← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 52

Sashe 50

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani tsuka ta ja mai ƙarfi tana aika masa da harara. Ta saki tana zuwa makaranta da islamiya duk da babu abin da take ɗauka. Burinta ayi hutu taje gidan Anty Amarya da wani lokacin Mommy tana kiranta su gaisa, musamman in ta ƙi sallah ko ta yi rashin kunya.

Sai aka yi sa'a, sam hankalinsa ba shi a inda take ballantana ta ji tsakin.

Ganin ya shiga ciki sai ta ci gaba da wasanta, kamar kuma ance ta miƙe sai ta yi hanyar ɗakinsa.

Ganin ɗakinsa a buɗe, sai ta tsaya tana tunanin yaune Allah ya ba ta sa'a, zata rama karya mata hannu da ya yi. Har ta dumfari kofar, sai ta ji muryar Umma tana kiranta a bayanta.

"Safeeya, kina ina Mommy na ta neman ki?" Ta yi mata tambayar tare da ƙarasowa.

Jimmalo, sai ta ɗan haɗe rai, duk da cewar yanzu ta saki dasu har magana take musu, amma ba sosai ba sai in tana cikin farinciki.

"Ina kallon gidan ne." Ta ce mata tare da juyawa za ta tafi.

"Ok, ni kuma ya Captain ya ba ni ɗan makullinsa na gyara masa ɗakinsa, ashe bai kulle ba."

Ba ta ce komai ta wuce ta bar gurin. Umma da ta shiga ta ɗauko masa wayarsa da ya umurce ta je don ta kai mishi ta dawo.

Ganin ta bar gurin ta koma, da sauri tana addu'ar kar ta dawo sai ta aiwatar da kudirinta.

Sa dai ko da ta shiga, babu tarkace a cikin ɗakin komai a killace, ballanatana ta ga inda yake ije takaddunsa ta yaga don su zama jahilai ya daina kiranta da jahila. Ganin ba ta ga komai ba, sai ta fara duba jakarsa da ya zo da ita, nan ma babu bin da ta gani, sai kayansa da turare sai brush da makilin.

"Laa! Ashe yana wasa da bulumbulum!" Ta furta cikin zallar mamaki lokacin da ta ga condom.

Cikin sauri ta tura a cikin siket ɗinta, tana murna za ta yi wasa da shi. Jin tafiya sai ta fito da sauri, da takaicin ba ta samu komai ba.

Umma ganin ta a ciki mamaki ya kamata."Safeeya, lafiya mai kike yi a cikin ɗakin Ya Captain?" Ta yi mata tambayar tana kallonta da tuhuma.

"Babu komai." Ta ba ta amsa tana ƙoƙarin fita fuskarta a ɗaure.

Duba ɗakinsa ta yi sai bata ga komai, da zata zarge ta ba, saboda ta mayar da kayan. Ganin haka sai ta gyara masa ɗakin ta wuce cikin gida.

Jimmalo ba ta fito da bulumbulum ɗin ta ba, sai washegari da ya yi tafiyar, don har ta manta sai kawai ta tuna. Cikin sauri ta ɗauko cikin kayanta sannan ta fito waje tana ƙoƙarin hurawa, amma duk yadda ta so ta hura ya ƙi tashi irin na bulumbulum.

"Kai wannan bulumbulum na manya ne bari na zuba masa ruwa." Ta ce tare da ƙarasawa bakin tanki ta fara ɗura ruwa a cikinsa.

Nufaisah, da ta fito da gudu-gudu sauri-sauri za ta fita daga gidan, saboda makaranta za ta je kuma suna da test ta yi latti.

Har ta wuce Jimmalo, sai kuma ta ja ta tsaya cikin mamaki tana zare idanunta.

"Safeeya, ina kika samu wannan abin? So kike cuta ta kama ki?" Ta yi mata tambayar tare da ƙarasawa gurinta tana son ta ƙwace.

Matsawa ta yi ta ɓoye condom ɗin a bayanta.

"Ba zan ba ki ba, bulumbulum ne na ke wasa da shi."

Jin abin da ta ce, sai ta kalle ta cikin mamaki."Ba bulumbulum bane condom ne."

"Ni fa ban san wani candoom ba, kawai ki bar ni na yi wasa da shi." Ta ƙarashe maganar za ta gudu.

Da sauri ta kai hannu za ta ƙwace ta ce,"Cuta ake samu a cikinsa a gina kika samu? Sannan abin da ake y.." Sai kasa karasa maganar rashin sanin yadda za ta gaya mata abin da ake yi da shi.

"A ɗakin wancan mai kama da zabiyan."

"Kina nufin ɗakin Ya Captain?" Ta yi mata tambayar cikin shakku da razana.

"Eh, a ɗakinsa na samu, na san kuma so kike na baki ki mayar masa."

Mamaki da al'ajabin abin da yake yi da shi ya kama ta. Fara tunanin ta yi ko ƙarya take masa, amma ganin yadda take sanya abin a bakinta tana hurawa, sai ta gasgata bata san abin da ake yi da shi ba.

"Ke nan ya Captain ɗan iska..." Ta kasa ƙarashe zancen tana son kore tunanin da ya zo mata.

"Kai Ya Captain mutumin kirki ne." Ta ce tare da surfatan Jimmalo, zata kamata ta karɓe don ta rufe sirrin ɗan'uwanta.

Kamar ta fahimci abin da take shirin yi, sai kawai ta ruga Nufaisah ta bita zuwa falo, tare da addu'ar Allah ya sanya babu kowa a cikin falon.

Tsananin tashin hankali ya kamata, ganin Mommy da Daddy suna saukowa. Don haka ta juya zata fita, gudun kar Jimmalo ta nuna musu.

"Nufaisah, kika ce mini kin yi latti?"

"Eh, mantuwa na yi." Ta furta tana sosa kanta.

"Ƙarya take yi Mommy, za ta kwace mini bulumbulum ɗina ne." Ta furta tare da ɓoyewa a bayanta.

"Bulumbulum, a ina kika samu bulumbulum? Kar dai kin fara ɗaukan kayan mutane a makaranta?" Daddy ya yi mata tambayar yana murmushi.

"A ɗakin mai kama da zabiya na..."

"Ba na gaya miki Yaya zaki rinƙa ce masa b...."

Maganar ta maƙale wa Mommy, ganin Jimmalo ta tura bakinta, ta fito da condom ɗin za ta sanya a baki ta hura.

"Innnali wa inna ilahir raju'un! Safeeya, ina kika samu wannan?" Suka yi mata tambayar cikin tsananin razana.

"A ɗakin Ya Aliyu." Ba ta san lokacin da ta kira shi da ya Aliyu ba ganin yadda suka ruɗe.

"Condoms?" Suka haɗa baki gurin faɗi, lokacin da Mommy ta sanya hannu ta karɓa.

Ganin yadda suka razana, sai ta sakin musu tana zare idanu, domin ta yi tunanin mutuwa ta riƙe a hannunta.

"Innnalilahi wa inna ilahir raju'un! Daddy ya furta yana mamakin abin da ya kai condom ɗaƙinsa."

Mommy kuwa ji ta yi kanta yana juyawa, ta fara zargin yana bin mata ne.

Nufaisah, sai ta rasa tunanin da za ta yi, ta manta makaranta za ta je.

"Aliyu mazinaci ne?" Daddy ya yi musu tambayar cikin tsananin tashin hankali.

Mommy ta rintse idanunta, jin mummunar sunan da ya danganta shi da shi.

"Kai Aliyu mutumin kirki ne, na yarda da tarbiyyar da na ba sh.." Kafin ta gama maganar sai Lubaynah ta yi sallama ta shigo, wacce ta tsaya a bakin ƙofa jin ana magana cikin tashin hankali. Nan ta ji duk abin da ke faruwa, sai ta yi murmushin nasara ta shiga ciki.

Saboda tashin hankalin da suke ciki, sai suka kasa amsawa har ta yi sallama na uku. Da ƙyar Nufaish ta amsa tana kallon fuskarta.

Ganin baƙuwar fuska, sai suka yi ƙoƙarin ɓoye damuwar da ke fuskarsu, amma zuciyarsu zafi take musu, musamman Daddy, yana jin tashin hankali yana ƙara xiyartarsa.

"Baiwar Allah daga ina?" Mommy ta ce, lokacin da Nufaisah ta kawo mata ruwa da lemu.

"Na san ba za ku gane ni ba, amma ni daga Kano nake sannan na zo da wata magana ne."

Kallonta suka yi, suna mamakin maganar da ta zo da ita.

"Ok, muna jin ki." Cewar mommy da ta kasa motsawa.

"Sunana Lubaiynah,kuma iyayena a Kano suke. Mun ɗauki tsawon lokaci muna soyayya da Aliyu, har ya yi mini alƙawarin zai aure ni." Ta furta tare da ɗago idanunta ta kalle su, tana son ganin yadda suka karɓi zancen.

Ganin sun zuba mata na mujiya, sai ta gyara murya ta ɗora da cewa,"Aliyu ya yi mini alƙawarin aure, har ta kai ga na mallaka masa jikina, sai bayan nan ya ce ba za aure..."

"Ƙarya kike yi sharri za ki yi masa, amma yarona bashi tarbiyyar da ba zai iya kula matan bariki ba, domin duk macen da take da daraja, ba zata yarda wani namiji ya yi taraiya da ita ba."

Jin abin da Mommy ta ce, cikin fushi sai ta fashe da kuka."Na yarda da haka domin Aliyu yayi mini alƙawarin aure, amma tun daya ga ya mayar da ni farkarsa ya gama wulaƙanta rayuwata sai ya ƙi aurena. Da gaske nake yi game da abin dana faɗa domin har kwana na ke yi a gidansa, wani lokaci in zan yi tafiya tare take tafiya da ni. In kuma baku yarda ba na yarda a kira shi, sannan a yi bincike. Abin da ya sa na zo na gaya muku, iyayena sun yi fushi da ni sun daina kula ni. Shi kuma ya gaya mini ba zai auri mace mazinaciya ba, bayan shi ne ya lalata mini..."

Daddy da yake tsaye yana kallonta, cikin tashin hankali. Wani irin jiri yake gani, domin fuskarta ya bayyanar da duk abin da take faɗa.

"Aliyu da ma abin da yake aikawa ya kenan, ya sanya ya ƙi aure?" Ya yi wa kansa tambayar, yana jin zuciyarsa na zafi duhu yana rufe ganinsa.

"Ta shi ki fita kar ki yi wa ɗana sharri, domin zan iya shedar shi. Sai da in wani Aliyu kike amma ba yarona..."

"Zan iya yarda da maganarta in har ta nuna mini sheda." Daddy ya furta cikin damuwa yana kallonta

Babu musu ta ciro wayarta, tana share hawaye ta fara nuna musu hotunan da suka yi da Aliyu, har da waɗanda bai kamata ta nuna musu ba. Daidai lokacin da ta nuna musu, hoton da suka ɗauka da Aliyu yana kwance da ga shi sai gajeren wando na sojoji ita kuma tana gefenda da matsatstsun kaya.

Da sauri suka kauda idanunsu cikin tsananin tashin hankali.

"Innnalilahi wa inna ilahir raju'un Ubangiji!" Daddy ya furta tare da rintse idanunsa yana jin jiri na ibansa.

Taga-taga ya yi zai faɗi, sai kuma ya dafe kujera jin yadda jiri ke ibansa.

Mommy salati ta furta, tana zare ido cikin tsanannin tashin hankali.

"Tabbas ta yarda ba ka shedar ɗan yau. Ashe duk kame kan da yake yi Aliyu masha'a yake aikatawa? Sai ta rinƙa jin tamkar za ta haukace, saboda wani irin tashin hankali da yake ziyartar ta.
Chapter 50 · 0% Book details