Sashe 1
Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
*💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞*
*NA*
*BILKISU H.MUHAMMAD*
_(Matar Auwalu By fos zage)_
*Free page 1*
*_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_*
*Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa*
*1. IZZATU*
*2. MULKIN MALLAKA*
*3. KAUNA CE*
*4. DACEWA*
*5. RASHIN RABO*
*6.TARAIRAYA*
*7. JINI BIYU*
*8. AKWAI BAMBANCI*
*9. TSALAR KAUNA*
*10. YA YI SAKE*
*11. ILLAR SABO*
*12. SO DA SANKARA*
*13. RASHIN RABO*
*14. WATA RAYUWA*
*15. HUBBAN SHADIDAN*
*16. BAKIN K'AZAFI*
*17. MATSALAR KAUNA*
*18. KYAN KUSKURE*
*19. WA YAFI SONTA?*
*20. GABA DA SO*
_NOW_
*KYAUTA ZUCIYA*
```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah```
*_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_*
*_2277439558 UBA Bank_*
Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_*
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
ABUJA
Tsarin unguwar tamkar a Turai, unguwa ce wadda ƙaramin mai kuɗi ba zai taɓa iya mallakar muhalli a cikinta ba, shahararrun masu kuɗi waɗanda su ka ci su ka tada kai irin manyan ‘yan siyasa, ƙusoshin gwamnati, ministoci, ‘yan majalissu, sanatoci. Su ne su ka yi sansani a cikin wannan unguwar. Cikin unguwar da kewayenta ba za ka taɓa ganin ƙasa ba, ƙamshin unguwar kaɗai ma ya fita daban. Manyan gidaje masu ɗauke da wasu irin manyan get, su suka fi yawa a nan. Kai kan ka kana dosar unguwar za ka san ka zo unguwar masu gidan rana, ta yadda tun daga nesa za ka hangi sojoji suna ta faman safa da marwa ɗauke da bindigoginsu, kamar masu shirin fita yaƙi. Ko kaɗan babu mabuƙaci a cikin wannan unguwa, za ka gane hakan ne ta yadda za ka dinga ganin kaji a abin shara waɗanda su ka yi funfuna. Shiru-shirun unguwar ya fi komai daɗaɗa wa ‘yan cikinta. Idan kai kaɗai ne a gidanka sai ka mutu har ka ruɓe babu wanda zai sani.
Akasari ‘yan cikin unguwar kansu kawai suka sani, babu wanda ya damu da shiga harkar wani. Ba kowane maƙoci ne ya taɓa ganin maƙocinsa ba, saboda kowanne gida garƙame ya ke da get, tsakanin get ɗin ma zuwa gidan sai an yi tafiya mai nisa, wanda ko da yanka ka za a yi in maƙogoronka zai tsago saboda ihu, babu wanda zai ji ka. Akasarinsu ba su san me ake nufi da talauci ba, ba su san me ake nufi da sanyi ko zafi ba. Kullum suna cikin A.C, ba a taɓa ɗauke wuta wuta a wannn unguwar, duk da suna amfani da sola, shirun unguwar tamkar ba a duniya ba, in ka ji hayaniya sai ta motoci.
Wannan kenan.
Yana zaune a babban sitroom idanunsa a kan akwatun talabijin, yadda ya ga talakawa na kukan farin ciki, tare da sanya masa albarka ya dinga jin tsigar jikinsa na tashi. Burinsa kullum ya ga ya sanya talakawa farin ciki, hakan ne kaɗai ke sanya shi nishaɗi. Daga can bayansa Hajiya Khadija ce wadda ya ke kira da Ummi, motsinta ya jiyo ya yi saurin miƙewa ya ƙarasa gare ta. Zai yi magana ta riga shi.
“Ka kalli yadda talakawa ke farin ciki, zuciyarsu fari ƙal! Deedat ɗina, kai ma Allah ya faranta maka”.
Ya riƙo hannunta.
“Ummina, duk ke ce. Komai na zama ke ce sila, ke ce ki ka ɗora ni a wannan turba. Na gode miki ƙwarai da gaske Ummina”.
Ya kwantar da kai a kafaɗarta. Ta shafa gashin kansa.
“Allah ya yi maka albarka”.
Komawa su ka yi suka zauna, tare da sake mai da hankali a kan akwatun talabijin. Daidai lokacin da wasu matasa ke roƙon ya fito ya tsaya takarar kujerar gwamna. Ummi ta dube shi, “Ko bayan raina ban amince ka tsaya takarar siyasa ba, ban ƙi ka yi ja-gaba gurin cicciɓa na gari ba har ya kai ga gaci kamar yadda ka ke yi, amma siyasa? Sam ban lamunta ba”.
Yana murmushi, “Ki kwantar da hankalinki, ɗanki ba shi da wannan ra’ayin, burina da man a kada wannan gwamnan, kuma na ji daɗi da ya faɗi tun a primary election, na san gaba ma ba zai taɓa cin nasara ba”.
Ummi ta dinga kallonsa cike da wani irin tausayinsa.
“Ummina, kina tuna baya ko? Ka da ki damu, da izinin Allah sai mun ga bayan wannan gwamnan”.
Ta dinga kaɗa kai.
“Ka bi a hankali, ka dinga sassautawa…”
Kuka ne ke ƙoƙarin ƙwace mata, da sauri ta bar gurin.