Haby bata bar Ya Nura yafito daga gidanba, neman duniya Khamis yayi masa a waya amma shiru, ga ba'kinsu nanesa nasonyin sallama dashi zasu koma gida hanne yasanya Khamis nufar gidan Nura domin jin ko lafiya?
Da isarsa abakin gate ya tsaya yana tambayar gate man, lafiya kuwa mutanan gidan suke? gateman yabashi amsa shidai yana da tabbacin babu wata matsala, hakan yasanyashi 'karasawa cikin harabar gidan Khamis yayi parking motarsa cikin parking space, ya fito ya nufi cikin gidan.
Chapter 16 · 0% Book details