Sashe 27
Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
gaskata abin da ta ke faxi. “Yayata da gaske ki ke yi?” “Mamaki zan ba ki. Zan yi komai don xorar da farin cikin qanwata”. Take suka shiga kiran layinsa, sai dai an yi rashin sa’a wayar tasa na kashe. Daxi ne ya kama Nurat, a tunaninta wayo za ta yi wa Aazeen, ta sani in ta ganshi za ta iya sonsa, yayin da ita ma Aazeen ke murmushin mugunta, tana jin cewar dabararta ta yi. Sun tsayar cewar duk lokacin da ya kunna wayarsa za su kira shi. Hankalin Alhaji Usman ya kai qololuwa gurin tashi a kan abin da Alhaji Aminu ya zo masa da shi a kan Nurat, ya sani rashin amincewarsa zai iya haifar da komai, yana tausayin Nurat, ya sani kawai son rai zai nuna, bai dace a ce ya aurar da ita nan kusa ba. Alhaji Aminu yana da kirki, ya taka rawar gani a rayuwarsa, shi ne ya koya mishi yadda zai dinga juya kuxi, shi ya fito da shi a idon duniya har aka sanshi. Alhaji Aminu ya fi qarfin komai a gurinsa, akwai kunya in har ya juya wa buqatarsa baya, ya yi masa halacci da yawa. Yanzu ne lokacin da ya kamata ya rama masa, don haka ya qudiri niyar kyautatawa Nurat ko don ya shawo kanta, don haka yau bai dawo gida ba sai da ya yi mata siyayyar kayan kwalliya, kayan sawa har da sabuwar waya. Lokacin da Hajiya Rahma ta shigo xakin, ya lura da yadda ta rame, tausayinta ya kama shi. Ya kai hannu ya janyo ta jikinsa, yana son Rahma tamkar ransa, in ban da fitina irin ta zamani mutumin da yake da kamar Rahma ya gama samun arziqin duniya, sautari in yana baqanta mata rai ya kan ji ya tsani kansa. Ta nuna mishi qololuwar so, ta rabu da komai da kowa saboda shi. Me ya sa shaixan ke hilatarsa haka? Sakin baki ta yi tana dubansa, ya xan numfasa, idanunsa a kanta. “Kin tsane ni ko?” Da sauri ta kaxa kai. “Me ya sa zan tsani mijina uban yarana?” Ya sauke ajiyar zuciya. “Na sani ban kyauta muku ba ke da Nurat, ni kaina na shiga tsaka mai wuya ne, babu abin da Alhaji Usman zai iya nema in hana shi, idan na juya mishi baya ma duniya za ta zage ni, danginsa za su yi mishi dariya. Kuma ni ban ga aibun shi Zaruk xin ba”. Idanunta fal qwalla. “Ai ni ban ce komai ba, Nurat ‘yarka ce, ka fi kowa iko da ita. Ina fatan Allah ya sa haka ne ya fi alheri”. Ya sake shiga jikinta yana zargin kansa da abubuwa da dama. “Yauwa Rahmar Allah, haka nake so. Yanzu ki turo min ita”. Ta miqe jiki a sanyaye, yadda ta samu suna hira da Aazeen har da dariya ya sanya ta xan ji sanyi a ranta. “Alhaji na kiranki”. Ta ce da ita. Tunda ta zauna yake ta rarrashi, amma zuciyar nan tamkar rodi, musamman da ta fahimci yadda yake qoqarin sai ya cusa mata son Zaruk ta qarfin tsiya. Ta yadda yake ta faman yabon Zaruk, yana kururuta dacen da ta yi, da faxin jaruntarsa, son mutanensa ga addini da taimakon marasa qarfi. Ya xora da cewar, “Ki fidda ni kunya, ban tava neman abu a gurinki ba Nurat, yau na zo da qoqon barata, kada ki zubar min da mutuncina, ki rufa min asiri”. Ba ta ji daxin yadda Dad ke roqonta ba, tamkar zai yi kuka. “Dad na amince, na yarda Dad. Ka daina roqona, kai mahaifina ne, za ka iya yin duk yadda ka so da ni. Zan aure shi ka bada aurena a duk lokacin da ka so, ba zan musa ba”. Daxi ya kama shi, ya sani an wuce gurin, ya gama sanin ‘yarsa kaifi xaya ce ba ta magana biyu, yadda ka san babbar mace. Yaqe ta ke yi yadda ta ga mahaifin nata na ta rawar jiki, yadda ya nuna farin cikinsa idanunta ke qoqarin zubda qwalla. Cikin dabara ta goge su ta sani zai iya tilasta mata ta aure shi, amma ba za a tilasta mata ta so shi ba. shi kenan ba ita babu wani farin ciki a duniyar nan? Ta katse tunaninta a daidai lokacin da ya nuna mata kayayyakin da ya siya mata. Ya xauko waya ya miqa mata, da cajinta full har ma an xora layi a kai. Yadda ya santa da son waya tun tana qaramarta, ya yi zaton za ta nuna farin ciki, karva kawai ta yi kamar ba ta so, haka ne ya tabbatar masa cewar ba ta son Zaruk. “Na saka miki lambata da ta Amminku, ki tashi ki je, Allah ya yi miki albarka”. Ta kwashi kayan ta yi waje.