Sashe 23
Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
*_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_*
*_2277439558 UBA Bank_*
Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_*
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*“T* unda dai su xin sun tafi komai ya wuce ko?” Ya faxa yana qoqarin matsawa jikinta.
“Ki yi haquri, taso mu je ciki zan nuna miki wani abu”.
Shi kanshi ya yi mamakin yadda yake faman kimtsa kansa kamar wani mace, wankan shadda ya yi gizna, ash colour, hularsa ma ash, hatta takalminsa ash ne, ya feshe jiki da turare ya fito sitroom cikin qoqarin gyara link xin hannun rigarsa.
Maryam zaune tana kallon talabijin.
“Wow, qaramin maigidan ka fa yi kyau, sai ina?”
Ya yi murmushi, “Matar Yaya yau zan tunkari mutuniyar. Yau zan yi mata zuwa na musamman”.
“Okey, kana son ka ce iyanzu ta san komai kenan?”
“Ke dai kawai ki yi min addu’a, ki bari sai na dawo mun yi maganar”.
Ya xauki key xin mota ya yi waje. Ta bi shi da kallo cikin tave baki.
Da alamar Hajiya rahma ba ta nan, hakan ya yi masa daxi, kai tsaye ya doshi vangaren Nurat.
Tana kwance a gado, bacci ta ke lakadan, iskan fanka na faman watsi da gashin kanta. Gabansa ne ya faxi, ya wani irin bugawa wani abu ya tsarga masa tun daga tsakiyar kai har zuwa yatsunsa. Duk yadda yake zana halittarta ta wuce nan, ashe dai bai ga komai ba?
Wani irin sha’awarta ya dinga shigarsa, zuciyarsa ta dinga ingiza shi da ya afka mata. Ya yi tattaki zuwa gabanta, ya xan ranqwafa a kanta, wani qamshi ya shaqa nan ya qara fitinuwa. Hannu ya kai zai xauke gashin da ya zubo fuskarta, ya ga ta xan motsa.
Tsam! Ya qame a tsaye, can ta qara nutsuwa cikin baccinta haka ya ba shi damar tattare gashinta yamaida shi baya. Ya xan matso da kansa daf da fuskarta zai sumbaci xan mininin bakinta. A karo na biyu ta sake motsawa, ya tuna idan ta farka ta ganshi akwai matsala. Da sauri ya fice daga xakin cike da tsananin so da sha’awarta, sai kuma ya jira ta a gurin Aazeen.
A daidai wannan okacin ta fito daga bathroom, bai san sa’ar da ya afka mata ba. sun gama shagalta da juna, gaba xaya sun mance a inda suke, hankainsu ya fita a jikinsu, shi kam Zaruk ji yake yi kamar tare yake da Nurat, surarta ce ta dinga yi masa gizo.
Daga vangaren Nurat firgigit ta farka, ta dinga ji a jikinta tamkar wani abu ya faru da ita. Ta miqe zaune, qamshin turaren Zaruk ta shaqa. Dam! Gabanta ya buga, da sauri ta dubi jikinta, riga ce a jikinta iya gwiwa mai xan siririn hannu. Ta miqe cikin sauri, hijabi ta xauko ta xora a kai ta shiga bathroom ta wanke baki. Al’adarta ce ko da baccin minti goma ta yi ba ta iya fuskantar kowa sai ta goge baki, ta xauraye fuska.
Ficewa ta yi daga xakin, kai tsaye sashen Aazeen ta nufa, duk takun da ta yi yana daidai da bugun zuciyarta. Haka kawai ta dinga jin wani tsoro na ziyartar zuciyar tata. Daf da za ta kutsa kai ciki ta dinga jin wasu irin surutai marasa kan gado, ta xan yi turus! Abu ya qi qarewa kawai sai ta tura kai ciki da qarfi. Gabanta ya buga, kanta ya yi wani irin sarawa yana kuma juyawa, jikinta ya hau vari. Ta yi saurin runtse idanunta ta kasa aminta da abin da ke gabanta, me ya sanya ta yi irin wannan mafarkin? Me ke faruwa da ita? Idan bacci ta ke Ubangiji Ya gaggauta farkar da ita.
Ta buxe idanunta, har yanzu suna nan, wayyo Allah ba mafarki ta ke yi ba, “Allahumma ajirni fi masibati…” Ta shiga maimaitawa cikin zuciyarta.
Kunyar kanta ce ta kamata, ta juya cikin matsanancin kukan da ke son qwace mata, gudu-gudu, sauri-sauri ta nufi xakinta inda ta zube a qasa. Wani irin azababben kuka ya qace mata, wani irin tsanar Zaruk ta dinga xarsuwa a zuciyarta. Tana ji a ranta ba ta tava tsanar wata halitta kamarsa ba.
Yaya Zaruk mutumin da ta ke matuqar ganin mutuncinsa wanda magana ba ta cika damunsa ba, idan yana magana wani lokacin tamkar wani limami.
Ta runtse idanu, kuka ya sake qwace mata, ‘Babu kama Yaya Zaruk babu kama, waye ya san tsawon lokacin da suke aikata hakan?”
Hirarsu da Fa’iza qawarta ta faxo mata, “In dai riqe hannu ne ashe da kowa ya samu ciki, da shegu sun cika duniya. Ke da Allah can tsokanarki Amminki ta ke yi, kawai tana tsoratar da ke ne kawai, ba kya ganin ‘yan Indiya har rungume juna suke yi da namiji, to su me ya sa ba su tava samun cikin ba? ‘Yan matan zamanin nan iyayen shan minti duk me ya sa ba su samun ciki?”
Nurat ta ce, “ko ma me ye ni dole ne in kiyaye, mahaifiyata ce yadda uwa ta ke da girma zai iya yiwuwa idan aka riqe hannun nawa in iya samun ciki”.
Ta dawo daga duniyar tunani, lokaci guda abin da ta gani ya dinga dawo mata.
“Yayata kin ci amanar Ammina, Zaruk na tsane ka, ba zan yafe maka ba”.
Taqarqarewa ta yi ta turar da shi, ya zube gefe yana faman ajiye numfashi.
“Kai wai ka mance a inda muke ne, ba ka tsoron wani ya ganmu?”
Da sauri ta janyo rigar ta saka.
Ya dube ta da lumsassun idanunsa,
“Aazeen, ina son Nurat, ki taimake ni kada in rasa ta”.
Ta xaure fuska tamau.
“Ba ka tava ganewa furta mata wani kalaman so zai iya nesanta mu da juna. Ka bari da zarar ta zana jarabawa sai ka yi duka xaya xauka”.
‘Ba zan iya ba, ba zan tava amincewa ba. wannan karon dole ne kowa ya sani. Na gaji, ina zuwa”. Ya ce da ita ya miqe.
Ta bi shi kawai da kallo.
Nurat ta gaji da kuka, idanun nan sun yi jawur har wani tasawa suka yi.
Takun tahowa ta ji, ta yi saurin kifa kai cikin filo, ga mamakinta muryar Zaruk ta ji a kanta.
‘Nurat, tashi za ki yi, ina son za mu yi wata magana da ke. Na zo ne kawai don ke, na san kina jina’.
Ji ta ke yi kamar ya watsa mata garwashi. Ya kaxa ya raya ko motsawa ta qi yi. Ya koma yi mata magiya tamkar dutse haka ta koma mishi, kamar zai yi kuka, tilas ya bar mata xakin, takaici bai sa ya bi ta kan Aazeen ba.