Sashe 16
Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
*** *** ***
Da murnarta ta danno kai hotel xin har zuwa xakin da yake, yana tsaye ya juya baya da gudu ta rungumo shi ta baya, ta daxe a haka ba tare da ya tanka mata ba. Ta sake shi ta zagayo gabansa, fuskar nan ta gani a xaure.
“Why?”
Ya kamo hannunta suka zauna.
Ya xauki tsawon lokaci kafin ya yi magana, gaba xaya ta gama kafe shi da ido, cikin son ji daga gare shi.
Ya furzar da wani huci.
“Ke ce ki ka lalata komai”.
Cike da mamaki ta dube shi.
“Ni kuma? Da na yi me?”
A qufule ya zayyane mata komai, hankalinta ya yi matuqar tashi. Ta miqe a zuciya, “Zan yi maganinta. Wallahi sai ta gane kurenta”.
Ta nufi hanyar fita, ya yi saurin janyonta ta zube a jikinsa, za ta yi magana ya danna harshensa cikin bakinta. Sun daxe a haka, cikin wani irin salo ya janye harshen nasa, sai dai tana manne a jikinsa.
“Ina son mu bi komai a hankali kamar yada ki ka ce yarinya ce za mu bi da ita ta dabara. Ina so ki samu bayanin komai daga bakinta, ina son ki yi mata wayo har ki samo mana lambarsa, inyaso sai ki bar min ragowar aikin, ni na san yadda zan ji da komai”.
“Okey, to shi kenan, ni zan tafi”.
Ya sake qanqame ta.
“me ki ke nufi, haka za ki tafi ki bar ni?”
“Na ga kai ma ya ba wannan ce ta kawo ka ba”.
Ya sanyaya murya cikin salon yaudara.
“Kin sani duk yanayin da nake ciki da zarar na ji ki a jikina na kan ji sanyi, bana iya jure rashinki, don Allah kada ki yi min xangwalilliya”.
Ta daddage ta tankaxa shi, “Ba za ka samu komai ba yau ko da na amince da kai babu abin da zan xorar, ni kuma ba zan yi abin da zai daxa dama wani ni na kasa nishaxantuwa ba”.
Ta miqe yana magana ta yi saurin ficewa a xakin.
Tun daga harabar gidan ta ke faman qwalla mata kira, ba ta ji motsinta ba har ta ratsa sitroom inda ta ga Ammi zaune a kan darduma da alamun sallah ta idar. Ba tare da ta ce komai ba, kodayake matar da ba ta yi sallama ba me za ta iya cewa? Kawao ta bi ta da kallo gurin nema mata shiriya.
A can xaki ta tarar da Nurat tana gyaran littattafanta, ba ta saba ganinta cikin wannan yanayin ba, don haka duk ta gama tsorata. Zama ta yi a kan kujera ta xora qafa xaya kan xaya tana faman haxa su, wannan shi ne alamarta duk lokacin da ranta yake a vace haka ne ya sa Nurat ta qara kiximewa, ba qaramin abu ne yake sanya ta haka ba. gabanta ya shiga bugawa tsawon mintina uku kamar ba za ta yi magana ba, sai faman huci ta ke.
“Ki gaya min ina son sani da wa ki ke yin waya a cikin waya xina?”
Ta ji tambayar ba-zata, tsananin ruxewa ta yi, ji ta yi tamkar numfashinta zai xauke.
“Wayyo Allah”. Ta ce a zuciyarta.
Wata irin tsawa Aazeen ta daka mata.
“ke nake sauraro ki yi min bayani, ko ke kurma ce?”
“Um-um…Aa’, um daman… da man… ba…ba…”
“Wannan wace irin magana ki ke yi haka, munafuka? Za ki buxe baki ko sai na yi miki xankaren duka? Shegiya lumbu-lumbu wutar qaiqayi, da an yi magana Ammi ta ce ke qarama ce, ko ke ustaziyya ce, nan kam ke baqar shaixaniya ce, wallahi in ba ki gaya min gaskiya ba yau sai kin raina kanki”.
Ba ta san sa’adda ta sa kuka ba, cikin shessheka, “Ni ban aikata komai ba, ban yi komai ba”.
“To gaya min yadda aka yi ki ke bin maza a cikin wayata, har kina amfani da sunana ki yi min magana”.
Ta ce cikin xaga murya.
‘Wayyo Allah na shiga uku Yayata kada ki yi mini mummunan fahimta. Kada ki zarge ni, don Allah ba zan aikata ba daidai ba, ki yarda da ni”.
“Idan kina son in rufa miki asiri, ki buxe baki ki gaya min gaskiya, in ba haka ba sai kin gane shayi ruwa ne”.
Hankalin Nurat ya sake tashi, duk lalacewar Aazeen hakan bai sa Nurat ta raina ta ba, Amminsu ta koyar da ita yadda za ta girmamata. Tana tsoron Aazeen ba ta ajiye mata kara ta tsallake, tana matuqar tsoron vacin ranta. Waxannan abubuwa su ke qara dasa wa Aazeen qaunarta, haka ne ya sa ba ta cika takura ta ba, wani fannin tana sane ta ke biye mata su yi ta shirme, duk kuwa da cewar ta bata shekaru takwas.
“Wato soyayya ki ke yi ko? Gaya min me ki ka sani game da so?”
Ta shiga rantse-rantsen cewar ba haka ba ne.
“Ba soyayya ki ke ba, me ki ke yi?”
Gaba xaya ta rasa kalmar da za ta kare kanta da shi.
“Okey, to me ki ke yi?”
“Da gaske nake Yaya, ban san me ki ke nufi ba, ban san me soyayyar ba. Ban tava ganinsa ba, ban san yadda ake yi ba, ki yarda da ni kawai dai na saba da shi ne saboda ke…” Ta qarasa zancen cikin shaqaqqiyar murya mai tattare da tsoro cikin kallon Aazeen xin.
“Okey, wato kina nufin ke ce za ki aurar da ni kenan?”
Ta shiga sintiri, ta koma ta tsaya.
“Oh ni yanzu kin gama zubda min mutunci kenan?”
Ta kai mata hauri da qafa. Jikin Nurat na krayma.
“Ki yi haquri, na tuba ba zan sake ba”.
“Sai kin gaya min ta yadda ki ka sanshi, idan ki ka yi min qarya sai na gaya wa Ammi na ke wadda kullum ke yi miki kallon yarinya mara wayo”.
Ta sake kiximewa, cikin sarqewar murya ta soma magana.
“Na saba da shi ne ta dalilin mistake xin lambar Anisa qawata wadda suka koma Lagos, ta ba ni lambarta shi ne kiran ya shiga wayarsa. Hakan ne ya sa muka saba da shi a dalilin ya ce shi yayanta ne. Na kan kira shi akai-akai ina tambayarsa labarinta, a haka muka saba, sai daga baya ya ce da ni bai ma santa ba. Yana da kirki haka ya sa muka ci gaba da gaisawa…”
“To me ya sa lokacin da ya ce da ke bai santa ba ki ka ci gaba da bibiyarshi? Kuma na duba na ga kaf ke ce kaxai ki ke kiranshi, tabbacin shi talakan talas ne?”
*💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞*
*NA*
*BILKISU H.MUHAMMAD*
_(Matar Auwalu By fos zage)_
*Free page 11*
*_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_*
*Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa*
*1. IZZATU*
*2. MULKIN MALLAKA*
*3. KAUNA CE*
*4. DACEWA*
*5. RASHIN RABO*
*6.TARAIRAYA*
*7. JINI BIYU*
*8. AKWAI BAMBANCI*
*9. TSALAR KAUNA*
*10. YA YI SAKE*
*11. ILLAR SABO*
*12. SO DA SANKARA*
*13. RASHIN RABO*
*14. WATA RAYUWA*
*15. HUBBAN SHADIDAN*
*16. BAKIN K'AZAFI*
*17. MATSALAR KAUNA*
*18. KYAN KUSKURE*
*19. WA YAFI SONTA?*
*20. GABA DA SO*
_NOW_
*KYAUTA ZUCIYA*
```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah```
*_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_*
*_2277439558 UBA Bank_*
Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_*
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation