← Book details Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 28

Sashe 20

Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*** *** ***
“Ba wani yanayi a soyayya, so kamar rayuwa ne, ba kowane lokaci ba ne ake samun sauqi kuma ba kowane lokaci ake samun farin ciki ba. Ya kamata ka koyi sona, tunda ina nan a raye bana jin zan iya rabuwa da kai Yaya Deedat. Kai ne numfashina na sani ba wata damuwa ka yi da ni ba, da zan iya da tuni na cire ka a raina. Sai dai ina ji a jikina wataran za ka so ni, zan iya jure komai a kanka. Na amince zan rayu da kai a ba ka sona xin”.
Kalamanta sun karyar masa da zuciya. Duk sai ta ba shi tausayi.
“Nabila ban ce bana sonki ba, xabi’unki kawai za ki sauya”.
“To ka gaya min, me ye aibuna? Me nake yi wanda ba daidai ba?”
Ya ja wani xan qaramin tsaki, matsalarta kenan ba ta amince da ba ta yin daidai, xabi’unta tana xaukarsu abin burgewa.
“To shi kenan, tunda kina ganin komai daidai ne babu matsala, yanzu ki gaya ma su Papa, wata biyu na xiba”.
Ta yi sororo.
“Yaya Deedat, wata biyu ba ma sati biyu ba?”
Ya ce, “Akwai tafiyar da zan yi, zan kai kusan hakan idan na dawo sai a yi bikin. Ni zan wuce”.
Ta matso kusa da shi, matsalarsa kenan, sam bai iya soyayya ba, yadda ka san mutumin da.
“Yaya Deedat shin ba ka xokina ne? Ya kamata a yi bikin nan kafin ka tafi inyaso sai mu tafi tare, please”.
“Ba zai yiwu ba, idan hakan bai yi miki ba kin iya neman wani”.
‘Uhm Yaya Deedat, ka sani ba ni da mijin da ya wuce ka. Ina son ka sani ko da za ka kai shekaru goma ina nan daram babu inda zan xaga, kawai dai ka sa a ranka duk bala’i ba ka da matar da ta wuce ni”.
Ya yi wani murmushi mai ciwo.
“Allah ko? To sai ki ci gaba da jira”.
Murmushi ta yi, ta sani gaba xaya Deedat ba ya sonta, bai tsara rayuwarsa da ita ba, kuma dole ne ya aure ta, ba za ta bari wata shegiya ta rave shi ba, ba ta fatan ganinshi da wata ko da ba shi da komai, ballantana hamshaqi kamarsa, ko za ta mutu babu aure za ta jira shi. Ta sani haramtaccen abu ne ya yi aure ba tare da ya aure ta ba. Ta sani dama yake nema da zarar ta ji haushi ta ce za ta auri wani zai auri wadda yake so, don haka za ta jira shi.
Ta qarasa gabanshi inda suke iya jin hucin juna.
‘Zan jira ka ko da hakan zai kai mu da tsofewa, na yi alqawari ba ni da miji face kai, in ka je ka yi shekara ba ka dawo ba Mr. Man”.
Ta yi murmushi, a gurin ta barshi.
Takaici kamar zai rufe ta da duka.
“Dole ne fa ka yi yadda iyayenka ke so, kai ma ka sani tuntuni ita xin zamanka ta ke yi, ba ka da hujjar da za ka guje mata”.
“Mtss! Salim ka sani bai tava sonta ba, ta ya ya zaman aure ya yiwu a haka?”
“Nawa aka yi Yaya? Iyayenmu na da suka yi ba su tava zaven mace a kan kansu ba, kai wasu ma ba za su tava sanin wace matarsu ba sai ranar da suka tare”.
‘Ok, na ji wannan, amma kuma ba ka tunanin ita xin Nabila wace ce ita ba?”
“Wannan ba hujja ba ce, a koyaushe xan Adam na iya sauyawa, ballantana Nabila wadda da zarar ka aure ta soyayyarka na iya sauya ta, in fa ka aure ta za ku kasance ne tare, in ma ba ku kasance tare ba kana datse ta a gida zama za ta yi”.
Deedat ya furzar da wani huci mai zafi, kalaman Salim ba su zame masa hujja ba. ya sani babu wanda zai iya fahimtarsa, babu wanda zai hangi abin da shi yake hange.
“Kawai ka lallava ku rabu da Ummi lafiya”. Salim ya katse shi da faxin haka.
Bai dai ce masa komai ba, ya soko wata maganar, ba ya son ci gaba da maganar Nabila.
Gaba xaya rayuwar gidan ta sauya, gida ya koma tamkar ba na musulmi ba, kixe-kixe da raye-raye shi ne abin yi. A kullum cikin kawo maza suke, da Hajiya Rahma ta yi magana sai Aazeen ta ce abokansu ne daga ofis xinta, tana tsoro, don haka kusan kullum ta ke nemar wa Nurat inda za ta tura ta ta wuni. Tana jin tsoron kada idanunta su dinga ganin irin waxannan abubuwan.
Haka a wannan lokacin ta qara qaimi gurin kai kukanta ga Ubangiji a kan Aazeen, babu abin da ba ta ayyanawa a kan Aazeen. Tuni ta gama sallama cewar ita xin tana bin maza ne, don haka ma babu aure a gabanta. Yau kam ta gama kai wa qololuwa, ko qawayenta ko ita ba za ta ci gaba da zama da su ba alhalin ba su da niyyar komawa, sun ma miqe qafa, don haka ko da ya dawo ba ta doshi turakarsa ba, ba ta kuma kai mishi abinci ba.
Ya dinga kiranta a waya ta yi biris! Ya turo text nan ma babu amsa. Ya qulu sosai har wani huci ya dinga yi. A zafafe ya miqe ya nufi shashinta, ya afka ciki. Tana zaune a kan sallaya yana huci.
“Ban san sa’adda raini ya shiga tsakanina da ke ba, ina so ki sani ba zan xauki wannan wulaqancin ba, ba zan tava ba. In ban da rashin mutunci ta ya za a yi in dawo ban tarar da abinci ba, in kira wayarki ki qi xauka, wannan ai iskanci ne”.
Har ta shafa addu’a ta cire hijabi tare da ninke darduma ta ajiye a gefe, ta koma bakin gado ta zauna ba tare da ta tanka mishi ba, hakan ya sake qular da shi, hannu ya xaga ya kifa mata mari.
Dafe da kunci ta dube shi da ido fal qwalla.
*💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞*

*NA*

*BILKISU H.MUHAMMAD*
_(Matar Auwalu By fos zage)_

*Free page 14*

*_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_*

*Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa*

*1. IZZATU*
*2. MULKIN MALLAKA*
*3. KAUNA CE*
*4. DACEWA*
*5. RASHIN RABO*
*6.TARAIRAYA*
*7. JINI BIYU*
*8. AKWAI BAMBANCI*
*9. TSALAR KAUNA*
*10. YA YI SAKE*
*11. ILLAR SABO*
*12. SO DA SANKARA*
*13. RASHIN RABO*
*14. WATA RAYUWA*
*15. HUBBAN SHADIDAN*
*16. BAKIN K'AZAFI*
*17. MATSALAR KAUNA*
*18. KYAN KUSKURE*
*19. WA YAFI SONTA?*
*20. GABA DA SO*

_NOW_
*KYAUTA ZUCIYA*

```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah```

*_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_*
*_2277439558 UBA Bank_*
Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
Chapter 20 · 0% Book details