← Book details Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 23

Sashe 1

Qiyayya Saganin Laifi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[17/11/2017, 03:16] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: QIYAYYA SA GANIN LAIFI··! 01

@QURRRATUL-AYN

SHAMFI'DA

BISMILLAHIRRAH MANIRRAHIM

Wannan littafi 'ka gaggen labarine, amma idan yayi dai_dai da rayuwar ka/ki kuyi hakuri kuskuren idea ne, banyi dancin fuskar wani ko wataba, fatana darasin dake cikin littafin ya ammafani al'umma
Littafin QIYAYYYA SA GANIN LAIFI··! littafine daya kawo maku wani saban salo naban mamaki kusani Annabi muhammad (S.A.W) awani hadisi yace (kada kutsananta son abu, haka kuma,kada ku tsananta qiyayya)
domin abinda kake qi wata rana zai iya zama shi kakeso sosai, haka kuma abinda kake so sosai wata rana zai iya zama kana qinsa sosai, sannan yace awani hadisin (Idan zaka so mutum kasoshi domin Allah idan zaka qi mutum ka qishi domin Allah) ALLAH yasa mudace, acikinn wannan littafi akwai ILMANTARWA, FADAKARWA, WA AZANTARWA SANNAN UWA UBA NISHADI DA BAN DARIYA (camedy) da TSAN_TSAN SOYAYYA kudai kubiyoni cikin litttafin QIYAYYA SA GANIN LAIFI··!

*** *** *** ***
NURATU! NURATU!! NURATU!!! wata 'yar dattijuwar mata tafad'i tana mai sanya kanta cikin d'akin, kai taye gado ta nufa tasanya hannu tana mai janye bargon tare da fad'in "nasan kinajina, to kada kitashi, 'karfe takwas saura" jin hakan da tayi yasanyata mi'kewa tsaye da sauri atsakiyar gadon, tana mi'ka, duka-duka bazata wuce shekara tawas da watanniba, dattijuwar bata sake fad'din komaiba tafice daga d'akin, Nuratu takoma da'bas tazauna kan gadon dai-dai sanda agogon d'akin yabuga takwas dai-dai, aguje tanufi toilet , nan da nan sai gata tafito jiki aji'ke da alamu wanka tayi, a gurguje ta shafa mai, ta sanya kayanka tad'auko jakarta tari'ko hijabinta a hannu, tayo waje da gudu tana fad'in "ni nawuce Ammy na" kai kace wani abin tashin hankaline yafaru, banda Ammy tasan halin d'iyar tata da tsorata zatai da yanayin data fito, ta nufi kitchen dan acan tajiyo motsinta, da zuwa kiss tayiwa Ammy agoshi, zata tafi Ammy takira sunanta, Nurat da takusa kaiwa wajen kitchen d'in ta tsaya da sauri tare da juyowa, Ammy tami'ko mata foodplask, Nuratu tad'anyi jim..kaman bazata amsaba sai kuma ta amsa da murmushi akan fuskarta, ta bud'e jakarta tajefa foodplask d'in, tayi waje aguje sai da tafita sannan tatuna bata saka hijab ba, ta tsaya tasanya duka_duka hijab d'in iya kacinsa wuya, wai gawarnan da zatayi taganshi zaune saman motarsa a bakin gate, da waya ahannunsa yana dannawa, gabanta yabada dammm, “yaushe yadawo?”Nuratu ta furta afila, tatako kaman wacce kwai yafashewa zata wuce ta gabansa tashiga gidan, wani mugun kallo ya watso mata tare da daka mata wata uwar tsawa, wadda sai da tasanya Nuratu sakin d'an guntun fitsari tana zare ido, “'karfe nawa yanzu?”ya watso mata,tambayar da bata shiryaba“amm ta..tahh takwas”tabashi amsa cikin rawar murya, kai kawai ya gyad'a gami da fad'in “mai yahanaki fitowa da wuri, yanzune lokacin zuwa skull?”“Aa ya Nura, Ammy ce bata tasheni....”mugun kallon daya watso matane yasanyata dakatawa, bata gama dai_daita tunanintaba sai saukar rankwashi taji atsakiyar kanta, yana fad'in “ni zakiwa 'kary?” ai kuwa ta runtuma wani uban ihu tana fad'in “Allah ya....”kafin ta 'karasa yakawo mata bugu a bakin, da gudu tayi cikin gate d'in, tana fad'in “wayyo Mama zai kasheni....!”
[17/11/2017, 14:04] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: QIYAYYA SA GANIN LAIFI··! book 1

02
MALLAKA.....QURRRATUL-AYN

*** *** ***
Tana shiga haraban gidan Mama da Aunty nakawo kai da saurinsu, sabida ihunta da sukajiyo suna sama, Nuratu ta'buya bayan Mama tana ihu, dai-dai sanda Ya Nura yabiyota, cikin 'bacin rai Mama ta dubeshi da fad'in “wai kai Nura baka girmane?, kai kullum rigima da 'kannanka, yanzu sabida Allah mai Nuratu tayi maka, ko kuwa tsabar cin zaline? daga dawowarka jiya da dare zaka fara zaluntar yara”
Aunty ta kar'be da fad'in
“a'a Mama kinmance halin 'yar taki kenan? nasan Nura bai da laifi yanzu haka Nuratun ce”Nura da yayi tsaye yanajinsu yayi murmushi yana fad'in “yauwa Aunty gayawa Mama dai, ita akan wannan yarinyar sai duk ta rufe idonta”
Mama ta galla masa harara, tana mai kamo hannun nuratu ta dafa kanta tana cewa “rabu dasu kinji, gayamin mai yayi maki?”“Mama wai kawai akan namakara fitowa makaranta shine ya dake ni,kuma fa Ammy ce bata tashe niba”Mama ta 'bata rai tana duban Nura “yanzu sabida Allah kana nufin kakaisu Hilal makaranta kabar Nuratu?”Nura yad'an sosa kansa da murmushi wanda ba kasafai yakeyinsaba sai da dalili, Mama tayi kwafa tajawo hannun Nuratu ta dan'ka mata naira d'ari biyun da idi almajiri yadawo mata da ita, tana mai fad'in “barni dashi maza kije kihau keke-napep yakaiki makarantar banda wasa kinji, kada ki makara”

Aunty tayi murmushi tajuya tana fad'in “nikam nakoma ciki bazan iya da rigimar 'yannan taki marajiba, ni wallahi ihun da tayi nadauka wanine ya mutu ko d'auketa akazo yi”bata sake bi takansuba tayi ciki abinta, Nuratu ta kai-kaici idon Mama tayiwa Ya Nura gwale, kwafa kawai yayi yafice daga haraban zuwa bakin gate.
Mama ta gogewa Nuratu fuskarta, tana rarrashinta tare da fatan Allah kiyaye ta kula da hanya.
Nuratu tayi murmushi tafito zuwa gate itama, ta bud'e gate d'in tasanyo 'kafa kenan taji andan'keta 'kam, tare da rufe bakinta, Nuratu tazaro ido ganin Ya Nura ne, idanunsa sunyi ja da alamu na'bacin raine, hannu yami'ko mata yana fad'in “bani kud'innan, yau zanga 'karshen rashin kunya”ba musu Nuratu tami'ka masa, domin tamatsu ya saketa sabida zafin ri'kon dayayi mata, sanya kud'in yayi a aljihunsa yana fad'in “wallahi kikamin ihu ko wani yun'kuri har Mama taji ta fito, Allah yau na lahira sai yafiki jin dad'i”Nuratu ta girgiza kai alamun bazata yiba, Ya Nura ya cikita yana fad'in “wuce kibani waje, kitafi a'kafa kuma wallahi zanbiyo sahunki naga bakijeba tammm”yafad'a cikin tsawa,yayi kwafa, Nuratu ta goge 'yar kwallarta ta murgud'a baki kamin tajuya takama tafiya tana fad'in “Allah ya isa mugu kawai”ciki ciki tafad'a dan kada yajita, shi kuwa saman mota yakoma yazauna yabi bayanta da kallo yana 'karewa shigarta kallo.
unifoam d'in jokinta black blue & white ne riga da siket, siket d'in iyakacinsa gwiwa, aka sanya safa fara zuwa gwiwar, sai riga fara sai aka d'ora falmaran kalan siket d'in, sai hijab fari babu batun d'an kwali ko hula, hijabin iya kacinsa wuyanta da kad'an yasauka kafad'a, shigar ba 'karamin yiwa Nuratu kyau tayiba kasancewar itad'in farace, ga diri ga kyawu, duk da 8yrs take amma hakan bai hana wasu daga cikin halittun jikinta bai yanaba, Nuratu ma'abociyar doguwar fuskace amma ba canba, sannan tana da cikar gashin gira dana ido, ga siririn hancinta dake 'karawa fuskarta kyawu tare da d'an ma dai-daicin bakin 'karami pink colour kamar tasanya jambaki, uwa uba abinda ke jan hankalin kowa akan Nuratu bai wuce blue eyes d'intaba mai jan hankali, gasu ma dai-daita tubarkalla sannan bata cika sirantaba amma bazakace mata mai 'kiba ba, tun yanzu kenan, ina ga kuma shekaru sunja, shiyasa duk wanda ya kalli Naratu yasan za'ayi had'add'iyar mace da kowanne namiji zaiyi burin mallakarta.

Ya Nura kuwa wani dogon tsaki yaja tare da fad'in “yarinya sai kace aljanah, mummuna kawai, gawasu shegun unifoam, shiyasa nace Abba yasanyasu makarantar mutumci amma ya'ki waishi wannan tafi ilmi”yasake jan tsaki (kunjifa Ya Nura kodai-kodai 🤣) .

har Nuratu tabar layin yana binta da kallo, yana mita acikin ransa.

Nuratu nafita titi tafiya tacigaba dayi, tana 'yan wa'ko'kinta, da alamu babu abinda yadameta, jin tsayuwar mota tayi abayanta tare dayin hon, ta juya da sauri tad'auka Ya Nura ne yazo kaita wani matashin saurayi tagani kyakkyawa yana fad'in “zo ki hau 'yan mata na rage maki hanya, naga kin makara ma" Nuratu tayi ajiyar zuciya had'e da hamdala azuciyarta, afili kuwa murmushi tayi tabud'e gaban motar tashiga tahakimce abinta (araina nace su Nuratu an iya danna lamba tara 9number).
Nuratu ta gaida mutumin tana sanar masa sunan makarantar tasu, shaf tamancema Ya Nura yace zai biyo bayanta, domin yariga yasan kunnen 'kashi irin na Nuratu, ile kuwa duk abinda tayi akan idonsa, har aka sauke Nuratu 'kofar school d'insu, tafito tayi godia mai motar yaja yatafi, tana juyawa suka had'a ido ko d'arr bata nuna jin tsorontaba, sai ma murgud'a masa baki da tayi, Ya Nura yabita da kallo kawai yana mamakin Nuratu wacce irin yarinyace, bai kuma bi takanta yasan 'batawa kansa lokaci zaiyi yawuce yabarta agun, amma ya 'kudurta aransa yau zai koya mata hankali kuwa.

Nuratu na ganin yabar wajen da gudu tayi bayan school d'in sai gata asaman katanga, ta wulla jakarta sannan ta sauka, tana duddubawa ko wani ya ganta, da taga babu kowa ta sunkuya tana tafiya asunkuye har zuwa wajen windown class nasu, dayake dai-dai saitin window wajen zamanta yake, ta jiyo uncle nasu a ajikin class d'in, abokiyar zamanta tasan halinta sau tari haka takeyi, ta matsa mata ta wullo jakarta, da yake window d'in irin mai glass ne, bata sha wahalaba wajen shigowa uncle nacan na rubutu bai kulaba, 'yan ajin kuwa babu wanda bai saniba, amma kowa natsoron Nuratu domin bahaushe naceawa (dokin mai baki yafi gudu), Nuratu ba wani 'karfi garetaba amma akwai baki, sannan babu malamin da baisan Nuratuba wajen rashinji da tsokana domin duk laifin daka tarar anyi a school d'in idan ka bincika da sa hannun Nuratu, ga surutu sai dai inda take burgesu d'aya akwai 'ko'kari Nuratu, dan ita ke d'aukan first class koyaushe, da ka karanta data iya, ko haurowan katanga babu wanda yasani acikin malaman, amma 'yan school kowa yasani, domin Nuratu ogace fannin makara, gudun duka yake sanyawa take haura katanga, gashi kuma class nasu daf da katangar school d'in, domin,idan akwai abinda Nuratu tatsana aduniyarnan to dukane, sabida duk aka ta'ba lafiyar jikinta to har jinya sai tayi, shiyasa take kiyaye lafiyarta.
Chapter 1 · 0% Book details