Sashe 24
Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
*** *** ***
“Sam-sam sonka ne ba ta yi, ta gane inda ka dosa shi ya sa ta xauki wannan matakin”.
“Ba zai tava yiwuwa ba akwai alaqa mai qarfi tsakanina mahaifina da nata, in na ga dama sai dai kawai ta ga an xaura aure. To amma don in fita haqqinta ne ya sanya na shaida mata. Amma ita xin ma…”
“Zaruk kenan, kada ka mance kamar yadda Dad ke qaunarka ita ma haka nata ke qaunarta. Ina ba ka shawara in ka ga ba ta ra’ayinka ka haqura ga mata nan da yawa?”
“Matar Yaya idan na qyale ta mutuwa zan yi, ni kaina ban san yadda nake sonta ba, wallahi dole sai na aure ta duk bala’i sai na mallake ta”.
“Uhum Zaruk kenan, shi kenan Allah ya ba ka sa’a, Ubangiji ya zava mana abin da ya fi alkhairi”.
“Daga baya kenan, ni kam ko babu alkhairin zan aure ta, sai fa na auri Nurat. Shekara kusan goma ina gadinta, lokaci xaya na faxo? Ina! Allah ba zai xora mini wannan ba, ba zai tava xora min ba’.
“Shi ke nan”.
A can bedroom xinsa sambatu ya yi ta yi tamkar mahaukaci. Ya sha sigari babu adadi duk ba ta gamshe shi ba, ya buxe firij ya xauki kwalbar giyar da rabonshi da ya sha ya fi wata uku, tun lokacin da ya yi ma Dad xinshi alqawari, bai ma san akwai ragowa a firij xin ba sai da ya hange ta.
Kafa kai ya yi bai sauke kwalbar ba sai da ya ga babu komai a ciki, ya kwanta rigingine, Nurat ce ke masa gizo. Ya miqe tsaye yana sanxa wai zai kamo ta. Haka ya yi ta yi, daga qarshe ya yi wani irin wawar faxuwa, har sai da ya faxa kan kwalbar ta fashe ta yi masa wata muguwar yanka a gefen fuska da qirji, jini ya valle.
Daidai lokacin Alhaji Aminu ya turo qofa, duk warin giya ya cika xakin, ga xansa kwance cikin jini yana faman amai. A sukwane ya qarasa gare shi ya janyo shi kan cinya yana jijjiga shi. Sunan Nurat kawai yake faman kira, a ruxe ya kira likitansa a waya tare da yi mishi bayanin abin da ke faruwa.
“Zaruk ashe qarya ka yi min, da man yaudara ta ka yi ka ce ka daina? Me ya sa?”
Qoqarin qwacewa ya dinga yi daga jikinsa yana kiran sunan Nurat.
Kuka Alhaji Aminu ya saka, yadda ya ga jini ya tsananta zuba. Likita ne ya turo qofa. Shi kanshi hankalinsa ya tashi.
Ya dubi Alhaji Aminu, “Garin ya ya hakan ta faru?”
“Ban sani ba, kawai na xai ji yana ta ambatar wata Nurat”.
Likita ya sauke ajiyar zuciya.
“Ko wacce tana da alaqa da shigarsa wannan yanayin”.
Allura ya yi masa ya yi dressing xin raunikan, ya kuma xora masa da allurar bacci, kafin wani lokaci bacci mai qarfi ya yi awon gaba da shi”.
Hajiya Amina da Maryam sun dawo daga gidan suna, suka riski mummunan labari.
“Da na san abin da zai aikata ma kansa da ban barshi shi kaxai ba”.
A nan ta kwashe labarin komai ta shaida musu.
“Ban da abin Zaruk ya sani dole ma ya aure ta ko da ba ta so, da ita da Baban nata duk a hannun Alhajina suke shi ne fa qarfin arziqin ba ko wannan uwar girman kai ya ce yana so dole ne ta amince, balle ita Nurat baiwar Allah, yarinyar da babu sa wa ba fitarwa”.
Yana zaune a tsakiyar gado ko a jikinsa halin da ya ganshi a ciki, ya sani hakan zai xaga ma Dad hankali, ba zai bari ya rasa Nurat ba, sigarinsa ma ya ke faman zuqa.
Hajiya Amina da Alhaji Aminu suka shigo xakin daidai lokacin wutar sigarin ta cimma hannunsa. Da gudu Alhaji Aminu ya zare tabar a hannunsa ya cillar a qasa haxi da mitsike ta a qasa. Suka zauna a gefe, gaba xaya yanayinsa ya nuna yana cikin damuwa, ya yi ramar wuni xaya.
Ya raunana murya, “Haba Zaruk har kana da damuwar da ka ke tunanin ba zan iya magance maka ba? Maryam ta gaya min komai kai ma da gangan ka tada hankali, ka sani ni da Alhaji Usman mun zamo xaya babu abin da ba zai iya mallaka min ba”.
“Daddy, Nurat ba za ta so ni ba, ta daina kula ni, ba zan iya rayuwa babu ita ba, ina tsananin sonta, da ita kaxai nake son rayuwa, ka taimaka kada ta guje mini”.
“Ya isa haka, na ji za ka auri Nurat, amma sai in na ga ka raba kanka da waxannan mugayen xabi’un, domin babu uban da zai so ka zama surikinsa in har ba ka daina ba, zan fita a harkarka…”
“Ban da ma abin Zaruk, ai ita xin taka ce, ko da ba ta so dole ma ta so ka, ka kwantar da hankalinka in ba haka ba za ka kashe rayuwarka a banza, kana ji kana gani wani nan zai aure ta”.
“Mommy na yi muku alqawarin na daina har abada, ku yi haquri”.
Suna zaune a falo dukkansu, kallon suke yi, hankalin Alhaji Usman ya karkata ga Nuratm ya fahimci kamar akwai abin da ke damunta. Kallon ta ke yi amma tunaninta na wani guri.
“Nurat wai me yake damunki?”
Ta tilasta wa kanta sakin murmushi, wato yaqe.
“Dad me ka gani? Lafiya ta qalau”.
“Tunda na dawo na ganta a haka, na tambaya ta ce kanta ne ke ciwo”. Hajiya rahma ta faxa.
“Ai na sha magani, ya daina ciwo”.
Aazeen ta xan dube ta, ta kawar da kai, don idan tana kallon program xin Ahmad ba ta son abin da zai katse ta, tana tunanin kamar za ta samu hasken inda za ta same shi.
Wayar Alhaji Usman ta shiga ruri, ya xaga.
‘Subhanallahi, yaushe? Okey za mu shigo gobe, Allah ya ba shi lafiya”.
Gaba xaya hankalinsu ya koma kansa. Ya ajiye wayar cikin dubansu.
“Lafiya kuwa?” Hajiya Rahma ta tambaya.
“Wai Zaruk ne ya yi hatsari”.
Aazeen ta ji wani shook, “Daddy xazun fa ya bar gidan nan?”
Ta iya yuwuwa ko a hanyar komawarsa ne ya gamu da tsautsayi”.
Duk ta gigice.
“Dad yana asibiti ne?”
“A’a yana gida”.
“Allah Sarki Zaruk”.
Ta wutsiyar ido Nurat ke duban Aazeen, ji ta ke yi kamar ta shaqe ta, ta ja tsaki a zuciyarta, dole ta damu tunda abokin fasiqancinta ne.
‘Idan Allah ya kai mu gobe, sai ku je gaba xaya”.
“Ni dai ba za ni ba, gobe wuni za mu yi a school”.
“Qarya ki ke yi, ba ki isa ba, wallahi sai kin je, mara mutunci”.
Yadda ta hayayyaqo mata ne ya sanya ta tsuke baki.