← Book details Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 28

Sashe 2

Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*** *** ***
Gaba ɗaya ‘yan jam’iyyar hankalinsu a tashe ya ke, cikin kakkausar murya Injiniya Usain ya ke magana.
“Ba mu san me ye dangantakanka da shi ba, mun sani ka sanshi, kai ne kaɗan ka san ta in da za mu gane waye shi, amma ka qi ba mu haske, yaro qarami yana faman shigar mana hanci da qudundune. Ka gaya mana sa, ko mu ɓatar da shege”.
Dr. Munir ya furzar da huci mai zafi, wani irin miki ne ke taso masa.
“Na kasa tantance shi ɗin waye kun fi kowa sanin in da ya ke yadda bami, shu’umi ne shi tamkar aljani”.
Ya sauke ajiyar zuciya, “Mu dai mu tsananta bincike”.
Ahmad Deedat kwance a kan wani faffaɗan gado lulluɓe da wani lallausar bargo ruwan damusa. Idanunsa a lumshe shi ba bacci ba, ba kuma ido biyu ba, muryar Sudais cikin rairo Suratul Mulk ne ke tashi a hankali. Ya so ma jin rurin wayarsa. Muskutawa ya yi cikin gyara kwanciyarsa ba shi da alamar kai wa wayar agaji har ta katse. Ba a ɗauki wani lokaci ba ta sake ɗaukar ruri. Ya ja tsaki ya miƙe zaune, ya dubi windo yana kallon in da sojoji ke faman shawagi. Ya ja tsaki, “Idan mutuwa ta zo ba za ku hana ta ɗauke ni ba”. ya ce a ransa.
Ya miƙa hannu zai ɗauki wayar, ta sake katsewa. Ya maida kai ga kallon agogon da ke manne a jikin bango. aƙarfe shida na safe.
“AAZEEN!” ya faɗa a ransa.
Da sauri ya sake ɗaukar wayar ya shiga jujjuya ta a hannunsa.
“Yau akwai rigima kenan”. Ya sake ayyanawa a ransa. Ya yi murmushi, daidai lokacin ya sake jin rurin wayar, ya yi saurin amsawa tare da karawa a kunne.
“Me ya sa ba za ka ɗaga min waya ba”. ɗasasshiyar muryarta ta ratsa kunnensa, muryar da ya fi ƙauna fiye da kowacce murya, muryar da ta fi kowacce murya burge shi. Haka kawai sau tari ya ke kewar muryar, bai san dalili ba idan bai ji muryar ba ya kan ji tamkar ya yi missing ɗin wani abu mai muhimmanci.
Ta ci gaba da faɗa, “Jiya na kira ba ka yi picking ba, yau ma ba ka da niyya”. Ta wani taƙƙaƙare.
Shi kuma sai murmushi ya ke yi, acting ɗinta na burge shi.
“Au ina ta magana ka ƙyale ni ko?”
Ya ƙunshe dariya a ciki.
“Ki yi haƙuri ƙanwata, ba zan sake ba”.
Duk da bai san wace ce ita ba, amma ya gama karantar halayyarta, akwai ƙuruciya a tare da ita, haka ne ya sanya ya ke biye mata.
“Au? Ka ci gaba da shirun ko?”
“Kin ga ai na ga bai kamata ina katse ki a magana ba…”
“To gaya min”.
“Ba ni da lafiya ne shi ne na sha maganin bacci, wannan shi ne dalilin da ya hana in ji kiran wayar taki”.
Tausayinsa ta ji sosai har zuciyarta.
“Oh! I’m sorry, me ya sa ba ka sanar da ni ba?”
Ya fahimci akwai alamun ruɗewa a cikin maganarta.
“Ta ya ya zan sanar da ke? Kin mance dokar da ki ka saka min na cewar kada na kira, kuma da tuni sai dai ki ji na mutu, kin ga da a ce ma ina kiranki da yanzu na sanar da ke”.
“Sannu, yanzu me ke yi maka ciwo?”
Ya ce, “Ciki da zazzaɓi”.
Ta zaro ido kamar yana a gabanta.
“Tab! An fa ce ba a son namiji ya yi ciwon ciki”.
“Ai na ji sauƙi, na je kyamis…”
Ta katse shi a zabure, “Kana son mutuwa ne? Kada ka sake zuwa kyamis, asibiti za ka je a duba ka. Shi kyamis zuwa ake sayen magani, ko karɓar taimakon gaggawa. Yanzu ka shirya ka je ka ji. Bara na turo maka kuɗi, sai ka je…”
Zai yi magana ya ji ta katse wayar.
Yana zaune a dinning room yana kallon inda Ummi da masu aikinta Dije da Dela suna ta sintiri daga kicin zuwa dinning room. In ka ga yadda ta yi kwalliya sai ka rantse wani gagarumin bikin ko taro za ta je, komai nata abin burgewa, ba ta yadda wani ya yi ma Deedat girki da duk abin da zai kai bakinsa, ba ta da yarda a kan Deedat. Ba ta lamunce kowa ya shige masa in ya wuce Salim da Sulaiman. Ita ke tsara masa komai tun yana yaro burinta ya zamo mutumin da za ta yi alfahari da shi, duk wani mai ƴyamarsa ya yi alfahari da shi ta koya masa dabaru, da duk wani salo, ga shi yanzu ya girma, Allah ya amsa mata dukkan addu’o’inta, ko yanzu ta koma ga Ubangiji ba za ta yi baƙin ciki ba. Abin da kawai ya rage mata shi ne, ya yi aure ta ga jikanta.
Ummi ce ke wannan tunanin a taƙaice, kawai Deedat ya zuba mata ido, da alama ta yi nisa. Ya shafi gefen fuskarta. Ta yi firgigi tare da sauke ajiyar zuciya.
“Ummina, me ke damunki ne?”
Ta taɓe baki haɗe da ɗaga kafaɗa.
“Me ko zai dame ni bayan ga ni ga ka?”
Ya yi murmushi, ya ɗan kurɓi shayi.
Da sauri ya ajiye kofin saboda zafinsa.
“Oh God! Sannu”.
“Shi ke nan Ummi… da ma ina son zan je gurin Kabir, kuma…”
“Ya isa, ban amince ba”.
“Don Allah Ummi ki bar ni, babu abin da zai same ni”.
“Idan ka je ba da yawuna ba, in kuma ka ƙi ji ga hanya”.
Ya lura da yadda ranta ya ɓaci. Ya miƙe ya ƙarasa gabanta, ya dire a kan gwiwoyinsa.
“Afuwan, ba zan sake ɗaga maganar ba”.
Ta ɗan saki fuska, ta sa hannunta biyu ta tallafi haɓarsa.
“Ka tabbata?”
Ya jinjina kai.
“That’s good! Na mance ban gaya maka ba, jibi Nabila za su dawo, Hajiya

*💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞*

*NA*

*BILKISU H.MUHAMMAD*
_(Matar Auwalu By fos zage)_

*Free page 2 3 4*

*_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_*

*Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa*

*1. IZZATU*
*2. MULKIN MALLAKA*
*3. KAUNA CE*
*4. DACEWA*
*5. RASHIN RABO*
*6.TARAIRAYA*
*7. JINI BIYU*
*8. AKWAI BAMBANCI*
*9. TSALAR KAUNA*
*10. YA YI SAKE*
*11. ILLAR SABO*
*12. SO DA SANKARA*
*13. RASHIN RABO*
*14. WATA RAYUWA*
*15. HUBBAN SHADIDAN*
*16. BAKIN K'AZAFI*
*17. MATSALAR KAUNA*
*18. KYAN KUSKURE*
*19. WA YAFI SONTA?*
*20. GABA DA SO*

_NOW_
*KYAUTA ZUCIYA*

```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah```

*_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_*
*_2277439558 UBA Bank_*
Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
Chapter 2 · 0% Book details