← Book details Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 28

Sashe 15

Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana gaisawa da Hajiya Rahma idanunsa na yawo, yana tsammanin ganin Nurat. Ya numfasa, “Ba kowa a gidan ne sai ke kaxai?”
“Mutuniyarka na xaki bacci ta ke yi, ba ta da lafiya, ita kuma Aazeen na shashenta”.
Ya miqe, “Bari in je mu gaisa”.
“To”. Ta ce da shi.
Ta miqe a doguwar kujera tana jin kixa.
Ta faxaxa fara’arta, “Yanzu nake shirin kiranka”.
“Kirana? Kina da magana kenan?”
Ta kaxa kai, ‘Kawai kewarka na ke yi”.
“Sai ga ni na zo ba, amma ni ma tawa ce ta kawo ni’.
Ta miqe zaune cingam ta xauka a kan table ta vare tare da cillawa a baki, ta tauna, ta yi qwai haxe da yin qas-qas ta koma ta tattara hankalinta kanshi.
“Ina sauraronka”.
Ya zauna kusa da ita, ya marairace kamar mai shirin yin kuka.
“Na kasa jurewa, ba zan iya ba”.
Ta bi shi da kallo, ‘Wai me ke faruwa?”
“Ina son Nurat, lokaci ya yi da zan furta mata. Rashin furtawa a wanan lokaci zai iya haifar da komai”.
Tuntsirewa ta yi da dariya, har da qyaqyatawa.
Ya qulu sosai, miqewa ya yi zai fita, ta sha gabansa ta kama hannunsa ta zaunar da shi.
“Afuwan, mu yi magana, amma ranka ya daxe ka rasa wadda za ka zava ta zame maka mata sai qwaila, kuma ma wacce ba ta waye ba? kuma wai har ma ka dubi idanuna ka ce kana son qanwata? To wai ma gaya min da me na rage ka?”
Ya watsa mata harara, “Ok, haka ki ke son na yi ta zama babu aure ko?”
“Why not, yanzun da me na rage ka ko kana son ka ce ni xin na gundire ka?”
“Kin ga Rangida wannan daban ne, kin san kamalar mutum shi ne aure ko?”
“Na ji wannan, amma me ya sa ba za ka samu gogaggiya irinka ba? Ka san Nurat qarama ce ba za ka samu yadda ka ke so daga gare ta ba”.
“Kin ga Rangida kada ki ce kishi ki ke da ita?”
Ta ja wani dogon tsaki.
“Matar arziqi ma ban yi kishi da su ba sai wannan? Kawai dai ina tsoron alaqarka da ita kada ka laluve mini ita’.
“Kin ga ki ajiye zancen wasa ju tausaya mini ki gaya min ya zan yi, ta ina zan fara?”
Ta lakuce masa hanci, “Dube shi don Allah ko kunyata ba ya ji. Ka ga shawarata ka bi a hankali, muddin ka kuskura gurin furta mata kalmar so, kai da ita, kun soma wasan vuya kenan in ma ba ka yi sa’a ba kun qulla gaba kenan don haka ka bi a sannu cikin dabara za ka fahimtar da ita a aikace”.
Ya miqe ya shiga zarya.
“Nurat, ban ga damar canza ta ba ne yarinyar bagidajiya ce amma ka ban lokaci, da sannu zan fahimtar da ita abin da duniya take ci….”
“Ban amince ba”. Ya yi saurin katse ta cikin gigita, “Ni rayuwarta ta yi min a haka nake son rayuwa da ita”.
Ya koma ya zauna cike da tsananin tsoro “Come down, abokina, kana tsoro ko, amman ba ka tabbatar ita din matarka ba ce ballantana ka…”
Turo qofar da a ka yi ne ya katse daga maganar da take son yi, sanye ta ke da zumbulelen hijab, Aazeen ta saci kallon Zaruk cikin muryar raxa.
“Haka xin yayi maka ko?”
Ya xan lumshe ido ya buxe alamar hakan ya yi masa.
“Yaya Zaruk sannu da zuwa”.
“Yauwa qanwa ta gwara da Allah ya kawo ki, daman ya dame ni da surutu”.
Shigar jikinta ya sanya Nurat jin kunyar Zaruk, three quater a jikinta na wando, sai riga plat, kan nan ya sha attach, ta lura da yadda Zaruk ke faman satar kallonta. Yana ji tamkar ya bi ta.
“Ya Zaruk me ya sa ba ka yi mata faxa na ga kamar tana jin maganarka”.
Ya maida kallonsa gare ta, “A kan me fa?
“A kan me? Ba ka ganin yadda ta ari al’adar da ta sava wa addininmu na islama?”
“Kada ki damu da hakan, ra’ayinta ne haka, wataran za ta daina da zarar ta shiga daga ciki shi kenan komai zai sauya, kamar ba a yi ba, kin ji?”
A hankali ta rausayar da kai.
“Haka ne Yaya Zaruk, Allah ya nuna mana lokacin”.
Wani mayen kallo ya dinga bin ta da shi har sai da ta tsargu.
Ya yi murmushi, “Ba kya son kallo da yawa ko? Ki yi haquri qanwata, kina da kyau da yawa. Ban gajiya da kallonki, da ma a ce mu dauwama a haka”.
Ta xan murmusa, “Yaya Zaruk ka iya zolaya”.
Ya sake riqe hava cikin kallonta.
“Murmushi na yi miki kyau, ina ma kada ki daina?”
“Yau ka zo ne musamman don ka tsokane ni ko? Ka san wani abu?”
Haka kawai ya ji zuciyarsa ta buga.
“Sai kin faxa”.
“Ammina tana son Yayata ta yi aure, na ga kai ma ka faxa idan ta yi aure za ta daina duk waxannan abubuwan shi ya sa nake ta neman taimakonka”.
“Shi ya sa na ce ki ba ni lambar mutumin nan”. Ya katse ta da faxin haja.
“Na san yadda zan bi in daidaita komai”.
“Ba ka sani ba, komai ya daidaita har na zurmo shi da bakinsa ya furta cewar yana sona”.
Lokaci xaya ya firgice duk walwalar fuskarsa ta dusashe, cikin shaqaqqiyar murya ya soma magana, “Kina son ki ce kin zubar da qimarki gurin roqonshi ya so ki ko? Nurat kin hauka ce? Me ya sa ki ka fitini kanki da yawa a kan wannan? Ki gaya min ki ke sonsa ko? Ki gaya min gaskiya”.
Ta tsorata da sauyawarshi.
“Yaya Zaruk ni in ce ina sonsa? Wace irin magana ka ke yi haka?”
“Shiru! Na ce ki rufe min baki, ni za ki raina ma hankali? Ni za ki yi wa haka?”
*💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞*

*NA*

*BILKISU H.MUHAMMAD*
_(Matar Auwalu By fos zage)_

*Free page 10*

*_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_*

*Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa*

*1. IZZATU*
*2. MULKIN MALLAKA*
*3. KAUNA CE*
*4. DACEWA*
*5. RASHIN RABO*
*6.TARAIRAYA*
*7. JINI BIYU*
*8. AKWAI BAMBANCI*
*9. TSALAR KAUNA*
*10. YA YI SAKE*
*11. ILLAR SABO*
*12. SO DA SANKARA*
*13. RASHIN RABO*
*14. WATA RAYUWA*
*15. HUBBAN SHADIDAN*
*16. BAKIN K'AZAFI*
*17. MATSALAR KAUNA*
*18. KYAN KUSKURE*
*19. WA YAFI SONTA?*
*20. GABA DA SO*

_NOW_
*KYAUTA ZUCIYA*

```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah```

*_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_*
*_2277439558 UBA Bank_*
Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*A* zahiri ta gama tsorata ba ta tava ganinshi cikin irin wannan yanayin ba, gani ta yi ya miqe a zafafe ya fice ya turo qofa da qarfi har sai da ta firgita, kawai ta bi shi da kallo, ta rasa me hakan ke nufi.
Ta sauke ajiyar zuciya, a sanyaye ta miqe ta yi waje.
A harabar gidan ta samu Ammi zaune tana alwala, Aazeen na qoqarin ficewa.
“A’a sai yanzu ki ka bar Ya Zaruk ya tafi?” Aazeen ta faxa.
Nurat ta xaure fuska.
Aazeen ta maida kallonta ga Ammi tana faxin, “Ammi da alamun tuwona maina za mu yi”.
“Ammi kina jinta ko? Wallahi za ta sa na daina kula shi”.
“Me ya yi zafi? Allah ya ba ki haquri, ai shi xin Yayanki ne”. ammi ta ce tana murmushi.
“To ai Ammi shi ma babu abin da zai yi da qwaila”.
“Eh xin na ji”. Nurat ta faxa a qufule kamar za ta yi kuka.
Binshi kawai ta ke da kallo, yadda ta ga yana faman dudduba ko’ina na gidan.
“Yallavai lafiya kuwa?”
“Ina duba ta inda zan fara ne”.
“Me za ka fara?”
“Rangida za ta yi manyan baqi daga Jos, tana buqatar a yi wa gidan kwaskwarima”.
Ta jinjina kai cike da takaici.
Ya janyo kujera kusa da ita ya zauna, ta dube shi cikin sanyin murya, ya fahimci haka, “Da magana ne?”
“Ina ganin bai dace a ce ‘yar da muka haifa ta dinga tsara mana abin da za mu yi ba, hatta da girki sai wanda ta ke so ake yi? Ya kamata ka yi nazari watarana fa gidan wani za ta je, za ta iya rayuwa da kishiya ko uwar miji, kana ganin za su xauki wannan? Waye zai iya zama da ita da wannan xabi’un? Ya kamata ka duba ka koma ka sauke ta daga wannan layin ya kamata Aazeen ta san rayuwa, sangartar nata ya yi yawa, rayuwa na iya juyawa a kowane lokaci bana fata, amma…”
Ya yi saurin katse ta, “Ba za ta tava ganin duhu a rayuwarta idan kina tunanin gidan aurenta ne, su kansu mazan yanzu har da iyayen nasu duniya suke bi, idan za ta ce mijinta ya durqusa ta hau bayansa ina rantse miki sai ya durqusa”.
“Shi kenan”. Ta ce da shi, ta koma ta tsuke baki.
“Kin yi shiru, ba gaskiya na faxa ba ne?”
“A naka ra’ayin ka yi daidai amma don ya kamata a qalla mu koya mata mu’amala yadda za ta jeranto wa wanda ya girme mata magana”.
“Okey, gaya mini wa ya tava kawo qararta? A kunnena ina jin yadda ake yaba mata, ba ta tava yin ba daidai ba”.
Ta miqe cikin qoqarin barin gurin, ta xan dube shi a qufule.
“A ganinka ba…”
Kan ya kai ga magana ta yi saurin barin gurin.
Chapter 15 · 0% Book details