← Book details Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 28

Sashe 9

Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

KANO
Gida ne madaidaici ba za a kira shi na masu kudi ba, daga waje gidan bai wani hadu ba, a cikin gidan duniyar ta ke, don duk wani abin more rayuwa an tanade shi a ciki. Mutane biyu ne ke kula da gidan wadanda suke amintattunsa ne, su ne ke kula da komai na gidan.
Tunda ya shigo Kano bai iso gidan ba sai da ya je ya gama duk wasu harkokinsa, sannan ya nufi gidan. A harabar gidan ya yi parking. Idris ya yi saurin karasowa ya bude masa murfin motar cikin yi mishi sannu da zuwa.
“Ya na ganka kai daya Ina Adamu?”
“Ya fita karba wa Madam take away”.
“Madan? Wacce?”
“Nabila”.
“Nabila kuma, yaushe ta zo?”
“Tun dazu”.
Nan da nan yanayinshi ya sauya, bai sake bi ta kan Idris ba ya yi gaba.
Ya yi arba da ita ta fito daga wanka daure da tawul. Ya yi saurin kawar da kai. Ya sake tamke fuska.
“Ke ba kya jin kunyar abin da ki ke aikatawa ko?”
Ta yi dariya, “Saboda na ganka in fita da gudu in dauko hijabi in yaba ko ya ya Deedat? To ma me zan boye maka? Ka yi min wanka, ka sanya min kaya, Yayana mijina. To me ya rage?”
“Wannan abubuwan duk sun faru ne lokacin da kina karama, yanzu kin girma, ya kamata ki kiyaye”.
Ya shige bed room.
Ta yatsina fuska, “karamin abu kana son maida shi babba”.
Yana zaune a kan gado da laptop a gabansa yana tura wa abokan kasuwancinsa sako ta mail dinsa. Ta shigo sanye da wasu fitinannun kaya, sai faman karairaya ta ke. Ta zauna a kusa da shi.
“Na tsorata da rashin dawowarka, har na soma tunanin yadda zan iya kwana a gidan nan ni kadai”.
Ya rufe laptop dinsa ya kallo ta.
“Wannan ya zamo zuwanki na farko da na karshe a gidan nan, muddin ki ka kara tako kafarki gidan nan wallahi sai kin yi da na sanin zuwanki. Kuma yanzun nan ki shirya na kai ki gidan Salim, gobe ki wuce gida”.
Kuka ta saka masa.
“Yanzu saboda na zo ne duk ka ke gaya min ba dadi? Mene ne laifina? Sati na biyu ban sanya ka a idona ba, na dawo gida a do kance a ka ce ka taho, ba zan iya kwana guda ba tare da na ganka ba shi ya saka na biyo ka, kuma ai Mom ta san da zuwana, kowa ya san gurinka na taho”.
“Okey su su Mom sun san gaskiya suka take? Ina ganin hakan bai dace ba”.
“Ai su ma sun san abin da ya dace, amincewa da kai da suka yi ne ya sanya su barina na taho”.
“Idan sun amince min ke kuma fa? Shin ba su san ke din fitinanniya ba ce?”
“Yaya Deedat ka san abin da ka ke cewa kuwa?”
Mikewa ya yi zai fita, ta yi saurin shan gabansa.
“Ko ma me ce ce ni ai mijina na yi mawa, aure ne kawai ba a daura ba, akwai baikonka a kaina. A wata ruwayar ma tamkar ka aure ni ne…”
“Shi ya sa ki ke ta bibiya ta? Ai don an yi baiko bai zamo lallai a ce ni ne mijinki ba”.
“Hakan ba zai taba yiwuwa ba. Allah ma ba zai sa haka ba, na sani ina da rayuwa mai tsawo a gaba inda ba kai ne mijina ba, ba zan yi tsawon rai ba. Don kai Allah ya halicce ni, dole ne sai mun yi aure”.
Ta kuma sanyaya murya.
“Ka gaya min me ya sa ba ka damu da ni ba? duk lokacin da na yi maka maganar aure, sai ka nemi kashe min jiki. Zancenka kullum ba ya wuce aure nufin Allah ne, aure lokaci ne. ta bangaren iyaye ma cewa ka ke yi a kara maka lokaci, me ya sa ba ka jin tausayina? Me ye laifina? Ina son ka sani rayuwata ta ginu ne da soyayyarka, ban san me ake nufi da soyayya ba sai a dalilinka. Kai ne nutsuwa ta, idan ba ka son na ci gaba da bibiyarka ka amince a daura aure ko da ba a tare ba, zan iya jiranka zuwa duk lokacin da za ka gama shirinka”.
“Dadina da ke ba kya rabo da shirme. Kin cika shirme. Ba ni da lokacin tsayawa jin wannan maganganun naki, ni ban san me ye so ba, bana son kuma na sanshi. Zan yi aure kawai don cika umarnin Allah da Manzonmu. Ke ma haka nake so ki saka a ranki, sai ki samu sassauci a ranki. Kada ki kara yi min wani zancen so, don ba burge ni za ki yi ba, maimakon haka ma sai matsala da za ki kara ma kanki”.
kokarin barin gurin yake yi, da sauri ta riqe shi kamkam da qarfin da bai san tana da shi ba.
“Nabila, me ki ke nufi da hakan?” Ya fada cikin kausasshiyar murya.
“Yaya Deedat, ni mace ce mai tsananin bukata, na kai kololuwa. Idan ba ka bari an yi auren nan ba, zan iya aikata komai. Ka tausaya min don Allah”.
Da karfi ya watsar da ita gefe ta zube a kan carpet, tana faman maida numfashi.
“Yaya Deedat karya ka ke yi, burga ka ke yi. Na sani kai namiji ne mai girman kai, amma akwai mutanen da suka fi ka girman kai, sai dai ba su nunawa a irin wannan lokacin, ko shi sarki idan aka zo wannan gabar sauke rawaninsa yake yi. Da farko na san ba za ka ce ba ni da kyau ba, na san kuma ina da kirar da duk wani namiji zai so ya mallake ni. Zan fi yarda da cewar sona ne ba ka yi sam! Bana kuma burge ka, to ina son ka sani, idan ba ka bari an yi auren nan cikin wannan lokutan ba zan samu hanyar da zan sama wa kaina mafita, kuma dole ka aure ni, ni ajiyarka ce”.
Ta mike a fusace ta fita.
Ya koma ya zauna a kan gado, maganganunta ne suke dawo masa.
“Ummina, ban yi ma Ummina adalci ba”.
Da sauri ya mike, kokarin ficewa daga gidan ta ke. Da gudu ya cimmata ya damko hannunta ta shiga kiciniyar kwacewa. Tsawar da ya daka mata ne ya sa ta shiga taitayinta.
Bai saki hannunta ba har sai da suka dangana ga falo. Ya zaunar da ita, ya kasa zama sai faman kai-komo yake, ya koma ya dire gwiwoyinsa a gabanta yana son rarrashinta. Tausayinta yake ji musamman yadda idanunta suka tattasa saboda tsabar kuka. Ta ya ma zai iya wanke mata zuciya.
Ya lura Nabila babu abin da ta ke bukata irin tarayya da soyayya, ga shi bai iya ba, ya zai yi da ita? Ya dan cije lebe.
“Oh God! Nabila bana son cutar da rayuwarki shi ya sa nake ta jan lokaci, ke mace ce wadda ba za ki iya rayuwa ba tare da mijinki na nuna miki soyayya ba, ni duk irin wannan abubuwan ban sansu ba. Ban taso a gaban iyayena na ga hakan ba, na taso cikin tsangwama da qyama, Ummina ba ta tare da Babana, ni ban iya ba ban san ya zan yi ba”.
Duk sai ya dinga ba ta tausayi, kalaminsa sun taba mata zuciya, abin da ya tsana dai shi ta yi, ta dora hannunta a kan nashi.
“Yaya Deedat na fahimce ka, ka daina tuno da abubuwan da suka wuce, ni zan iya zama da kai, zan koya maka yadda za ka kula da ni, zan rayu da kai a yadda ka ke. Kada ka damu ni ina sonka”.
“No, Nabila kina buqatar miji jarumi wanda zai dinga kulawa da ke. Na ji mutane na cewa ci da sha ba shi kadai ake bukata cikin rayuwar aure ba. ana bukatar kulawa, kin ga ni kuma ban da isasshen lokaci, asalima ni ba mazauni ba ne yadda al’amuranki suka nuna kin fi son ko da yaushe kina tare da mijinki”.
“Sai dai ko rayuwa da ni ne ba ka son yi, amma ni zan rayu da kai a hakan’.
“No Nabila, akwai abin da ya rage da nake son gaya miki. Amma sai na komo gida, wannan shi ne zai zamo maganarmu ta karshe da ke, idan ki ka amince za a iya yin bikin a duk lokacin da ki ka shirya kin ji?”
“Me ya sa ba za mu yi maganar yanzu ba?”
“Dare ya riga ya yi, ina jin barci saboda gobe da wuri zan fita, ki bari kwana biyar kacal zan yi, ina komawa gida zan gaya miki”.
Washegari da sassafe ya sallame ta bayan sun gama karin kumallo.
Chapter 9 · 0% Book details