← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 52

Sashe 33

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin sun shigo Kaduna ya sami ajiyar zuciya yana hamdala. Haka Hajiya burinta su iso ya kai ta gidansa, domin ba za ta iya da ita ba.

Ganin ya yi hanyar gidanta sai kalle shi. Abubakar, gidanka za ka kaita ka haɗa da yaranka ka riƙe marainiyar Allah, saboda ka san ba zan iyada rigimarta ba? A wannan shekarun nawa."

Zare idanunsa ya yi cikin tsananin tashin hankali."Hajiya, na ɗauka a gidanki za ta zauna sai a ɗaukar mata mai aikin da zata taya ki tarbiyartar?"

"Wa ni rufa mini asiri na mutu maza su kai ni ba mata ba. Ni Jikar Kulama! Ina na ke da ƙarfin tarbiyartar da ita? Kawai ka kaita ka haɗata da su Nufaisah ka ga Ummu kusan sa'arta ce za ta iya koya daga gareta. Ga kuma mahaifiyarsu kai ma duk za ku kulada ita, amma in har na kaita gidana wallahi zata iya sanya mini hawan ruwa. Don haka in har ba so kake watarana ka zo ka ga na yi bunga ba, to ka kaita gidanka."

Hankalinsa ne ya tashi ya rasa yadda zai yi. Bai taɓa tunanin Hajiya za ta ce a gidansa za ta zauna ba. Shi kuwa ya zai yi ya gyara yarinyar da take jin za ta ya karawa da kowa. Tun da har zata iya kallon tsabar idon maigari ta gaya masa magana don ranta, shi kuma bai san abin da za ta yi masa ba.

Jikinsa mace ya kalle ta."Bari to na kai ta gidanki in ta yi wanka sai na taho da ita."

"A'a muje ni ma zan je gidanka nayi kwana biyu har sai na ga zamanta a gidan." Ta furta mishi don ba ta son taje gidan.

Babu yadda zai yi kan dole ya nufi hanyar gidansa. Suna isa ya yi hon maigadi ya buɗe masa get ɗin. Jin ya dawo duka mutanen gidan har da Mommy suka fito don taransa.

Ganin da Hajiya sai Mommy ta duƙa cikin ladabi, ta gaishe ta tare da yi mata ta'aziya.

Daddy ya buɗe bayan mota ya kira maigari ya zo ya kwance ta. Mamaki sosai ya kama su ganinta a bayan mota. Tun kafin ta sakko suka ji tana ta aunawa mutanen ƙauyen su zagi.

"Subuhanallahi! Alhaji mahaukaciyar ce za ayi mata magani a birni?" Sa'idu maigadi ya faɗa yana kallonta, ganin shigarta da zagin da take yi kamar bamagujiya.

"Kai ne mahaukaci bani ba mai kama da goriba." Ya samu na shi rabon daidai lokacin da ya kwance ta.

"Daddy ba ta da lafiya ne?" Auta ya faɗa.

"Lafiyarta lau ta dawo nan ne za ta rinƙa zama. 'Yar'uwarku ce anan za ta rinka zama da m..."

"What?!" Gabakiɗaya suka ja da baya suna kallonta tare da zare ido.

"Daddy, do you mean ta dawo gidanmu da zama?" Umma ta yi masa tambayar cikin tsananin ruɗani, tana tunanin yadda za su iya rayuwa da ita a cikin gidan.

"Eh anan za ta zauna saboda kakarta ta rasu, kuma kun zama 'yan uwa domin a nan za ta ci gaba da rayuwarta. Ke Jimmalo ki shiga ciki." Ya ƙarashe maganar yana kallonta.

Wani irin harara ta so ta banka masa, amma kuma sai ta fasa ta kalli ƙaton gidan. Kuka ta fashe da shi ganin kyawun gidan.

"Wallahi dama na san tsafi kuke yi, dubi gidanku mai kyau, wannan in ba jinin mutane ake sha ba? A ina za a samu kuɗin nan a yi gidan nan? Wayyo Kaka Tani mun kai kammu inda za a kashe mu saura ni."

Sororo suka tsaya suna kallonta jin abin da ta ce. Hajiya ta cire gyalenta tare da jan tsuka ta fara ƙoƙarin shiga ciki. So take yi ta yi wanka ta bar musu gidan, domin ba za ta iya zama da ita ba. Su da Allah ya ƙaddara wa kazar wahala suna da sauran karfi sai su ɗauki ƙaddara, amma ita kam tana gama wanka za ta tafi, saboda ko muryarta ta ji tana kuka sai kanta ya buga.

"Zo mu shiga cikin gida Jimmalo." Mommy ta ce, ganin Daddy ya kuma hanyar shiga ba tare da ya kalle ta ba.

"Babu inda zani sai dai a mayar da ni Damagaran."

"Kin zo kenan domin ba ki da kowa a ƙauyen. Hatta gidan da kike zama an siyar, don haka ki zo ki shiga cikin gida ki karɓi canjin rayuwar da kika samu."

"Ni fa babu inda zani a yanke mini kai. Wayyo Kaka Tani ina ma tare muka mutu." Ta furta tare da sakin razanannen kukan da sai da ta toshe kunninta.

"Hajiya, ki barta ta zauna a nan tunda ita shashasha ce ba ta san rayuwa a cikin daula ba. Ana miki tayin shiga cikin aljannar duniya kina wani zancen ƙauye wai shi Damagaran. Kawai tun da bata da rabo a duniya a kai ta b.q sai ta zauna a can."

Cikin takaici ta rarumi karfe ta yi gurinshi zata kwaɗa masa."Ba ka san wace ce ni ba a ƙauye ko? Na yi faɗa da mutane masu ƙiba duk ba su samu nasara ba, ballantana kai kana ji da siranta kamar tsinke. Wallahi a gidan nan sai na karya maka wuya." Ta ƙarashe maganar, tana nuna alamun karya wuyar da hannunta.

"Ke ba ki da tarbiyya jakar ƙauye kawai!"

"Don Allah Hassan biye mata za ka yi? Ke Jimmalo zo mu shiga cikin gida." Ta ce tana miƙa mata hannu.

"Babu inda za ni, kuma wallahi tun da ka kira ni da jakar ƙauye, zan nuna maka jakanci, domin sai na zame maka kaɗangaren bakin tulu."Sai kuma ta noƙe ganin Mommy ta ƙara miƙa mata hannu.

Kallonta ta yi, sai kawai ta girgiza kai ta shiga cikin gida. Tunanin yadda za ta yi ta gyara ta take yi.

"Yarinyar nan ta ƙi shigowa tana waje sai ɗurawa Hassan zagi take yi."

"Please ki ƙyamar ta dole ta shigo. Yunwa da dare zai sanyata dole."

"Yanzu ya ya za mu yi da ita?"

"Shine nake ta tunani. Dole na kaita makaranta boko da islamiya, sai na sanya Umma ta rinƙa koya mata."

"Aikuwa ka haɗa umma da aiki yarinyar nan ba ta da kunya, domin bana tunanin zata yarda."

"Ni kaina Hajiya ta haɗa ni da aiki wallahi. Tun da muka je kaina yake ciwo saboda ihu da ta rinƙa yi."

Zama sukayi suna tautauna yadda za su gyara ta, musamman yadda za su yi ta fara wanka da sallah.

Jimmalo, tana harabar gidan riƙe da kayan Kaka Tani da take ji a yanzu sun fi mata komai mahimmanci. Da sun haɗa ido da Hassan, sai ta yi masa daƙuwa tana murguɗa masa baki.

Kallonta kawai ya yi, saboda ya fahimci tafi ƙarfin tunainsa. Shiru suna tunanin za ta shigo, amma har ka kira magrib ba ta shigo ba. A lokacin Hajiya ta yi iyakan ƙoƙarinta, don ta shigo ta kama kanta.

Ganin Hajiya bar gidan, sai ta rushe da kuka ta ɗauki ƙullin kayanta tabi motar tana faɗin,"Gidanki zani ba zan zauna a nan ba..." Kafin ta ƙarashe maganar motar ta fice

Ajiyar zuciya Hajiya ta saki ta kalli Daddy."Jihadi za ku yi don Allah, ka san yadda za ku yi ta zama mai hankali."

Ajiyar zuciya ya saki kawai ba tare da yace komai ba. Hajiya ce take ta yi masa nasiha, da irin alkhairin da yake cikin riƙe maraya.

Bayan ya dawo ya ƙara lallabarta, amma ta ƙi shigowa, domin har da tsoro gidan yake bata, saboda a kyawu gidan Hajiya ba komai ba ne.

Mommy ganin an kira sallar Isha, kuma bata ci duk abincin da aka ka mata ba, sai ta miƙe ta fita zuwa gurin ta. Kuka take yi tana ta kiran sunan Kaka Tani.

"Jimmalo tashi mu shiga ciki gobe xan kai ki ƙauyenku." Jin abin da ta ce su ta kalle ta da sauri.

"Da gaske nake yi tun da bakya son zama damu."

"Eh, na fi son na yi rayuwa a ƙauye bana son rayuwar birni."

"Shikenan, ki shiga ciki ki yi wanka da sallah, sannan ki ci abinci zan mayar dake gobe."

"Zan dai ci abinci na yi dakatsami, amma ba zan yi wanka ba, sannan sallah sai gobe zan yi da safe saboda a gaji."

Galala ta yi tana kallonta, cikin tsananin mamakin abin da ta ce, amma da ta tuna rarrashinta take yi dai ta ce,"Ok, mu shiga ciki to."

Ƙullin kayanta ta ɗauka tare da maƙe su a hamma. A tsanake take tafiya tana kallon gidan sama mai kyau. Mamaki sosai take yi irin kyau da tsarin gida. Ba ta ƙara tsoratar da tabbatar da cin kai suke yi ba, sai da ta shiga cikin falon. Duk halin da take ciki sai ta saki baki da hanci.

"Zo mu je ki shiga cikin ɗakin 'yan'uwanki, ki kwanta kafin gobe." Hajiya ta ce mata tana kallonta ganin yadda take a firgice.

Saboda tsananin kyawu da girman, gidan sai ta kasa musa mata, don tana tsoron ta kwana ita kaɗai cikin dare a su kashe ta, domin har ga Allah tunaninta su suka kashe mata Kaka Tani.

Nufaisah da Umma, suna zaune a kan makeken gadonsu. Nufaisah ce take yin assignment, sai Ummah da take zaune da wayarta tana kallon TikTok. Ganin sun shiga duk suka mayar da hankalinsu kan Mommy.

"Ga 'yar'uwarku nan, za ta kwana gobe zan mayar da ita ƙauye."

A yadda ta yi maganar sun ɗauka da gaske ne. Sosai suka ji daɗi duk da cewar ba su da wulaƙanci, amma sam ba sa son ta rayu da su, saboda abin kunya ne a kalle ta a matsayin 'yar'uwarsu.

"Ok ga gadona sai mu yi amfani da na wa."

"No Mommy, a haɗa ta da Baba mai aiki mana."Umma ta furta tana mata wani irin kallo, saboda tun da ta zagi Captain take jin haushinta.

"Kul! Matsayinta ya wuce haka. Ƴar'uwarku ne don haka ke Umma ki koma gadonta."

"To," Ta ce da sauri tare da ɗauke filo za ta koma.

Nufaisah kallon ta ta yi sai ta kalli Mommy da idanunta yake kanta, don haka ba ta ce komai ba, sai ta ci gaba da assignment ɗinta.
Chapter 33 · 0% Book details