Sashe 25
Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
*** *** ***
Alhaji Usman ya nuna farin cikinsa sosai, “Ban da abinka Alhaji Aminu, kai fa me iya xaukar Nurat ne ka bada aurenta, ballantana yarona ne mai sonta”.
“Eh na na sani, amma duk da haka ina son ka ji ra’ayin Nurat”.
“Kada ka damu, ban da lalacewar zamani, auren fari iyaye ne ke sama wa ‘yarsu miji. In dai Nurat ce kada ya damu an gama, kawai bari zai yi ta qarasa karatu, lokacin ta qara tasawa, don ita xin har yanzu akwai quruciya a tattare da ita, shekara sha shida”.
“Gaskiya ne”.
Duk wannan hirar a ofis xin Alhaji Aminu ake yinta.
‘Yanzu ya jikin nasa?”
“Da sauqi”.
“Yanzu na barsu sun tafi duba shi dukkansu”.
Sun zube a sitroom, ita kam Aazeen har ta isa xakin Zaruk, Hajiya Rahma suna gaisawa da Hajiya Amina da tambayar yadda mai jiki ya qara ji, hankalin Hajiya Amina na ga Nurat, tana mamakin me Zaruk zai yi da wannan tatsitsiyar yarinyar, ina ma a ce ta xan fi haka? Babu matar da ba za ta so Nurat ta zame mata suruka ba, duk xabi’unta abin so ne, kunya, biyayya, kawaici da ibada. Nan-nan ta dinga yi da ita, ta so su xan tattauna maganar da Hajiya Rahma sai dai ta ga alamar kamar ita xin ba ta san komai a kan zancen ba.
“Ya aka yi na ganki ke xaya?”
Cike da jimami ta ke dubansa.
“Dukkanmu muka zo, to ina ki ka baro Nurat?”
“Tana can sitroom”.
Ya xan yi shiru, zuwa wani loakci ya koma ya numfasa, “Aazeen, na karaya, kamar Nurat ba za ta so ni ba”.
Ta xan murmusa, “Ka daina shakka Zaruk, babu macen da za ta ganka ba ta yi fatan ta mallake ka ba”.
“Ki gaya min me zan yi ta so ni?”
Lakuce masa hanci ta yi.
“Dube shi don Allah, duk qaramar yarinya ta gama rikita shi’.
“Don ba ki san yadda nake ji ba ne”.
“Ta ya za a yi na ji? Kai ma ka ne ka xora ma kanka,. Babbar soyayyata ita ce in gan ni da kuxi. Duk lokacin da na ga account xina ya soma qasa a nan za ka ga tashin hankalina”.
“ba za ki gane ba, yanzu dai ya za a yi ki iya turo min ita?”
“Korata ka ke son yi kenan ko? Shi kenan bari na turo maka ita”.
Ta miqe ta yi waje.
“Wai ke ba dubiya ki ka zo ba ne, kin wani kime a nan?”
Ta xaure fuska, har kullum gani ta ke duk lokacin da suka kevance da Zaruk xin abin da ta gani shi ne suke yi.
“Tare za mu shiga da Ammina”.
“Tashi ki shiga, ga ni nan”.
Ta miqe cike da damuwa, ko kaxan ba ta son ganin fuskarsa, kullum qara tsanarsa ta ke.
Ta daxe tsaye a bakin qofar, sai da ta ji motsi kamar za a taho ta yi saurin ture qofar ta shiga haxe da sallama.
Yana kwance dafe da gurin ciwonsa, a daidai wannan lokacin zogin ciwon ya addabe shi. Kasa qarasawa ta yi ta tsaya a xan nesa da shi, ko son kallonsa ba ta yi.
Yunqurawa ya yi ya miqe zaune cikin dubanta.
“Qanwata ga kujera ki zauna mana”.
Ta yi yadda ya ce kanta a qasa.
“Sannu, ina wuni? Ya jiki?” Duk ta faxa a lokaci xaya.
“Sai ki ka ji mummunan labari ko?”
Qala ba ta ce masa ba.
“Yau babu makaranta? Ammi tana sitroom?”
Haka ya yi ta soki burutsunsa ya qosa da yanayinta, ya kafe ta da ido.
“Qanwata kin canza, gaya min me ya sa ki yin shiru?”
Nan ma babu amsa, tilas ya tsuke baki cike da tunani barkatai. Ya zai yi ta fahimci yana sonta? Ya zai yi ta fahimci ita ce farin cikinsa?
Zumbur ya ga ta miqe, kasa magana ya yi kawai ya bi ta da ido. Me ya sa ta daina sakin jiki da shi a daidai lokacin da ya fi buqatar haka? Me yake faruwa haka?
“Ya Allah ka nuna mini hanyar da za ta fahimci ita kaxai nake so”. Ya ayyana a zuciyarsa.
“Nurat tafiya za ki yi?”
“Sallah zan yi”.
Ba ta jira jin me zai sake cewa ba ta yi saurin ficewa.
Bayan ta idar da sallah tana sani ta miqe a kan doguwar kujera da faxin kanta ne ke ciwo.
Ba su bar gidan ba, sai bayan sallar magriba.