Sashe 18
Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah```
*_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_*
*_2277439558 UBA Bank_*
Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_*
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*M* amakin yadda ta biye mishi yake yi. Ita xin ma haka ne, tana mamakin yadda ta kasa share shi, yau shi ne karo na farko da ta saki jiki da mutumin da ba ta san waye ba. babu alamun shashanci a tare da shi, ba mutum ne wanda za a iya rainawa ba. yana burge ta da yawa, da alama mutumin kirki ne, kuma ma ai shi xin babba ne, ba za ta iya biris da shi ba.
Miqewa ta yi.
“Ya na ga kin miqe?”
“Na gama”.
“Ai cewa ya yi ki jira shi, ko dai ni ne na cika ki da surutu?”
Murmushi kawai ta yi.
“To bari in jira shi”.
Zamanta ya yi daidai da shigowar Principal, “Kada dai kin gama?”
“Eh tun xazu”.
“Okey sannunki”.
Ta yi saurin nufar qofar ficewa.
“Qanwata babu sallama?”
Tsoro ya kamata, ba ta iya cewa komai ba ta yi saurin ficewa.
*** *** ***
“Haba Malam a kan yarinya qarama ka ke neman lahanta rayuwarka? Tunda na shigo ka ke faman xaxxakar sigari, ba ka san wannan hayaqin matsala ne a lafiyarka ba?”
“Faisal zuciyata ta kasa samun nutsuwa, ina ma zan san inda wannan xan iskan ya ke? Ban tava kisa ba,amma da na soma a kansa. Ya zo ya rusa min komai, wani abin takaici wai ba ta sanshi ba ma, ina ga idan tasanshi?”
“Zaruk sam rayuwa ba za ta yi daidai da ita ba, yarinyar da ta ke ‘yar qauye sam ba ta da wayewa, yarinyar da kwalliya ma ba ta dame ta ba, idan ka ce ita ce za ka aura za ka zamo kullum cikin jin kunya, don ba za ta fidda ka jin kunyar abokai ba, tunda ba ka rigaya ka furta mata ba ka nemi Aazeen ita ce daidai da kai”.
“Kana son ka ce in zavi Aazeen ta zamo uwar ‘ya’yana? Anya kana kishina kuwa? Ta ya ya za ka ba ni shawarar haka alhalin ka riga ka san ita xin wace ce? To bari ka ji, ni na tsani mazinaciya, na tsani ‘yar iska. Ba zan tava rayuwa da tantiriyar mace mai wayewa irin Aazeen ba, na fison na auri matar da ba zata zo wucewa wani namiji ya dube ta yana tuna abin da suka aikata da ita ba. Na fi son na auri macen da ko hannunta wani xa namiji bai tava riqewa ba. Na fi son mai nutsuwa da kamun kai irin Nurat, ina ganin ita ce ta fi kowacce mace halin qwarai”.
Faisal baki buxe yake kallonsa cike da mamaki, ya koma ya tuntsire da dariya.
“Oho da kyau, wato kana son ka ce Allah za ka yi ma wayo ko? To bari ka ji, shi Ubangiji ba haka Yake ba, ita xin ta gama kauwama kanta tana tsare mutuncinta, sa’annan sai Ubangiji ya yi mata tukwici da samun miji qasurgumi kamarka? A’a ranka ya daxe ba wannan zancen, lallava kawai ka qarasa rayuwarka da Aazeen xin dai… kai ba ma wannan ba, ita xin Aazeen ta ya ya za ta iya barin ka yi wannan kwamacalar?”
Ya kai ma kafaxar Zaruk duka.
“Ka ga Malam, kawai dai ka sake tunani”.
Da qarfi Zaruk ya daki table xin da ke gabansu har sai da Faisal ya firgita.
“Allah ya tsine ma duk mutumin da ke qoqarin shiga tsakanina da Nurat ko da bai furta ba”.
Ya faxa yana huci da zaro ido.
Faisal ya xaga kafaxa cikin yanayin ko a jikinsa.
“Ni dai na ga ka makance ne shi ya sa nake son dawo da kai kan hanya. Ka gama bin yawon matanka, sannan ka ce kana qyamarsu?” Ya faxa daidai lokacin da Zaruk ya bar gurin.
“Kana tunanin za ka kuvuta daga faxin Ubangiji ne, alhalin har yanzu ba ka tuba ba? kama ta dini tujani”.
Gidan ya cika da ife-ifen Aazeen da qawayenta, gaba xaya suka qanqame ta. Kallo xaya za ka yi mata ka tabbatar tana ji da qawayen nata fiye da yadda Dad xinsu ya sake mata komi na xakinsu an yo musu odar abin da za su dinga ci, an samo ‘yar aiki daga wani hotel wanda za ta dinga kula da abincinsu zuwa lokacin da za su tafi.
Suna zaune a dinning room, hira suke yi na yaushe gamo tare da gaya mata yadda suka yi kewarta. Zainab wadda suke kira Zee ita ce wadda halayyarsu ta zo xaya da Aazeen, tantiriya ce ba a haife ta da xigon kunya ba, ba ta da tsoro, haka ibada ba ta dame ta ba. Ba ta da burin da ya wuce kullum ta ganta ga ta ga namiji.
Sai Mima, ita kuma tana son harkar qawance, tana xaukar kowa da muhimmanci fiye da uwar da ta haife ta, duk rayuwarta tana qarewa a yi ma qawaye hidima. Hakan ne ya sa ta jefa kanta a harkar less.
Sai Tina, ita xin arniya ce, ba ta da addini. Ita kuma sun fi kusanci da Mima saboda kusan harkarsu xaya, don haka ba su tava rabuwa. Minal ita ce mai sauqin hali a cikinsu, ita dai bar ta da shaixanci, ga tsananin yaudara. Kyakkyawa ce ta gaske, kyawunta ya zame mata kadara, iyayenta talakawa ne tuvus, ita ce komai nasu. Kyawunta ke burge Aazeen, don haka ta ja ta jikinta, Minal na da kirki, datausayi. Tanada son taimako, ga ta da shiga rai.
Ammi ta fito daga sashenta cikin nuna farin cikinta.
Minal ta dube ta, “Our Momcy ko?”
Hankalinsu ya karkata gare ta.
Wani irin gaisuwa suke mata, kawai yaqe Ammi ke yi. Cikin nuna musu shariya bata ji daxin mu’amalar yarinyarta dasu ba, shigarsu gaba xaya tamkar ba yaran musulmi ba. Daga gaisuwar nan ci gaba suka yi da harkokinsu. Zee ce ta kunna music a wayarta suka hau rawa daga zaune, Ammi ta kaxa kai kawai ta koma ciki.
Nurat ta shigo sanye dakayan makaranta, ganin fuskar Aazeen a sake ya ba tadamar qarasowa ta tsugunna tana gaida baqi.
“Nurat ce ta girma haka?” Minal ta faxa yayin da ta kai hannu ta xago ta daga tsugunnen.
“Masha Allah, ka ga yadda yarinyar nan ta qara girma, ta yi kyau na ban mamaki”. In ji Mima.
“Zauna mu ci abinci kin ji”.
Gaba xaya Nurat ta gama shige musu rai.
“Qanwata ba kya magana, ko don ba ki sanmu ba”. Zee ta faxa.
“Rabonmu da ganinki tun kina ‘yar mitsitsiya, lokacin da ku ka je da Dad xinku visiting”.
Tina ta karve zancen, “Yanzu ga yadda ta cika har tana son ta fi sister Aazeen nonuwa”.
Aazeen ta xaure fuska tamau cikin duban Nurat, “Ke je ki xaki”.
Sum-sum ta miqe, Mima ta kai mata duka.
“Ji ki da Allah, sai wani muzurai ki ke”.
“Na lura yarinyar akwai ta da kunya”.
Wannan kalmar ce ta tuno mata da layin da Amminsu ta xorata na cewa, in ta bari namiji ya riqe mata hannu za ta samu ciki, gaba xaya suka kwashe da dariya.
“Ki ce an cusa kan yarinya a ta kunta ba za ta ji daxin rayuwarta ba, ita xin zubin hakan ce”. In ji Aazeen.
Suka sake sheqewa da dariya.
“Haka ya fi mata”. Minal ta faxa.
Horn xin motar Alhaji Usman suka ji da gudu, Aazeen ta miqe kanta kan ya fita har ya cimma gurin. Gaba xaya ta qanqame shi, shi kuma sai washe baki yake.
“Baqin namu har sun qaraso kenan?”
“Sannu Dad, da fatan mun same ku lafiya?”
A xaya daga cikin kujerun gurin ya zauna. Hira suke da shi sosai.
“Wai ina Amminku ne?”
Aazeen ta yatsina baki, “Tunda ta leqo suka gaisa ta shige ciki ba ta sake leqowa ba”.
“Bari in qarasa na gani”.
Yana barin gurin suka shiga yaba masa.
Da alama Dad ya fi yi da ke, amma fa ya burge mu, wayayye da shi. Dole ki fantama yarinya, ashe xaurin gindi ki ka samu tun daga tushe?” Zee ta faxa.
Suka saka wani ihun shewa, haxi da tafawa.
*** *** ***
“Ke kullum burinki ki qasqantar da Aazeen, ina amfanin haka? Kun yi baqi kin wani shigo ciki kin kwanta, kina son nuna musu cewar ba ki damu da ita ba kenan ko?”
Banza ta masa tamkar ba da ita yake ba, idanunta a rufe.
‘Na sani kina jina, da ke fa nake”.
Ganin ta qi motsawa ya daka mata duka.
Ta buxe ido a qufule.
“Ina magana kin maishe ni sha-ka-tafi, wai shin ba baqi ku ka yi ba ne?”
Ta miqe zaune.
“Kana son ne in je na zauna a cikinsu kamar yadda kai xin ka yi?”
Ya saki baki yana kallonta.
“Kada dai a ce kishi ki ke yi da ‘ya’yan cikinki?”
“Uhum, Yallavai kenan. Ashe da na daxe da qarewa, ai ni inda sabo na saba da irin haka, ina da aikin yi”.
Ta miqe za ta barshi a gurin. Ya wani figo ta ta zube a qasa.
“Ni za ki raina wa hankali, ina magana za ki fita? Yaushe ki ka dawo haka?”
“Komai koya xan Adam yake yi”.
Mamaki ya sake kashe shi, yana ji kamar ba Rahmarsa ba ce.
“Ni ki ke gaya ma magana?”
Ta tave baki, kallonsa ta ke a tsakiyar ido, babu shakka a tare da ita.
“Kana mamaki ko? Muddin waxannan qananun ‘yan barikin ba su bar gidan nan yau ba, zan ba ka mamaki”.
Yadda ta yi xin ya xaga masa hankali, ya kasa zaune ya kasa tsaye.
*💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞*
*NA*
*BILKISU H.MUHAMMAD*
_(Matar Auwalu By fos zage)_
*Free page 13*
*_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_*