Sashe 7
Kyautar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
islamiyya da ire-iren wadannan tambayoyin. Shin wa ke nan yake kauna? “Dankali kawai na gani, ban ga farfesun da na ce ladidi ta yi min ba?” “Kira ta, kila karasawa ne ba ta yi ba, ai babu wanda zai ketare umarninki Rangida”. Ta bude murya baki daya cikin kwala mata kira. A sukwane ta karaso tare da durkusawa a gabanta. Ta watsa mata harara. “Ina kayan karyawata?” “Yanzun nan na hattama, bari na kawo miki”. Da sauri ta yi waje, sai ga ta da kayan karyawar ta jere a gabanta. Janye plate din Ammi ta yi a gabanta. “Kada ki taba komai a nan ba tare da kin je kin sauya kayan jikinki ba”. “Haba Ammi, kashe ni za ki yi? Na ce da ke yunwa nake ji. Ni kam gaskiya a’a”. Ai kuwa ta shiga yi mata fada, takaici kamar Aazeen za ta mutu. Baqin cikinta wai Ammi ta yi mata fada a gaban mai aiki. Juyin duniyar nan ba ta mike ba, ta bude farfesun a qufule, cikin neman wanda za ta huce a kansa. Ta dubi Ladidi. “Cewa na yi ki saka min curry? Uban waye ya sa ki? Kawai ba ki yi shawara da ni ba kin yi abin da ki ke so ko?” A sanyaye, “Ki yi haquri, na ga ai kullum ina yi miki amfani da shi”. “Shut up! Ina magana kina yi?” Gaba xaya ta dauki plate din farfesun ta watsa mata a fuska. Wata gigitacciyar qara Ladidi ta saka. Da gudu Nurat ta mike tare da rungume ta a jiki. Ladidi na ta ihu tamkar wadda ake kokarin zare mata rai. Da taimakon Nurat suka nufi famfo. “Man kana ganin abin da Aazeen ta aikata ko?” Hajiya Rahma ta fada tana kallon Alhaji Usman. “Ita ta ja ma kanta. Ya kamata ta dinga kiyaye matakan aikinta, tunda ba kyauta ta ke aikin ba”. “Dad, ina son gaya maka. su Zee fa na tafe”. Aazeen ta fada ba tare da ta nuna nadama a abin da ta aikata ba. Gaba daya ma sun mance da ita Hajiya Rahmar, hirarsu suka shiga na yadda za su sauki bakin nata. Miqewa ta yi cike da takaici, har lokacin tana jin ihun kukan Ladidi, Nurat na faman ba ta haquri. A can shashin masu aiki, Ladidi ta yi matashi da cinyar Nurat ta dage sai bushe mata idanu ta ke faman yi, hankalinta a tashe, yadda idanun suka kumbure sun yi jajir da kyar ta ke motsa su. Hawaye sai faman tsinkowa suke daga idanun. Cikin muryar kuka. “Ladidi sannu, za ki warke. Yana yi miki zafi? Sannu”. Ta rude matuqa, jikinta sai bari yake, zuciyarta fal haushin Aazeen. Karin bakin cikinta shi ne na halin ko’inkular da akai wa Ladidi akalla ya kamata su zo su duba halin da Ladidi ke ciki, yanzu ya za ta yi idan Ladidin ta makance? “Nurat ina son dora girki”. Cikin tausayawa, “Haba ta ya ya za ki iya wani girki? Ki bari ni zan yi kokari in ga na yi”. “A’a Nurat, ki rufa min asiri”. “Kada ki damu babu wanda zai fahimci haka. Ina zuwa… amma dai akwai duk abin da zan bukata ko?” Ladidi ta jinjina kai. “Ok, yanzu ki kwanta ki huta kafin ki tashi na gama kin ji”. “Na gode Nurat”. Ta bi Nurat da kallo tana jin qaunarta a ranta. Halayyarta daban da na iyayenta, kamar yadda ta lura kowa na gidan bai damu da damuwar wani ba, sun dauki rayuwarsu tamkar na turawa, musamman Aazeen wadda duka dabi’unta irin na ubanta ne. Ita kam Hajiya Rahma babu wanda ya fahimci inda ta sa gaba, ba za a dai a kira ta mara kirki ba, kodayake ba lallai a fahimci wace ita ba, saboda ba ta cika shiga shirgin mutane ba, sabanin Nurat wadda ba ta wuce shekaru sha bakwai ba, yarinya mai mutumci da shiga rai, wadda ba ta xauki kanta da zafi ba, ba ta da wahalar sha’ani, kunyarta shi ke kara mata daraja a idanun jama’a, don hakan ya zame mata tamkar wani ado. Tazarar da ke tsakanin kicin da dakunan da ke gidan ya sanya babu wanda ya lura da kai-komonta. Wanke-wanke ta fara yi, ta ci uwar damara. Bayan ta gama ta shiga dogon tunanin abin da za ta dafa wanda ba zai ba ta wahala ba. taliya ta ayyana a ranta, amma ta ya ya za ta sarrafa kayan miya? Ita ba ta taba kwatanta shiga kicin don sarrafa wani girki ba. Komawa ta yi dakin Ladidi, don ta gaya mata yadda za ta yi. Bacci ta ke yi lakadan, har da su minshari. Murmushi ta yi ta koma ta shiga tunanin yadda za ta yi. Tunawa ta yi da tana da littafin girki, da sauri ta nufi ma’ajiyar littattafanta. KADARAR KITCHEN wanda Bilkisu Salisu Funtua ta rubuta ta nemi guri ta zauna, tare da dubo abin da ta ke son dafawa. Ta mayar da littafin ma’ajiyarsa, ta koma kicin ta debo kayan miya ta wanke, ta soma yanka albasa. Ji ta yi wuqa ta shige hannunta, ta kwalla kara tare da sakin wukar yadda ta ga jini na zuba ne ya sanya ta rudewa. A sukwane Zaruk ya dano kicin din ya kai hannu zai riko hannunta. Da sauri ta maida hannun baya cikin tsananin tsoro. “Ki bari in gani, ba ki ga jini ne ke zuba ba?” Ta yi saurin maida hawayen da ke qoqarin silalo mata. “Kada ka damu, kawai jinin ne, amma ai babu zafi”. “Oh God! Wai ke me ma ya kawo ki kicin? Wa ya aike ki?” Ta fara in’ina, ya daure fuska. “Na ce da ke waye ya aiko ki kicin?” Za ta yi magana ya mike a fusace zai fita. “Don Allah ka yi haquri, zan gaya maka. Ka dawo don Allah Yaya Zaruk”. Ya koma ya zauna cikin kafe ta da idanunshi. “Ke nake ji”. “Ladidi ba ta da lafiya shi ne nake taya ta”. Ya sake xaure fuska. “Ita din ce ta ce ki taya ta?” Cikin rawar murya, “A’a, to gaya min”. Dole ta zabi ta ba shi labarin yadda abin ya faru. Ya ja tsaki ya janyo mata kujera. “Maza zauna”. Ba ta da zabi dole ta bi umarninsa. Komawa ta yi ta zauna, nade hannun rigarsa ya yi ya shiga aiki tukuru. Ta dinga kunshe dariya a ciki, ga mamakinta Zaruk ya iya komi. Ya dube ta a sakarce, “Nurat, fito ki yi dariyarki a bayyane”. Ta dabarbarce, “Da gaske Yaya Zaruk ba dariya nake yi ba”. Jalof din taliya ya yi, sai plaintain da ya soya farfesun kifi. Ya diba a cokali ya mika mata. Ya yi mata alama da ta yi testing. Ta karba tana dandanawa. Ya kafe ta da ido. “Ya ki ka ji?” “Yaya Zaruk, ashe ka iya girki?” Ya harare ta, “je ki yi maza ki shirya dinning ko?” “An gama Yayana”. Da sauri ta yi abin da ya ce. Bayan ta gama shirya komai ya ce da ita, zai je ya siya ma Ladidi magani. Yana fita ta shiga wanka.