Sashe 22
Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kiran sallar ishar da akaine yasanya Ya Nura da Khaleel mi'kewa suka nufi masallaci, Nana tace "Rahma kuzo muje gidan Ammy musanarwa Nuratu zuwan Ya Nura" suka fice cike da d'aukin kaiwa Nuratu kyakkyawan labari.
[10/01, 21:55] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》*Book1
mallaka-----QURRATUL-AYN
*29*
*KASHE GARI*
kashe gari misalin 'karfe goma da rabi nasafe, Ya Nurane sanye cikin wani farin yadi, wanda ana iya hango best d'insa ta ciki sabida shara-sharansa, 'kafarsa sanye da wani ba'kin takalmi, idanuwansa cikin farin glass daya 'kara masa kyau, sannan yad'ora ba'kar hula akansa, duk da ramar dake baiyane ajikinsa hakan bai hana kyawunsa baiyanaba.
ya fito daga d'akinsa ya kulle, mai makon yayi cikin gida gate ya nufa, suka gaisa da mai gadi yafice kai tsaye tsallakawa yayi yanufi gidansu Nuratu.
Da sallamarsa ya shiga cikin gidan, Ammy dake falo ta amsa masa cike da farincikin ganinsa, yazare takalminsa yashiga a'kasa yazauna yana gaisheta ta amsa fuskarta cike da fara'a, tana tambayarsa anzo lafiya? ya amsa da "lafiya 'klau, naso shigowa ajiyan to gajiya tahanani wallahi" "babu komai, hutu na dakyau ai" Ammy tafad'a.
ta mai da kanta cangefe tana fad'in "ke bakya ganin yayan naku, amma ko gaisuwa babu" sai lokacin Ya Nura yakai dubansa zuwa inda yaga Ammy nakallo tana magana, Nuratuce kwance bisa doguwar kujera, da wani 'karamin littafi ahannunta mai suna (HISNUL-MUSLUM) tana karantawa, tana sanye da wani riga da wando pink, wandon yad'an kamata, rigar kuma daga sama zuwa cikinta dai-dai jikinta, daga 'kasa kuma tabud'e antsaga gefe da gefanta, tayi rolling da blue d'in mayafi, jelukan kalbar kanta sunzubo abayanta, Ya Nura yayi murmushi kawai
Ammy tace "magana nake maki, kuma sannan kiwuce kikawo masa d'an abin ta'bawa, da dukkan alamuma baka karyaba" Ya Nura yasake murmushi yace "wallahi kuwa, cewa nayi bari inzo mugaisa naje inyi breakfast daga baya, domin ina shiga gidan zasu shagaltar dani da hira" "ai dole munyi kewarka sosai ai" Ammy tafad'a, Nuratu ta ajiye littafin ta ziro 'kafafunta da suka sha jan lalle 'kasa, tana tura baki da 'ku'kuni ta furta "ina kwana" "ban ganshiba" Ya Nura yabata amsa, yana dubanta, Nuratu ta murgud'a masa baki, tazo ta wuce ta gabansa zata fice, yad'an bugi 'kafarta tayi kaman zata kifa, sai kuma ta tsaya tajuyo ta dubeshi da harara ta fice, Ammy tace "tsabar masifa har zata fad'i, ni dama kinfad'in mara kunya kawai"
Ya Nura daya bita da kallo yadawo da dubansa gun Ammy yana fad'in "haryanzu dai Nuratu na nan yanda nasanta, tsiwa da rashin kunya bai raguba, sai girma dai da akai" ya 'karashe maganar yana janyo littafin data ajiye yaduba, tare da murmushi aransa yana fad'in "ko yaushe rabonsa da karanta wannan litrafinma, bare azo batun karatun al'qur'ani" ya mance, Ammy ce tadawo dashi daga tunanin da fad'in
"ai Nuratu na nan yanda kabarta, sai dai girma da akai, inda take burgeni kad'ai waje d'ayane, bata wasa da addininta, idan ba karatun boko ba, babu ruwanta da karance-karancen banza, tafiso tad'au littafin addini tana biyawa, amma idan tsiyarta ta motsa kai kace aljanune akanta" sukai dariya tare, Nuratu tashigo da sallama ta ajiye babban faranti agabansa, amma fuskarnan tata atur'bune, kamar zata sanya kuka, ta ajiye takoma inda tatashi tayi kwanciyarta, Ammy tace "au bazaki zuba masaba" ya Nura yace "a'a barta,na zuba"
Nuratu tami'ke da 'ku'kuni tana fad'in "ya zuba mana ai yana da hannun dukan mutane, amma abinci ace sai an zuba masa" tafad'a tana mai ficewa daga falon tayi waje abinta.
ya Nura dariya yayi yace "au kice ri'kona ake?" Ammy tace "share shirman waccan kai dai ci abincinka"
ya Nura yabud'e flask d'in ya tsiyayo, sai yaga ashe kunun gyad'ane, ga soyayyan dankalin hausa da kwai daban, sai wani had'add'an danbun nama daketa tashin 'kamshin bai saniba yanaci suna hira da Ammy sai ganin kwanuka yayi agabansa, suka sanya dariya da Ammy, Ya Nura yace
"wallahi abincin yayi dad'i, gashi daman har namancw rabona da cin irin wannan girkin, shiyasa nakeson dawowa nigeria ai, kodan cin girkinki Ammy" Ammy tayi murmushi kafin tace "kai dai canti kake kawai, to wannan ba girkina bane, girkin 'yar gidan takace" Ya Nura yad'an zaro idanuwa waje yana fad'in
"wai Nuratuce da wannan girkin, a lallai yarinyar taki ta girma" Ammy tace "ai kuwa, dan yanzu nan gidan da gidan Mama muna kwasar garar girki, dan bata da muwa da aiki ita dai tayi girki ace yayi dad'i, shine burinta" Ya Nura yayi dariya yana girgiza kai.
sunsha hira da Ammy sosai, dan sai wajen shabuyi yayi mata sallama yafito ya koma gida.
Da sallamarsa yashiga falon lokacin har Aunty suna falon, yana shiga Nuratu na gaban TV suna game da Rahma yayi sallamar, kallo d'aya yayi mata yad'auke kansa, Mama ta bishi da kallo tana fad'in "yau kuma ina kaje haka tun safe?"
"ina wajen Ammy wallahi muna hira, sannan naci wani abinci mai shegen dad'i"
Mama tayi murmushi tace "ai nama gane girkin wadda kaci, girkin Nuratune" Ya Nura yasake duban Nuratu, amma wannan karon fuskarsa ad'aure yake dubanta, itama d'aure fuska tayi tami'ke daga game d'in tayi cikin d'akinsu tabarsu nan falon.
Ya Nura yadawo da kallonsa, kan Mama yana fad'in "wai mai nayiwa 'yar taki take jin haushina?" Mama tasanya dariya tana fad'in "wakenan?" Nuratu mana" Ya Nura yabata amsa, Mama tace "ai daman tace indai kadawo babu ruwanta dakai, bazata shiga harkarkaba bare kace zaka harbeta" suka sanya dariya baki d'ayansu.
Ya Nura yace "bari inje gidan Hafsat Hilal yarakani domin ba lallai ingane gidanba"
Mama tace "ai kuwa dai ka gaishe da ita to, Abbankuma yana hanya yau shida Inna" ok Allah kawosu lafiya kafin sudawo nadawo ai insha Allah"
yaja hannun Hilal suka fice, Aunty nafad'in "kagaishemin da ita".
[11/01, 22:13] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》*Book1
mallaka-----QURRATUL-AYN
*30*
Baki sake cike da mamaki Aunty Hafsat ke duban Ya Nura, dake tsaye cikin falon, Ya Nura yatako da murmushi ya zauna bisa kujera tare da fad'in "rufe bakin haka, nine dai Nura, yau a gidanki" Aunty Hafsat tazauna tana dariya, aranta kuwa godiya take ga Allah daya amsa addu'arsu, dan jiya da Aunty tayi waya tasanar mata, jin batun tayi kamar wasa, sai yanzu da taganshi ta gas-gata.
suka gaisa cike da farincikin ganin juna, Aunty waya tad'auko, tahau daddannawa takara akunnanta, ringing d'aya aka d'aga cikin murmushi ta furta "kazo yanzu kaga abin mamaki" takashe wayar, tunanin Ya Nura,Hamza takira mijinta, sai kuma yaga mijinta yasauko da murmushi yana fad'in
"a'a kice yau gidannamu cike yake da manyan ba'kin malesia?" ya Nura yayi murmushi yabashi hannu sukai musabiha, kafin yace "toni zan wuce, ana jiranane" sukai sallama,yafice yana tsokanar Aunty Hafsat da fad'in "yau anga d'an uwa, babu ko rakiya ko?" Aunty Hafsat dariya tayi tana yimasa byee-byee.
ta dawo tazauna kenan suna hira, a kai sallama bakin falon, Aunty Hafsat tace "bismillah shigo mana" Khamis yad'ago labule yashigo fuskarsa d'auke da murmushi, ganin Ya Nura zaune yasanyashi sakar baki ya washe baki da fad'in "master...!" Ya Nura yataso cike da farincikin ganin aminin nasa suka rungume juna, Aunty Hafsat tana kallonsu fuskarta fal murmushi.
nan suka zauna ana hira, Aunty Hafsat tad'auki waya tana kira, can aka d'aga, suka gaisa tace "gashi zaune yazo jiya Baffa" Baffa yayi hamdala kafin yace "to kada kuyi masa tambayoyi akan komai, domin bai san komaiba akan kansa da matarsa tunda dai Allah yasa yadawo sai akuma dagewa da addu'a domin haryanzu tsunne bata 'kareba, bashi wayar mugaisa ko" Aunty Hafsat tami'kawa Ya Nura waya, tana fad'in "ungo Baffa na jigawane" cikin girmamawa Ya Nura yakar'bi wayar yana gaisheshi, kamar yana gabansa, yana 'kara jajjada masa muhimmancin addu'a, da cemasa yadingayi sosai, sukai sallama yakashe wayar.
nan suka cigaba da hirar yaushe gamo, wayarsa dake aljihunsace tayi 'kara, ya cirota ahankali, kamar bayason d'aga wayarma, ganin number da sunan wadda takira, yasashi dai-daita nutsuwarsa, su Aunty Hafsat ma gani sukai kamar jikinsa har 'bari yake, wajen d'aga wayar.
a hankali cikin sanyin murya ya furta "assalamu alaiki"
bata amsaba illa tambayarsa data hauyi "wai kana inane mallam, tun jiya haryau baka dawoba kuma ko ka kirani kasanarmin"
"am sorry ina Nigeria yanzu haka"
cikin kad'uwa da d'aga murya ta furta "what...! nigeriafa kace?"
"ehh mana, naji kewar gidane shine natawo, kema nacewa Momynki jibi zaki zo, saiki shirya kizo"
"a'a ni bayanzu zanzoba gaskiya domin ina da ayyuka agaba" ta furta maganar dagaji atsoracectake
Ya Nura yace "okey duk yanda kikai" yakashe wayar.
Aunty Hafsat da Khamis dubansa kawai suke, ya kammala wayar yajefata gefan inda yake zaune yana fad'in
"Haby tafiye rigima wallahi, shiyasa natawo bansanar mataba nasan bazata barni inzoba"
bai jira mai zasuceba yacigaba da fad'in
"wallahi jiya ina zaune a office kawai sai naji baki d'aya hankalina yatashi, narasa mai yakemin dad'i aduniya, naji nidai kawai gida nakeson zuwa inganku, hankalina baki d'aya ya'ki kwanciya, sai da na sauka a nigeria sannan naji nutsuwa tazomin, najini cike da nishad'in da rabon da inji hakan harna mance wallahi, da kayan aikinma natawo dagani sai systerm d'ina"
Aunty Hafsat da Khamis suka dubi juna, Khamis yace "yauwa ya akayi suka barka katawo to?"
murmushi Ya Nura yayi kafin yace "abi mai sau'ki kenan a 'ka ida aftr 1yrs ina da hutun 1mnth ne, to ni tunda naje banta'ba hutun kwana gudabama, sai jiya kawai nace hutu zanje, yanzu sai sanda naga dama zankoma har nan da 5mnth" .
Aunty Hafsat tace "to mudai sai anyimana 5mnth d'in za'a koma" yanda kukace" Ya Nura yabata amsa
nan suka cigaba da hira abinsu, har lokacin sallah yayi suka nufi masallaci da suka dawo, Aunty Hafsat tagama readyn abinci suka cika tunbinsu, sai yamma li'kis lokacin Hamza yadawo, sukai musu sallama, suka nufi gida a motar Khamis, zai saukeshi shi kuma yawuce gidansu.