← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 52

Sashe 46

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba ta ƙara shan mamaki ba, sai da suka zo yin sallah. Sai kawai ta ji hawayen tausayi yana bin ƙuncinta. A ranta ta ji tana son taimaka mata a rayuwarta. Don haka ta ƙudurta za ta roƙi Mommy, in suka yi hutu ta kawo Jimmalo hutu Zariya.

Da suka idar da sallah falo suka koma. Bayan sun yi kallo suka kashe kayan kallon sannan suka shiga don su kwanta.

A daren tana naniƙe da ita kamar angon da ya yi sabuwar amarya. Ko da aka zo bacci sai ta daka tsalle ta ce alan baran ɗakin da Anty Amarya za ta kwana.

Mufida
Tun daren ranar Mufida, take ta tunanin yadda za ta samu ta sanya maganin kafin su tafi. Suna kwance kowa ya yi bacci, amma ban da ita da ta lula duniyar tunani, sai dai har ta fara jin bacci ba ta samu mafita ba.

Da safe da suka tashi, tun asuba Anty ta sanya Jimmalo ta yi sallah. Duk da cewar sallar da ita gwara babu, haka dai ta yi ta kallonta har ta sallame. Ta san cewa a yanzu ta ce za ta koya mata karatun sallah ɓata baki ne.

Jimmalo tana zumɓura baki, Anty ta taimaka mata ta shirya zuwa makaranta. Ita babu abin da ta tsana a rayuwar birni zuwa makaranta.

Kayanta gogaggu wanda Alu, mai wanki da guga ya goge mata ta sanya. Ga shi Anty ta tilasta mata ta yi wanka. Sai ta fito cas abin ta. Suna zaune a falo ana karyawa.

Mommy ce take kallonta cikin sha'awa ganin yadda ta canza. Ta so ace Anty ta daɗe yadda za ta gyara mata ita, amma da ta tuna an kusa yin hutu sai ta bari in an yi hutu sai ta kaita.

Da suka je makaranta wanna karan babu harare-harare, ta yi zamanta kan kujera. Ko yaran da suke kallonta ganin yada ta yi shiru suna son tononta ba ta kalla ba.

Har aka yi darasi uku, sannan aka kaɗa break tana zaune bata tare da ta kula kowa ba. Ko malamar da ta shigo, duk maganar da ta yi mata ta yi rubutu kan dole ta gaji ta ƙyale ta.

Bayan ta fita, sai ta je ofishin Principal ta yi masa ƙorafin ba ta rubutu. Jin hakan ya yanke shawarar zai kira Daddy, da kansa ya bashi shawarar a ɗaukar mata tuitor.

Tana zaune tana cin abincinta a cikin kula, wani yaro mai suna Muntazar ya kalle ta ya kwashe da dariya.

"Ke maman Aji ba haka ake cin abinci ba."

Jimmalo jin abin da yace sai ranta ya ɓaci da sauri ta kalle shi."Wuce ka bai guri mara kunya, don ni karya ka zan yi." Ta ce mishi tare da daka masa tsawa.

A maimakon ya wuce, sai ya kwashe da dariya, domin kamar shi ma irin taƙadiran yaran nan ne.

"Maman aji! Maman aji." Ya fara ihu yana faɗin haka jin waƙar da yake yi, sai wasu daga cikin yaran suka ɗauka har da jan mata hijabi.

Jimmalo cikin tsananin fushi ta miƙe tana huci kamar zata haɗiye su. Ita mamakinsu take yi domin in har za ta yi musu wani abu, tabbas sai ta illata wani.

Tana shawarar ko ta ƙyale su, amma sai ya ƙara jan mata hijabi. Ba tare da dogon tunani ba ta fisgoshi tare da maka shi a ƙasa.

Wani irin ihu ya sanya wanda ya sa yaran suka shiga taitayinsu.

"Wayyo ƙafana ta karya ni." Ya furta cikin kuka yana taɓa ƙafar.

Kallon yaran ta yi tana zare ido."Saura ku dama na gaya muku kashe ku zan yi." Ta ce tare da komawa ta zauna, ba tare da ta damu da ihun da yake yi ba

Ganin ya kasa tashi yana tsala ihu, sauran yaran suka ruga da gudu suka sanar wa Anty. Da sauri ta shiga cikin tashin hankali. Mamaki sosai ya kamata, na rashin imaninsa tana cin abincinta hankalinta kwance.

Da gudu ta ƙarasa gurinta ta zuba mata bulalar."Ke wace irin sheɗaniyar yarinya ce? Za ki kashe musu yaro?"

"Shi ne sheɗani da ya tone n.."

Kafin ta gama maganar ta ƙara zuba bulala. Wanda ya sanya ta zabura ta riƙe bulalar tana zare ido.

"Dukana za ki yi? Ka ga mini fitsarrarriyar yarinya."

"Wallahi kika ƙara dukana sai na rama tun da bance ya tone ni ba." Ta furta tare da ƙwace bulalar.

Jin yadda jikinta yake da ƙarfi sai ta sakin mata, domin ko da ta gwada ƙwacewa a yadda ta ji karfin jikinta ba za ta iya ba."Saki ko in ƙara miki ƙatuwar banza kina ƙatotuwa da ke a sanya ki a cikin yara."

"Kece jahila da kika kasa gane rashin kunya ya yi mini.."Ba ta ƙarashe maganar ba Principal ya shigo, ganin tana ƙoƙarin dambe da malamar sai wani ya ruga ya kira shi.

"Safeeya Abdullahi, saki bulalar nan!" Ya daka mata tsawa yana faɗin haka.

Jin tsawar ya sanya ta saki tare da ƙunƙunai. "Ɗauke shi a ka shi asibiti." Ya furta tare da ƙarasowa ya fara zuba mata bulala.

Tun tana jurewa har ta fara hawaye sosai. Hankalin Principal ya tashi lokacin da aka kira shi, aka sanar da shi Muntazar ya karye.

Cikin takaici ya karɓi bulalar daga hannun sajan ya ci gaba da dukanta.

"Ku yi mata shegen duka sai mu tafi gidansu."

Don Allah ku yi mini hakuri na yau babu yawa saboda uzuri.🙏🙏🙏🙏🙏🙏

Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.

*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!

08144072423

PAGE 23

*Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso kusa kar ayi* *babu ke*

*Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so*

*ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa*

*MTN 1gb 650*
*2gb gb 1300*

*Iya adadin da kuke so muna turawa*

*"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da kayan kitchen duk akan farashi me rahusa*

*Arabian oud*

*Lamsa oud*

*Black oud*
*Da Duk wane oud da kake nema*

*Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa*

*Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin*

*S D Y COLLECTION AND KITCHEN*

*Adress ringi road, na dorayi, kano*

*muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah*

*Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap*

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

*08130902505*

Sai da suka yi mata dukan tsiya sannan suka tasa ta zuwa gida.

Jimmalo ta ji dukan domin duk juriyarta sai da ta yi kuka.

Mommy da Anty suna kicin girki suke yi. Anty ce take yin gudun kurna, sakamakon abinci da ba su cinye ba, ya sanya suka ba ri su yi da rana.

Kicin ɗin ya ɗau kamshi Mommy duk ta kosa a kammala. Sai maganar yadda zai yi daɗi take yi, Anty na yi mata dariya.

Principal tun a hanya ya kira Daddy ya sanar mishi, sannan ya rantse korarta zai yi, domin ransa ya ɓaci sosai ganin yadda iyayen yaron suka yi fushi. Zai iya cewa tun da yake a makarantar, wannan karon na farko kenan da ya faru.

Daddy hankalinsa ya tashi sosai jin yadda yake magana cikin fushi. Duk haƙurin da yake ba shi bai saurare shi ba ya kashe wayar. Dafe kansa ya yi cikin takaici jin abin da ta yi.

Kan dole ya baro kasuwan ya dawo hankalinsa a tashe. A lokacin da suka iso gidan, Maigadi ya shiga ya kira Mommy. Cikin fargabar wanda ke kiran ta fito ita.

Tana fitowa ta ga Jimmalo ta ci kika tana zare ido. Gabanta ne ya faɗi sosai ta kasa ƙarasawa gurin. Sai da ta ɗan ɗauki lokaci cikin rashin madafa, sai ta ƙarasa tana faɗin,"Sannunku bayan Allah. Jimmalo mai kika yi?" Ta yi tambayar tana kallon Principal ɗin da ya ci magani.

"Yarinyar nan ba ta da mutunci ta karya yaro."

Salati ta saki sai ta rasa abin da za ta ce. Tana cikin wannan jimamin sai ga motar Daddy. Wani irin ajiyar zuciya ta saki ganinsa, domin ba ta san abin da za ta ce ba.

Daddy parking ya yi sannan ya fito cikin motar cikin damuwa.

"Jimmalo, ba kya jin magana ko? Saboda me za ki karya shi?" Ya yi mata tambayar, daidai lokacin da Captain ya sanya maigadi ya buɗe masa get zai fita.

Ganin Daddy a gurin da Mommy ya tabbata ba lafiya ba, musamman yadda fuskokinsu suke ɗauke da tashin hankali.

"Wannan sheɗaniyar yarinya mai ta yi?" Ya furta a ransa sannan ya fasa shiga cikin motar ya ƙarasa gunsu, daidai lokacin da ta ce,"Tonona ya yi ni kuma na yi masa ƙufula ɗaya."

Dukanninsu babu wanda ya gane hausar da ta yi musu. Jin abin da ta ce Aliyu ya kawo mata mari ba tare da ya ji abin da ta yi ba.
Chapter 46 · 0% Book details