Sashe 19
Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa*
*1. IZZATU*
*2. MULKIN MALLAKA*
*3. KAUNA CE*
*4. DACEWA*
*5. RASHIN RABO*
*6.TARAIRAYA*
*7. JINI BIYU*
*8. AKWAI BAMBANCI*
*9. TSALAR KAUNA*
*10. YA YI SAKE*
*11. ILLAR SABO*
*12. SO DA SANKARA*
*13. RASHIN RABO*
*14. WATA RAYUWA*
*15. HUBBAN SHADIDAN*
*16. BAKIN K'AZAFI*
*17. MATSALAR KAUNA*
*18. KYAN KUSKURE*
*19. WA YAFI SONTA?*
*20. GABA DA SO*
_NOW_
*KYAUTA ZUCIYA*
```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah```
*_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_*
*_2277439558 UBA Bank_*
Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_*
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*Y* adda ta yi xin ya xaga masa hankali, ya kasa zaune ya kasa tsaye.
“Tabbas ni xin kaina ina ji a jikina irin wannan tashin hankali da ya shiga da walakin, kamar yana tsoron wani abu. Da sauri ya rufa mata baya, kai tsaye sashen su Aazeen ya yi.
Bai ji motsinta a nan ba, haka ne ya sa ya nufi vangarenta, inda ya tadda ta zaune a tsakiyar gado tana faman kuka. Gaba xaya ya gama karaya, dole ya sassauta yana ganin wannan karon tsaurinsa ba zai sa ta biyu ba, dole ne sai ya haxa da lallami.
Ya haye gadon tare da raunana murya.
“Kin kasa fahimtar dalilin biye mata xin da nake yi, a tunani na yadda nake mata xin zai sanya ki yaba mini, sai na ga savanin hakan, in ban biye ma yaran nan ba ya ki ke so su yi? Su ne komai namu, idan ba mu biye musu ba waye za su je gurinsa da lamarinsu ya biye musu? Ki fahimce ni mana, ki duba ki gani Aazeen ta wuce munzalin da za mu takure ta. Ta mallaki hankalin kanta, ta san fari ta san baqi, ba za ta aikata abin da zai cutar da rayuwarta ba, kawai abin da za mu yi shi ne addu’a, lallavawa za mu yi su tafi inyaso sai mu kiyayi gaba kin ji”.
Binsa ta ke yi kawai da kallo cike da mamakin yadda soyayyar ‘yarsa ta rufe masa idanu, har ya kasa tantance fari da baqi.
“Ji yadda duk ya bi ya ruxe, sai faman zuba yake”.
Hannu ya kai yana share mata qwalla.
“Ki yi haquri kin ji”.
Dole ta dinga xaga kai alamar ta haqura.
Labarin da Aazeen ke ba su ya yi matuqar sanya su nishaxi, ita xin kanta cikin nishaxi ta ke ba su labarin. Minal na dariya, “Bai kamata ki yi ma Nurat haka ba, ki karvi zavinta, Hajiya ta. Sau tari abin da ake xauka wasa yakan dawo abin burgewa…”
“Babu mamaki wani alheri ne ya tunkaro ki”. Zee ta katse ta da faxin haka.
“Hajiya ta ki nemi ganinsa, ke ma za ki yaba. Hajiya alheri na tunkaro ki kina wasarere?”
Aazeen ta kai mata duka.
“Rufa min baki, alheri ko shirme?”
“Ku tsaya duk ku ji”. In ji Tina.
“Idan da ni ce ita, biye mata zan yi. Bai kamata a ce kin gwale ta ba, musamman yarinya irin Nurat”.
“Tabbas haka ya kamata ta yi”. Minal ta ce.
“Ok, kuna son ku ce in biye ma shirmenta kenan ko? Ok, zan yi yadda ku ka ce, ko ba komai na yi sabon kamu. Allah ya sa xan harka ne”.
“Good aminiyar, ashe kin gane karatun namu?”.
A wannan daren kwana suka yi cur a gindin talabijin suna faman kallon tashar fim xin da addininmu ya haramta mana gani. Abin da ya jawo Mima da Tina suka kasa xaga wa juna aka keve suka yi gefe suna biya ma kansu buqata.
Ita kam Zee chating ta shiga yi da saurayinta, Minal da Aazeen hira suke yi, a haka suka kwana zur sai da aka fara kiraye-kirayen sallah, Aazeen ta xauki filo ta koma gefen su Tina.
“Ni ban ga tsiyar da za ki tsinta a wannan harka ba sai wahala”.
Ta ja tsaki ta yi waje tana faan haxa hanya saboda tsananin baccin da ta ke ji. Sashen Ammi ta nufa domin tashinta. A kan dardua ta riske ta a zaune ta xaga hannu tana kai kukanta ga Ubangiji.
“Na kasa samun nutsuwa, farin cikin rayuwata na fushi da ni”.
Nurat ta dube ta don gaskata abin da kunnuwanta ke jiyo mata.
Aazeen ta dafe kuncin Nurat da hannu biyu ta xago fuskarta.
“Ko ba haka ba ne qanwar?”
Nurat ta yi murmushi, har kumatunta na lotsawa.
“Okey yanzu na amince da zavin abar qaunata, shi ke nan?”
Nurat ta buga tsalle.
“Yayata da gaske ki ke yi?”
“Eh ana”.
Ta rasa inda za ta tsoma ranta saboda tsananin farin ciki.
“Saura kawai na ganshi. Allah ya sa dai qanwata ta iya zave”.
Cike da farin ciki, “Yayata, dole a ya yi miki. Ya dace da ke. Na gode yaya Aazeen”.
“No, kafin ki yi min godiya, ki fara jin sharaxina. Akwai wanda nake son aure ke ma kin san da wannan shi ne burina. Ina son ya zamo mallakina yana da kuxi, ni kuma ina matuqar qaunar kuxi, bana son haxa hanya da talauci muddin na haxu da mutumin nan zan janye naki mijin da ki ka yi min,saidaiidan ke ki aure shi”.
Har ta sa Nurat dariya.
“Yaya ni aure kuma? Hmm har kin sa na ji kunya. To amma shi wancan xin idan bai ce yana sonki ba fa?”
Dariya ta dinga yi har da tafa hannu, ta tsagaita dariyarta cikin duban Nurat.
“Ke a tunaninki har akwai namijin da zai iya cewa ban yi ishi ba? Ki ma daina wannan tunanin, ni na yarda da kaina, kodayake ba za ki fahimci abin da nake nufi ba. Za mu fita da su Zee idan mun dawo za ki haxa ni da shi, kin ji?”
Ta miqe ta yi waje.
Nurat ta yi ajiyar zuciya, wani irin farin ciki ya ci gaba da lulluve mata zuciya.
*** *** ***
“Ba ka isa ka ce za ka juya wa Nabila baya ba, wannan karon dole ne a yi wannan aure inyaso kabarta a gidan nan, ka sani kullum ina jin nauyin mutanen nan, karo na uku kenan mahaifinta na yi mini maganar yaushe za a saka ranar auren nan, don haka yau ba za ka bar gidan nan ba sai ka sanar da ni. Ba ka san cewar cikar kamalar xan Adam shi ne aure ba?”
Miqewa ya yi tsaye, tare da juya mata baya.
“Ummita, kin sani ba ni da wata kamala, don Allah ki yi haquri ki qyale wannan maganar”.
Da sauri ta zago gabansa, a can qarqashin zuciyarta ji ta ke yi tamkar ta sa kuka da kalamansa mai narkar mata da zuciya.
A zahiri kuma ta xaure fuska, “Na sani kada ka yaudare ni na san dalilin janye-janyen nan naka. Ita Nabila ai ko ma ya ta ke bai kamata ka duba haka ba, karamcin iyayenta gare mu za ka duba ko da kuwa a ce tana zaman kanta ne”.
Ya sanyaya murya, “Ummita, idan na ce zan aure ta ba kya ganin abin zai yi min yawa haka? Rayuwata da ta yarana za ta qara lalacewa, abin da ya faru a kaina ba ni na xora wa kaina ba, sai dai ba zan so a ce ni ina ganin kuskure in take saboda kawai wata alaqa. Don girman Allah Ummita ki qyale ni, ba zan iya ba, ba kya ajiye min kara na tsallake sai dai wannan karon ki yi min afuwa”.
Yana gama faxin haka ya juya zai fita.
Kuka ne ya qwace mata, ta durqusa kamar qaramar yarinya, dole ya juyo a ruxe ya qarasa gare ta. Xago ta ya yi yana goge mata qwalla.
“No Ummita, don Allah kada ki yi min haka, kin san matsayin hawayenki kuwa a gurina? Shin kina son na lalace?”
Da sauri ta girgiza kai.
Ya jawo hannunta ya zaunar da ita, ya koma ya buxe firij ya tsiyayi ruwan Faro a glass cup, da kansa ya ba ta a baki. Ta sha ya ajiye kofin.
“An yi an gama Ummita, ki bari na haxu yau da Nabila sai mu yanke hukunci, kin ji ko?”
Daxi ya kama ta.
“Allah ya yi maka albarka Babana, Allah ba zai tozarta ka ba insha Allah”.
Tsararren qaton hall xin da kallo xaya za ka yi masa ka yi tunanin fada ce ta shugaban qasa. Gurin ya yi matuqar tsaruwa, kujerun gurin ma kaxai abin kallo ne, yadda jama’a suka zazzauna a kan kujerun kaxai abin burgewa ne.
Hall xin ya yi shiru, sai sautin muryar Ahmad Deedat ne kawai ke tashi. Sanye yake da wasu fitinannun qananan kaya, wanda ya bi ya kwanta a fatarshi. Fuskar nan sai sheqin annuri ta ke. Ya wani qara kyau. Ya xan dakata da maganarsa lokacin da ya hangi wayarsa na wuta alamar ana kira. Qanwata ya gani a kan fuskar wayar.
Mamaki ya ke yi, Aazeen a wannan lokaci? Lafiya kuwa? Dole ne ya xaga wayar ya nemi su ba shi minti biyu, ya koma farfajiyar kamfanin wayar a kunne.
‘Kana can ka mance da ni ko?”
Muryarta ta ratsa dodon kunnensa.
“Da a ce ba ki kira ni yanzu ba da jimawa kaxan ni zan kira ki”.
Ta yi dariya har yana jin sautin dariyar.
“Ka ji ka da qoqari, ina za ka samu katin?”
“Xazun na saka xari biyu na kira Kakata, akwai bonus”.
“Na ji ka ce za ka kira ni, kana nufin kana kewata kenan?”
“Sosai ma kuwa”.
‘Okey, gaya min yaushe za ka zo?”
Ras! Gabanshi ya buga.
‘Har kin shirya ganina?”
“Eh mana, sosai ma”.
Ji ya yi an qwalla mata kira. Xuf! Ya ji wayar ta katse.
Ya yi murmushi, “Ba mu tava yin sallama da ke ba”. Ya faxa a bayyane cikin murmushi.