← Book details Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 28

Sashe 21

Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

*D* afe da kunci ta dube shi da ido fal qwalla.
“A kan me za ka mare ni?”
Ya sake xaga hannu zai qara mata, ta yi saurin kaucewa ta dube shi a tsakiyar ido, yayin da qwalla ta gama lulluve mata ido.
“Akwai Allah”.
Ya bi ta ya shaqo ta.
“Ki gaya min abin da ki ke nufi”.
‘Ni ka cika ni na ce”.
Ta daddage ta qwaci kanta da qyar tana haki.
“Wallahi muddin waxannan yaran ba su bar gidan nan ba, ba za mu tava zama lafiya ba”.
‘Zancen banza, an gaya miki su irinki ne? su xin suna da gurin zuwa, ke kam idan na kora ki ba ki da gurin zuwa, su da gatansu, ke ko fa? Ba ki da gatan, ke xin korarriya ce, mujiya ce wadda ki ke da danvareren tabo har a gurin Allah, ke xin…”
“Ya isa! Ya ishe ka haka! Ka fara tunanin makomarka kafin ka hangi tawa. Wannan fuffukar da ka ke yi a da kenan, yanzu kar nake kallonka, na san ta yadda zan bi in wanke kaina. Na san yadda zan yi shari’a ta xaure ka, ita xin kanta na san yadda zan bi ta dinga ganin baqinka saboda ni ce mahaifiyarta. Sanin kanka ne uwa ta fi uba soyuwa a gurin zuciyar yaransu”.
Ya saki wata dariyar takaici.
“Ni a gurina Aazeen na yi nisa! Yadda nake da Aazeen ko cewa na yi ta kashe ki na yi imanin za ta bi umarnina, kuma wallahi idan ba ki bi a sannu ba sai kin yi kuka da idanunki, sai kin zamo qasqantacciya a gurin yaranki. Sai na yi miki lambar da za ki zame musu tamkar java, mara mutuncin banza. Qarqari kuma ki ce ba za ki ba ni abin da nake so daga gare ki ba, ki je ki riqe, kawai ina zuwa ne saboda in fita haqqinki, abin naki da kike rowarsa ba ya qara ta da komai, kawai maleji nake”.
Ya yi waje, ya rufe qofar da qarfi har sai da ta firgita.
“Wayyo Allah, na shiga uku!”
Ta zube a qasa tana wani irin kuka.
‘Ni na ja wa kaina, kaico! Na sani hakan za ta faru. Usman tuntuni na gama sanin waye kai, sai dai soyayyarka ce ta makantar da ni. Usman ban tava ganin mara imani irinka ba, Ubangiji ka kashe ni in har mutuwa ta za ta zamo alheri a gare ni”.
Wunin ranar ba ta iya fita ko da sitroom ba. A haka Aazeen ta riske ta, hankalinta ya yi matuqar tashi, duk shaixancinta tana son mahaifiyarta, ba ta son abin da zai xaga mata hankali. Da gudu ta tsugunna a gabanta.
“Ammina, waye ya tava ki? Ammi kalli yadda ki ka komo wuni xaya, gaya min, Dad ne ko?”
Ta kaxa kai.
“To me ke damunki? Don Allah ki faxa min kin ji”.
“Na ce da ke babu komai, kawai kaina ne ke yi min ciwo”.
“No Ammi, ban amince ba, tunda qawayena suka zo ki ka kasa sukuni. Za su tafi, zan sallame su, ko kuma na maida su hotel, hakan ya yi miki?”
Ba ta kula ta ba, kawai binta ta ke yi da ido har ta gama surutunta ta fice, tsananin tausayinta ta ke ji.
Ta gama ba su labarin abin da ta fahimta ga Amminta.
“Tab! Lallai Ammi tana da matsala”. In ji Tina.
“To ai shi ke nan, sai ki yi irin rayuwar da ta ke so xin, saboda na ga kamar kin shiga damuwa”.
Zee ta karvi zancen, “Yanzu ke hakan ne zai sauya ki? Kin ga Hajiyata kawai injoy your life”.
Mima ta ce, “Ita wannan Ammin a haka kamar wayayyiya. Duk ta maida kanta wata ‘yarqauye, ba ta da aiki sai riqe carbi, ga kyakkyawar qanwarki na qoqarin kwaikwayarta, qauyancinta ya sanya an kasa gane ita xin mai kyau ce. Wai shin ma idan ba ki more rayuwarki a lokacin quruciya ba, yaushe ake son ki more shi? Sai lokaci da ta zamo yagwalgwal?” In ji Zee.
Gaba xaya suka xau shewa.
“Kun ga ku daina wannan zancen kuna kada min da gaba, babu abin da na tsana irin in ji an ambaci tsufa, a hakan ma nauyin shekaruna na ke ji, don haka nake roqon in mutu kafin tsufa”.
“Shi ne aminiyas, kawai ki huta”. Minal ta ce da ita.
“Amman da har Ammi na son karya min zuciya, na ji tausayinta yau”.
“Okey, shi kenan sai ki koma zumbula hijbi, riqe carbi, zama a kan darduma takura kai”.
Suka sake kwashewa da dariya.
“A duk lokacin da ta sanya karatun alqur’ani na kan ji duk na takura”. Tina ta faxa, “Ban sakewa wallahi. Ki yi mata magana”.
‘No Tina, don’t cross your limit. Ki rufe bakinki haka kada ki wuce gona da iri”. Minal ta katse ta da faxin haka.
Tuni ta shiga taitayinta.
Chapter 21 · 0% Book details