Sashe 9
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To Baba." Ya masa tare da fara tafiya yana kallon su kamar zai lashe su.
"Kai gaskiya ƙauyen nan da akwai sunan da ake kiran inda yafi ƙauye, haka ya kamata a kira. Dubi ɗan ƙauye kamar a haɗa a yi gida ɗaya, kuma wai a haka suke rayuwa har suke farinciki? Allah na gode maka da ka halicce ni a birni, domin wannan ƙauye ba shi da maraba da maƙabarta, shi ya sa tun da muka shigo ventilation ya canza. Ga mutane kamar kaji kuma babu hyiegene, ai dole ya rinƙa wari." Ya ƙarashe maganar, cikin tsananin ƙyama yana kallon ƙauye tamkar kashi, sannan ya ɗora da cewa,"
"Ga turosu ake ce masa ko turasa, wannan kashin shanun?" Ya ce yana kallon Mommy.
"Turoso kake nufi?"
"Yauwa eh shi." Ya ce mata yana hangen kashin kamar zai yi amai.
Dariya Mommy ta yi, ba tare da ta ce masa komai ba tana kallon hanya.
Sai ƙorafi yake yana jan tsuka. Su kansu sai da suka yi dana sanin zuwa da shi.
Sun yi shiru suna kallonsa cikin mamaki, jin yadda yake sakin magana, ko kunyar ɗan maigari ba ya yi.
"Captain Aliyu, zan iya rantse maka akwai waɗanda suke rayuwa a ƙauye nan kuma suka fi ka farinciki. Ba kuɗi ko jin daɗi bane farincikin rayuwa. Duk wanda ka ga Allah ya halitta, sai ya ba shi abin da zai sanya shi farinciki."
Kauda kansa kawai ya yi, tare da jan tsaki, ba tare da ya ce masa komai ba. Ji yake ya takura saboda gabakiɗaya baya jin daɗin ƙauyen..Ga kayanshi da suka yi staining duk da ya goge da tissue paper.
A lokacin da suka yi sallama, Kaka Tani tana kicin tana gyara tukwane da ta gama wankewa.
Jin sallamar sau uku ya sanya ta zabga tsaki, sannan ta fara tafiya tana faɗin,"Na san ba ya wuce 'yan kawo ƙara. Bari na je na ji uban abin da za a ce ta aikata, kuma wallahi ko sama da ƙasa za ta haɗe ba wanda zai duƙar mini jikalleta."
Tana wannan ƙorafin ta isa ƙofar gidan, don bala'i ko sallamar ba ta amsa ba.
"Waye ya dame ni da sallama kamar na ci masa ba shi?" Ta yi tambayar, daidai lokacin da ta isa ƙofar gidan tana yafa mayafi.
Kallonsa ta yi ta ce,"To yau kuma mai za a ce ta yi? Don na san zuwanka ba alkairi bane."
"Halinta ya sanya ba na zuwa da alkhairi."
"Au rashin kunya za ka yi mini?" Ta ce masa tana kama baki.
"Baba ya ce na kawo ɓaki suna neman gidanki."
"Ni ƙawar mai daddawa! Su waye ne?" Ta yi masa tambayar tana dafe ƙirji.
"Ni ma ban san su, amma a mota suka zo kuma ƙatuwa, don kawai a ƙasa take tafiya da na ce jirgi ne."
"Nufinka mai kama da jirgi?" Ta yi masa tambayar cikin ruɗu.
"Eh, ga wani sanyi kamar raɓa a ciki."
"Kai muje na gani anya ba makuwa suka yi ba?Saboda iya sanina babu wanda zai zo a mota yace yana nemana."
Fara tafiya ya yi tana binsa a baya, yayin da zuciyarta take cike da tsoro.
Turus! Ta tsaya tana kallonsu cikin zallar mamaki.
"Su waye waɗannan?" Ta yi ma kanta tambayar tana kallon su.
Kamar yadda take kallonsu haka suke kallonta, musamman Captain Aliyu da yake mata kallon ƙaskanci.
"Da ma gurin wannan tsohuwar mai kama da lagwani muka zo? Na sha wannan wahalar." Ya tambayi kansa yana mata kallon sama da ƙasa. Tsananin mamaki ya kama shi, duk da cewar ya san ba wasu mutane masu aji za su gani ba, amma bai yi tunanin 'yar tsohuwa kamarta za su zo gurin ta ba. Siririn tsaki ya saki ganin tana sanye da riga da zani da ɗankwali, dukanninsu daban-daban, sannan fuskarta duk ta yi rama alamun tsufa, har idanunta sun fara shigewa ciki. Har ta fara duƙawa.
"Bayin Allah lafiya kuwa, ko dai makuwa ku ka yi?" Ta yi musu tambayar tana kallon su.
Wai ya ne readers ba kwa comments gaskiya ya kamata na ga ruwan comments yana tashi.
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 5

"Nan ne gidan Tani ƙanwar Malam Aifi, wanda yake wankin hula. A Ƙauyen Madu?"
"Eh, ni ce bayin Allah ya aka yi kuka san Yayana marigayi Malam Aifi?" Ta furta tare da zare ido tana kallonsu cikin tsananin mamakin yadda aka yi suka san shi, ganin su 'yan birni kyawawa da su.
Murmushi ya yi, ganin yadda ta shiga damuwa.
"Ki kwantar da hankalin ki baƙi kika yi daga birni."
"Ikon Allah ni?" Ta yi masa tambaye tana nuna kanta.
"Eh, zan iya shigowa saina yi miki bayani?"
"Ku zan tambaya don yadda na ganku jikinku kamar tsada, wataƙila ba za ku iya shiga ba."
Murmushi ya ƙara yi a karo biyu, ya kalli iyalansa ya ce,"Mu shiga ciki."
Captain Aliyu da yake tsaye yana kallonta a wulaƙance ya ce,"Wa ni? Allah ya tsare ni ku je kawai." Ya ce masa yana kallonsa yana taɓe bakinsa kamar ya ga kashi.
Ganin abin da ya yi, sai kunya ya kama shi, ba tare da ya iya cewa komai ba, ya shiga cikin gidan.
"Ni ban san wane irin jarrabawa na faɗa ba, har daddy ya sanya na biyo shi ƙauyen nan, domin wallahi da na san zan zo ƙauyen nan ba zan dawo ba, saboda takura da kashin shanun da nake gani a ƙauyen nan, har ji nake numfashinsu zai ɗauke." Ya ce tare da buga bayan motar.
A cikin gida, Kaka Tani mamaki sosai ya kamata bayan sun sanar mata daga inda suke.
"Ikon Allah, yanzu kai ɗan gidan Yaya Binta ne?"
"Eh wallahi nine ɗanta na farko, ita ta turo ni kan na zo na ga inda kike, kuma tun da na gani in sha Allahu za mu zo."
Kuka ta fashe da shi tana faɗin,"Ashe Binta ba za ta manta da ni ba? Oh Allah dube ka yadda ka yi ƙatoto abin ka, ka girma ka tara iyali. Rabona da ita tun da ta zo ganin gida a lokacin da ta yi arba'in ɗinka."
Shafa kansa kawai ya yi, ba tare da ya ce komai ba, yana murmushi.
"Umma, ku ce wa direba ya shigo da kaya a mota." Ya ce yana kallon Kaka Tani da take ta kallon su, kamar za ta lashe su.
A ƙofar gida kuwa, captain Aliyu yana tsaye cikin ɓacin rai yana kallon wayar da, da network har yanzu bai dawo ba.
"In har ana son mutum ya mutu ba tare da lokacin su ya yi ba, ace ya yi rayuwa a ƙauyen nan." Ya ce yana kallon wasu almajirai da suka zo wucewa.
Jimmalo ce take tafiya tana dariya, tuna abin da ta yi wa aljani. Idan dariyar ta ciyo ta har sai ta daka tsalle.
Ƙawarta Karime ta jawo da sauri wacce ta hango ta, ta rugo da gudu tana nishi.
"Ke zo ki ji labari?"
"Ni ma zuwa na yi na gaya miki..."
"Don ki tsaya ki ji nawa, kin san dai in ina magana bana bari a katse ii?"
"Ina jin ki to." Ta ce tana kallonta.
"Balaraben aljani na tsorata.."
"Aljani kika ce?" Ta yi mata tambayar tana matsawa kamar ita ce aljanin.
"Eh, wallahi yarinya. Ba ki ga yadda ya firgita ya riga da gudu ba." Ta ƙarashe maganar tana yaba jarumtarta, tare da sakin mahaukaciyar dariya.
"Ni dai na san ance duk wanda ya ga aljanu sai ya mutu Jimmalo?"
"Au ƙarya zan yi miki kenan? To aradun Allah yau idona idon aljani, kuma gani a gaban ki ras ban mutu ba, an gaya miki ni matsoraciya ce?" Ta ce da muryar ƙatti.
"A'a ni ban ƙaryata ki ba, kawai mamaki na ke yi."
"Ki daina mamaki, ina kan bishiya na ganshi yana tsaye kyakkyawar gaske! Da fari na firgita, amma da na daure na janyo masa aya, sai kawai ya fara hayaƙi zai ƙone, ganin haka na maka masa mangwaro , da sauri ya ɓace ɓat." Ta shirya mata ƙarya tana jinjina kanta.
"Kai Jimmalo ki ji tsoron Allah. Ke da ba kya zuwa makarantar allon sai kin ga dama, har yaushe kika iya karatun da za ki ƙona aljani?" Ta yi mata tambayar cikin mamaki.
"To uban me kika ɗauke ni? Ai gara ni ina zuwa in na yi ninya.. Ke da ko kin je kanki kamar ɗankwali yake ba ya ɗauka? Ina fa ji ranar nan kina karatun sallah kika ƙaranta addu'ar shiga bayi a maimakon sura"
"Ni Jimmalo ƙarya za ki yi mini?"
"Ki rantse da Allah ba haka aka yi ba?"
Cikin jin kunya ya ce,"Ai Allah ya halicce ni a haka." Don ta tuna ranar.