Sashe 17
Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
lokacin Ya Nura nazaune kan kujera a falonsu da jarida ahannunsa yana karantawa yayin da 'yar mulkin nasa ke kwance bisa cinyarsa, cikin wasu riga da wando dasuka kama jikinta, wuyan rigar nada girma sosai, wanda yafito da rabin 'kirjinta duk awaje, kanta ko d'ankwali babu, sai ribom data sanya taka gashin nata, cingum ne a bakinta tanata aikin taunarsa.
Khamis yai sallama bakin 'kofar falon batare da ya shiga ba, jin sallama yasanya Ya Nura ajiye jaridar agefansa yana duban Haby, dako motsi bataiba bare ta kula da wata sallama da ake, sai da Khamis yasake mai-maita sallamar sannan Haby ta buga wani tsaki tana fad'in "wai waye haka?" Khamis yace "nine Khamis" "sai ka shigo ai" Haby tabashi amsa, batare data tashi daga kan 'kafar Ya Nuraba, shi kuma yakasa furta ko da kalma d'aya.
Khamis ya danna kai cikin falon, cikin murmushi, ganin Nura da yayi zaune abin yabashi mamaki sosai, Haby ta dubeshi a wula'kance da fad'in " lafiya dai?, kazo katsaya akan mutane mai kake bu'kata?" Khamis sakar baki yayi yanaa duban ikon Allah, Haby ta tashi tazauna ta d'ora 'kafa d'aya kan d'aya tana girgizasu game da 'kare masa kallon wula'kanci tace "tambayarka,nake kayi shuri kana dubana" Khamis yaja wani mugun tsaki yana fad'in "ni ba wajenki nazoba wajen Nura nazo ki rufe mana baki malama" Haby ta sanya wata muguwar dariya tana fad'in "ok to dakyau hakan ai gaka gashi kuyi magana".
khamis yace "Master wai lafiyarka kuwa?, kana ganina amma ka tsaya kana kallona" Ya Nura mai makon yayi magana sai ya mai da dubansa kan Haby, da dukkan alamu umarninta yake jira.
Khamis yayi ajiyar zuciyar kawai yana kallon ikon Allah, can Haby tayi murmushi tare da hura cingum d'inta yaba da kwai ya fashe, ta dubi Khamis tana fad'in "kafad'i dukkan abinda yake tafe da kai, domin sai da umarnina zaiyi komai ayanzu" Khamis dubanta kawai yayi yad'auke kai aransa yana fad'in "kyan banza kyan d'an maciji" afili kuwa gyaran murya yayi yasake duban abokin nasa cike da tausaya, yaga alamun dukkan abinda tafad'a akwai 'kamshin gaskiya ciki, kuma shidai burinsa yafita da Nura sufita kunyar abokai, ya zaiyi dole yabi umarnin nata, Khamis yasake duban Haby akaro na biyu cike da tsana yafara fad'in "inason zamu fitane, domin yin sallama da abokanmu, zasu wuce gida" Haby ta dubeshi sama da 'kasa kamar bazata furta komaiba, sai kuma tamai da dubanta kan Nura tana fad'in "sai ka tashi kashirya ai" Ya Nura yami'ke da saurinsa ya nufi bedroom, baki d'aya da kallo suka bishi Haby ta kece da wata muguwar dariya, tana duban Khamis kafin tace "ji mana mallam, ruwankane ka rufawa abokinka asiri, ruwankane ka tona, amma bakayi mamakiba yanda abokinka ya koma mijin tace ko ince mijin kantace a dare d'aya" tasake sanya dariya, Khamis jiyayi kamar ya rufeta da duka, ko kuma yahad'iyi zuciya tsabar takaici, sai yajima tsabar tsanar da yayiwa Haby ayau gidanma yatsaneshi yaji kaman akan 'kaya yake.
mintuna kad'an sai ga Ya Nura yafito cikin wani bluen yadi, yayi kyau sosai, Haby tace "kada dai akai dare " da sauri Ya Nura ya furta "to, madam" suka fice Khamis ko takanta bai sake biba.
tafiya suke amotar amma babu mai furta komai, Khamis yamai da kansa ga driven, Ya Nura kuwa kwantar da kasa yayi bisa kujerar idanuwansa arufe, jefi-jefi Khamis na aikin jan tsaki, tare da duban abokin nasa, cike da tausayawa rayuwarsa.
har suka iso hotel d'in da abokan nasu suka sauka, suka gaisa sunata zolayar ango, shi dai murmushi ne nasa kawai, Khamis kuwa kan dole yake ya'ke, har dai suka kammala komai suka raka abokan nasu airport, sannan suka juyo kan motar tasu zuwa gidansu Ya Nura akan hanyarsune Khamis yakasa daurewa domin shirun da Nura yake yafara damunsa duk da yasan shi bamai surutu bane, yad'an dubeshi ta gefan ido yana fad'in "wai Master taya hakan yafaru?" Ya Nura ya dubi Khamis tsahon wasu lokata kafin yakau da kai, kamar bazaice komaiba, har Khamis zau sake magana sai yaji yana fad'in
"nima bansan yanda akai hakanba, amma idan ina tare da ita inajina kamar baniba, kawai kadingayimin addu'a"
Khamis ya dubeshi cike da tausaya, daga haka basu sake furta komai har suka iso gate d'in gidan, gate man yabud'e gate, Khamis yasanya hancin motarsa zuwa ciki, ya nufi parking space yayi parking, amma Ya Nura ko motsi baiyiba, illama 'kurawa gidan idanu da yayi kamar yana nazarin wani abu akan gidan, sai da Khamis yayi masa magana sannan yasanya 'kafa ya fito, suka nufi cikin gidan.
suna shiga mutan jigawa suka kama yi musu tsiya, nan d'inma Khamis ked'an kareshi amma shidai murmushine nasa kawai da haka suka gaisa da kowa suka nufi d'akin Mama, tana zaune falo dasu Ammy da Aunty harda Aunty Hafsat domin bata tafiba, cike da kunya Ya Nura yake gaishesu, suna ansawa sai yaji yanajin nauyin had'a ido da Aunty Hafsat, ita kuwa 'kura masa idanuwa tayi kamar tana so tafahimci wani abu akansa, Ammy ta dubeshi da fad'in "lafiya dai Nura, naganka jikinka duk amace?" Mama tace " nima naga kamar babu wal-wala atare dasu" Khamis yayi saurin fad'in "babu komai Mama, gajiyace kawai" suka mi'ke domin zuwa d'akin Inna, anan dai sund'anyi barkwanci kafin su fito su nufi d'akin Momyn Haby, anan kam sunga kallon wula'kanci da 'kas'kanci, Khamis yasake cika da mamakin wannan lumbu-lumbu irin nasu, ya fahimci duk wanda yace baya son ka da safe da yamma yazo yace yana sonka to 'karyane.
haka suka fito jiki amace, da Aunty Hafsat suka gamu a tsakar gida tace "ku sameni a falon Abba zamuyi magana" ba musu suka nufi can.
Aunty Hafsat dubansu take d'aya bayan d'aya kawai, musamnan 'kanin nata, Khamis yayi ajiyar zuciya yana fad'in "to kinji dukkan abinda yafaru yau" kuma duban Ya Nura tayi daya sunkuyar da kansa, bazaka iya tan-tancewa a wanne hali yakeba.
ajiyar zuciya Aunty Hafsat tayi kamin tace "nidai ahalin yanzu Khamis babu abinda zan iya cewa, illa kawai mu tayashi da addu'a domin yana cikin tsaka,mai wuya, amma insha Allahu zansan abinyi, matsalar d'ayace tafiyar da zaiyi, amma duk yanda za'ayi zansaka atayamu da addu'a domin babu abinda yafi 'karfin Allah" Khamis yace "hakane Aunty, nima insha Allahu zanyi wani abu kai, domin ba aboki nad'auki Master ba, d'an uwa" sun tattauna abubuwa da yawa, duk da Ya Nura baya cewa komai, dubansu kawai yake domin shi aganinsa babu abinda zaiyi, babu abinda zai iya, sun koma sunyiwa su Mama sallama kafin su fito zasu tafi, a harabar gidan suka hangi su Nuratu can cikin lambu suna wasa Ya Nura yatsayawa yayi yana dubansu cike da nazari, wanda Khamis yakasa tan-tance wanne irin nazari yakewa abu idan ya 'kura masa ido, sai da Khamis yaja hannunsa sannan suka wuce zuwa gidan Nura, a bakin gate Khamis ya ajiyeshi yajuya acewarsa babu abinda zai koma yayi agidansa.
Haby nazaune falo da waya akunnanta tana baiwa Zuly dukkan abinda yake faruwa agidan nata, da irin wainar data toya jiya zuwa yau, sunata shewa da 'karawa Haby wani makircin, yayi sallama yashiga ta dubeshi tad'auke kai tana fad'in "to Zuly tawa sai zuwa anjima zamuyi waya zakuji wani zazzafan story d'in domin yanzu holo'kwan nawa yadawo" suka sake sanya dariya kamar zasu fasa wayar.
[07/01, 00:20] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book1
mallaka-----QURRATUL-AYN
23
Wasa-wasa al'amarin Ya Nura sai 'kara ta'bar'barewa yake, cikin sati biyu Ya Nura yazama ko kad'an baya iya sarrafa kansa akan al'amuran Haby, akaran kansa yanajinsa kamar bashiba, amma kuma,baya iya dogwan nazari akan hakan, yana kallon kansa komai yayi dai-daine.
malesia takirashi akan batun zuwansa gobe, Haby tacika da murna domin tana ganin barinta nigeria shiyafi alkhairi da cigaban dukkannin wasu har'kallolinta, domin zamanta zai iya kawo cikas da tonuwar sirrinta.
Da dare suka shirya shida gimbiyartasa domin zuwa,gidansu danyin sallama da iyayensu, wanda dukkan umarnin Haby ne, badan mahaifiyarta dake gidanba da bata zoba.
Da sallama suka shiga cikin babban falon gidan, dake dukkansu suna falon suna hira, amma banda Momyn Haby domin itama ungulu takomo gidanta na tsamiya, sama-sama Haby ta gaida su Mama tami'ke zata nufi d'akin Momynta, da rawar jiki Nura yami'ke zai bita, Mama tace "a'a ba dai tafiyaba?" wani kallo Haby tawatsa masa yakoma yazauna, sannan tasanya kai tafice, Mama da Aunty sakar baki sukai suna duban ikon Allah, domin daman masu zuwa gidan nata kawo musu gulmar halin da d'an nasu yake ciki, Aunty daman tasani, Mamance take ganin kamar gulmar mutanece kawai, duk da itama wani lokacin tanajin ajikinta kamar gaskiyane, yau kuwa gashi agabanta tagani, ga irin duban da matar tasa ke masu, uwarta kuwa yanzu rashin mutunci take masu sanranta danma Abba yanzu yadawo daga rakiyarta,tana d'an shakkarsa.
Mama tayi ajitar zuciya suka dubi juna da Aunty, su Nuratu nacan suna aikin game, Ya Nura daya koma yazauna shima ajiyar zuciyar yayi, sai lokacin yasaki jikinsa suka kama hira kamar bashiba, can su Nuratu suka dawo wajensa suna yimasa 'korafin bayaso suje gidansa, murmushi yayi kawai batare daya kulasuba, domin baisan abinda zaice dasuba shi gashi bayason 'karya yatsani maiyin 'karyama, dayaga zasu takura masa tuni yayi musu jan ido suka koma game d'insu.
Mama ta watsa masa harara tana fad'in "sai dai kayiwa 'kannanka jan ido, amma ka kasa sarrafa gidanka ko?" a firgice ya dubi Mama sai kuma yayi 'kasa da kansa, haka kawai yaji zuciyarsa na'kuna, Auntyce tayi saurin kau da zancen da fad'in "goben kamar da yaushe zaku tafi, ko ba'ason rakiyarmu airport ne?"
Ya Nura yayi murmushi yace "a'a shidda nasafe zamu tashi, addu'arkuma ta isa, Mama dan Allah kidinga yimin addu'a, kada kiyi fushi dani ako da yaushe...." ya'kareshe maganar kamar zaiyi kuka, dai-dai sanda wayar hannunsa takama ringing, yana ganin number Haby ce da rawar jiki yad'aga, cikin tsiwa da rashin mutunci take fad'in "idan kagama gaisawa da tsohuwar taka, sai kazo ka gaida tawa ko, sha-sha kawai" takashe wayar, da rawar jiki yafice daga d'akin ba tare daya sake cewa komaiba.