Sashe 14
Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
*L* abari sai dai kai, ni da kullum ke kulle a cikin gida… amma dai yanzu gaya min yaushe zan ganka?”
Ya yi ajiyar zuciya, “Saura qiris na zo, to amma idan na zo gurin wa zan ce na zo in na tura kiranki, ke kuma wa za ki ce ya zo?”
Ta yi shiru.
“Sai ki ce abokinki ne?”
“Kai ai namiji ne, ba zai yiwu ba’.
“Ok, to za ki ce saurayinki ne ya zo?”
Nan ma ba ta iya magana ba. qoqarin share caftar ya yi, ta yi saurin dawo da zancen.
“Da gaske ni xin budurwarka ce, kana sona kenan?”
Ya yi murmushi yana jin daxin yadda yake zolayarta.
“Ina sonki mana”.
Da sauri ta katse wayar ta yi ciki da shi. Ta yi rigingine a gado haxi da runtse ido kawai, kunyar kanta ta ke ji. Ji ta ke yi kamar ta aikata babban zunubi, amma a can qarqashin zuciyarta wani irin nishaxi ta ke ji, ko me hakan ke nufi?
*** *** ***
“Ji yadda duk ki ka tada hankali kamar wadda ki ka aiki jaririya, wai ke ba kya ganin yadda hadari ya haxo, ga gari ya yi baqiqirin? Ni ba abin da ke tayar min da hankali irin iskar da ke tasowa, kin san Nurat da tsoro, na sani duk inda ta ke tana cikin ruxu. Na kira Hajiya Fati ta ce tun xazu ta fita a gidan, sai yanzu nake jin haushin rashin waya a hannunta, da sai mu kira ta”.
Shewa Aazeen ta yi ta qaraso gaban Amminta tare da rungumo ta ta vaya.
“Dube ki don Allah, inda a ce ni ce da yanzu kina nan hankalinki a kwance, da yanzu ma kina bacci, amma dai ki kwantar da hankalinki ‘yarki na da wayo, za ta dawo lafiya kin ji Amminmu, kuma na yi miki alqawari da kaina zan siya mata waya”.
Daga can vangaren Nurat hankalinta ya yi qololuwar tashi, musamman yadda ta ji ana ta tsawa gaba xaya a qanqame ta ke tafiya, cikin sharar qwalla duk motar da ta tsayar kko kallonta ba su yi. Tasowar iska ya tsananta sanadiyyar haka aka xauke wuta, gari ya soma duhu, jama’a sai gudu ake. Cikin lokaci qanqani ruwan sama mai qarfi ya sauko haxi da walqiya.
A hankali yake tafiya saboda kada ya haifarwa kansa matsala, lokaci xaya ya dallaro fitila ya yi arba da fuskar Nurat. Dam! Ya ji gabansa ya buga, sauran qiris ya saki sitiyari. Ya sake rage gudu, ya san rasa mota ta yi a daidai gabanta ya yi parking, bai fito ba bai kuma kashe motar ba, tunaninsa za ta doso shi don neman taimako, maimakon haka gani ya yi tana neman kwasa da gudu, haka ne ya sa ya tada motar. Gabanta ya sha ya sake tsayawa, ta yi saurin kauce wa motar. Bai sake mamaki ba in ya yi la’akari a abin da ya faru a makaranta, dole ya yanke shawarar yi mata magana. Kashe motar ya yi ya fito cikin sauri ya qarasa ya sha gabanta. Ta tsaya qyam kanta a qasa, jikinta na rawa.
“Ki shigo mota in kai ki”.
Ta yi saurin kaxa kai cikin tunanin inda ta san wannan muryar.
A hankali ta xago kaiza ta saci kallonsa, aka yi sa;a gari ya haska da walqiya idanunsu suka gauraya da juna. Gaba xaya Deedat ya kixime wani irin bugawa gabansa ke yi, shin wace irin yarinya ce wannan wadda yake jin abin da bai tava ji ga wata mace ba a yayin da ya xora ido a kanta, ko da kuwa a hoto ne tana yi masa kwarjini, ji yake yi ma kamar yana tsoronta, ita ma xin ta gane shi.
Abokin Principal xin sune sai dai haka ba zai sa ta shiga motarsa ba, ko da hakan na nufin za ta kwana tana tafe a qasa ne.
Ya sanyaya murya, “Ke fa xalibar abokina ce, na san kin gane ni, ba zan cutar da ke ba”.
“Ka yi haquri na gode”.
Yadda ya lura da ita ya sani ba za ta tava shiga ba, ga dare na daxa yi, ya xan kausasa murya wai ko da za ta ji tsoro.
‘Ki shiga na ce!”
Ta raunana murya kamar za ta rushe da kuka.
“Allah ba zan shiga ba”.
Takaici ya sanya ya shige motar, ya murxa key, amman ya kasa tafiya. Wayarsa ya xauko ya shiga kiran xaya daga cikin masu adaidaita sahunsa tare da yi masa kwatancen inda ta ke.
Bai bar gurin ba, har sai da ya tabbatar an xauke ta tukunna ya samu nutsuwa.
*** *** ***
“Ammi ga ‘yar mitsilanki nan ta dawo ba a cinye ta ba”.
“Za ki ci gidanku, ce miki na yi ba za ta dawo ba?”
Aazeen tana dariya, “Kin ga wannan Umman taki gaba xaya ta sukurkurce kamar ce mata aka yi an sace ki”.
“Ai ko ba don wani abokin Principal ya yi gadina ba da yanzu na sume a gurin, don ba kowa a gurin, ya yi ta nacin in shiga motar ya kawo ni, na qi shiga, har sai da na samu adaidaita”.
“Kin yi daidai”.
“Ammi, haka ne daidai? Inda ba ta samu abin hawa ba fa?”
“Na ma san Allah ba zai sa hakan ta faru ba”.