Sashe 26
Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*** *** *** Alhaji Usman ya shigo gidan cike da farin ciki. “Daddy ta samu kenan?” “Rangida ina cike da farin ciki, burina kullum zumuncinmu ya xore da Alhaji Aminu. Yanzu kam za mu zama xaya, don ko har zuri’a za mu haxa, kin ga kenan zai sake sakin jiki, babu maganar qyashi a tsakaninmu”. Hankalin Ammi ya tattara a kansa, tana son jin inda ya dosa. “Daddy ka vatar da ni, sam ban gane ba”. Ya numfasa, “Ina Nurat?” “Tunda muka dawo ta ke kwance”. Aazeen ta faxa. “To lafiya kuwa?” “Kanta ne ke ciwo, amma ta sha magani tun a gidan su Zaruk”. “Ok, to shi ke nan Allah ya sauwaqe”. “Dad ina jinka”. “Mutuminki Zaruk ashe duk wannan abin wai Nurat yake so?” Aazeen ta yi tsalle ta dire, har tana guxa. “Dad dole ka yi farin ciki”. “Allah dai ya sa Nurat ta amince da shi”. Ammi ta faxa tana kawar da kai. “Duk wani abu da na tsara a gidan nan ke ce ke rusawa, an gaya miki ina son jin ra’ayinta ne? to bari ki ji, ko tana so ko ba ta so Zaruk shi ne mijinta. Ni ne na haifi Nurat ba ita ta haife ni ba, ina da ikon ba ta duk wanda na yi ra’ayi kin gane?” Ya tashi ya shige sashensa ransa a matuqar vace. Duk jikinta ya yi sanyi, ta yi da ta sanin ba ta yi magana ba. “Ammi, Daddy yana da gaskiya fa. Ai ita Nurat ba ta da wani ra’ayi, kawai ki sanya masa ido, don ni ban ga aibun Yaya Zaruk ba, sai dai in ke xin ce ba kya son ta aure shi’. Ita ma ficewa ta yi ta barta zaune a gurin qiqam kamar an dasa ta. Tun daga farko har qarshe Nurat ta ji hirar tasu. Kifa kai ta yi a filo tana faman gursheqen kuka. A haka Ammi ta riske ta, zama ta yi a gefenta, ta ma rasa ta ina za ta fara. Ita kanta ba ta so hakan ba, ba wai don ba ta qaunar aurensu ba, sai dai tana ganin nawa Nurat xin ta ke da za a yi zancen aurar da ita yanzu? Ban da ma ta fara makaranta da wuri bai fi a ce tana J.S 3 ba. Hannu ta sa tana shafa bayanta. “Me ye na kuka Nurat? Fata za mu yi Allah ya sa haka ne ya fi alkhairi. Shi xin mutumin kirki ne, Yaya yake a gare ki”. Ta xago kai idanunta na tsiyayar da qwalla. “Ammi ki taimake ni, wallahi bana son auren nan. Ammi, Dad har ya gaji da ni ne da zai aurar da ni? Me ya sa ba za a yi wa Yaya Aazeen ba? ta fi ni girma, ta gama karatu. Ta fi ni cancanta, don Allah ki taimake ni ki fahimtar da shi”. Ta kai hannu tana share mata qwallan. “Shi ke nan, zan yi hakan. Amma sai na ga kin cire damuwa a ranki kin ji. Yanzu tashi ki je ki yi wanka ki ci abinci”. Ta miqe ta yi waje, Ammi ta bi ta da kallo, gaba xaya tausayinta ta ke ji. Babu kunya ya saka wa Abbansa rigimar ba zai iya jira zuwa wani lokaci ba. Alhaji Aminu mamakin Zaruk yake yi. “Ka shaida mini tun tana qanqanuwarta ka ke sonta, ka duba ka ga shekarun da ka xiba, don ka jira shekara xaya ai ba zai cutar da kai da komai ba…” “Abbana ba zan iya ba. ina sonta kamar raina, ba zan iya ba. Ji nake kamar zan mace, Dad ina son na yi rayuwa da ita kafin in mutu. Don Allah ka saka baki na sani muddin ka ce ba ka amince ta qarasa karatunta a gidansu ba zai amince. Abba kai ne fa komai nasa, da taimakonka yake samun komai’. Xaga masa hannu ya yi. “Kada in sake jin makamancin wannan zancen a bakinka”. “To Dad na ji, ba zan sake ba. amma ka duba, na amince ta qarasa karatun a gidana”. “Oh God, shin Zaruk ba ka san a gaban wa ka ke magana ba? ina kunyarka ta ke ne? ni ba zan yi musu dole ba, idan auren ka matsu da shi ka nemi wata cikin sati biyu zan aura maka ita. Amma ba za ka sanya ni in takura bayin Allah a kan son ranka ba”. Ya miqe a fusace ya yi waje. Zaruk ya miqe ya shiga sintiri, wani irin son Nurat na ratsa dukkan sassan jikinsa. Fuu! Ya yi waje da nufin ya koma gurin Abban nasa ya sanya masa kuka, qila ya gane abin da yake ji. Sai dai yana sa kai ya ji tashin motarsa, ya juya a zabure zai koma ciki suka yi arba da Ummansa. Kallonsa ta ke a tsorace. “Ciwon ne ya motsa?” “Umma, Abba ne, ba ya son farin cikina”. Kamo hannunshi ta yi, ba su zame ko’ina ba sai sitroom,. Ta zaunar da shi a kan kujera, ta soma magana cikin kafe shi da ido. “Tunda ka furta kana son Nurat, ba ta da miji sai kai. Me ya sa ba za ka kwantar da hankalinka ba?” “Oh Umma, me ya sa ba kwa ganewa? Nurat mace ce, kuma mai matuqar kyau. Tana da xabi’u masu kyau, a yanzu haka tana da masu sonta da yawa, wataran za su hure mata kunne, za ta juya min baya… Umma ta ma fara yanzu haka Nurat ta daina kula ni, ba ta son ganina. Ina ganin qiyayyata kwance a fuskarta…” “Ka ga Zaruk, kai ma ka riga ka sani aurenka da ita tilas ne, ko da tana so ko ba ta so. Na sani mahaifinka ya fi ka son wannan auren shi ya sa nake son ka nutsu”. “Zan yi haka, amman sai dai ta dawo gidan nan, inyaso ni sai na dinga kai ta makaranta”. “Haba Zaruk, ina ka tava ganin an yi haka? Gaskiya ba zai yiwu ba”. Ya miqe a fusace. “Umma, ke ma ba za ki fahimce ni ba ko? Shi ke nan”. Ya juya ya koma ciki. Aazeen tunda ake wannan abu ba ta xora ido a kan Nurat ba, kwana uku kenan ba ta zama a gida saboda binciken inda za ta samu Ahmad Deedat. Kuxi ta ke ta faman kashewa har da masu bincike a yanar gizo, wasu ma qarya suke yi mata da cewar sun sanshi don kawai su karvi kuxi. Duk kuxin kuma da ta ke kashewa ko a jikinta, kullum gani ta ke yi wataran za ta fanshe, ba ta fidda tsammanin cewar shi xin zai zamo nata ba. Yau qarfe huxu ta dawo gida, kai tsaye ta faxa bathroom ta yi wanka, riga da wando ta saka marasa nauyi, ta miqe a kan gado, ta janyo waya. Wasu rubutukan batsa ta ke karantawa, lokaci xaya ta ji kewar Zaruk, tunda ya qwallafa rikicin son Nurat ba shi da lokacinta, ita xin in ba shi ba ba ta tava ganewa, ya xora ta a kan salon da ba ta iya haqurcewa da shi, dole ne ta yi wani abu a kan lamarin nan ko don ya samu nutsuwa. Za ta je ta samu Nurat, za ta yi mata wayo. Ta shigo xakin, a bakin gado ta same ta a zaune tana ta fushi. Ta zo ta zauna a kusa da ita ta sa hannu ta kamo nata, ta kira sunanta. Ba ta amsa ba sai ma kawar da fuska da ta yi, ta soma magana. “Qanwata kin ba ni kunya, anya kuwa Nurat xina ce kuwa? Ni dai na san tawa Nurat xin mai biyayya ba ta tsallake abin da family xinta suka gindaya mata, amma yanzu duk ta sauya, me ya sa?” Ta saki hannun nata ta kamo havarta. “Gaya min ko akwai wani a cikin zuciyarki?” Da sauri Nurat ta kaxa kai, da ido taf qwalla. “Kullum kina yi min wa’azi ta ya ya mai dokar bacci zai vuge da gyangyaxi? Kin ga ke fa saukakkiya ce ga hadda a kanki, duk wasu littattafan addini suna kanki, kin kuma san hukuncin mutumin da bai bi iyayenshi ba, kin san irinku Allah ya fi kama ku da hujja”. Wasu siraran hawaye suka biyo kuncinta, lallai wannan ‘yar rainin hankali ce. Ta faxa a ranta. “Ni bana sonsa. Ban tava sonsa ba”. Ta kai hannu fuskarta tana share mata qwalla. “Kin ga in dai wannan ne ta zo gidan sauqi. Ke da ma ba ki san me ye so ba? Babu kowa a zuciyarki, zai koya miki yadda za ki so shi kin ji”. Ta kama kumatunta ta ja. “Yauwa qanwata, small”. Maimakon murmushin sai ta rushe da wani sabon kukan, cikin shesshekar kuka, “Yaya Aazeen ai kin fi ni buqatar aure, amma ni me na yi wa Dad da yake son xauke ni a gidan nan? Ni ba zan iya ba”. “Ni ma ina son ki yi aure ba Dad kaxai ba Nurat, ina qaunarki, ina tsoro kada ki riski kanki a rayuwa irin wadda nake ciki. Yadda Ammi ta ba ki tarbiyya ina son ki xora duk inda ki ka shiga a yi alfahari da ke…” “Yaya shi xin ai ba na gari ba ne”. Ta katse ta da faxin haka. “Wa ya gaya miki?” Ta tambaya cikin faxuwar gaba. Shiru Nurat ta yi. “Ni kam ban ga aibunsa ba, Zaruk xan asali, ga shi mai kyau. Za ki yi alfahari da shi”. Zumbur ta miqe tsaye. “Da an yi magana ki ce kyau, shi kyau ba abu ne mai xorewa ba, ai ba a tava gama wa xan Adam halitta har sai ya koma ga Ubangijinsa. Halayyar Yaya Zaruk nan gaba zai iya tsintarsa a kowane yanayi, ina da yaqini Allah ba zai xora qaddarar aurensa ba domin an tsarkake kaina”. Ya dace a ce Aazeen ta gano inda Nurat ta dosa a maganganunta, sai dai ba ta gane komai ba. Miqewa ta yi. “Shi ke nan, ni ma idan ki ka amince da Zaruk zai auri wannan Adamun zan yi duk yadda ki ke so, me ki ka ce? Ba kin ce kin yi masa alqawari ba?” A hankali ta jinjina kai. “Zauna, kirawo min shi, ina son ya zo in ganshi”. Ta dube ta don