Sashe 15
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Eh, sai ku kwana ko biyu ne."
Murna suka ji Jimmalo ta fara tana tsalle tana faɗin,"Za ni birni na ci daɗi, sai kuma ta tsaya da rawar ta ɓata fuska ta fito waje.
"Hajiya, mene dangantakar ki da wannan mara mutuncin da ba shi da mutunci?"
"Jikana ne." Ta ba ta amsa.
"Taɓ aradu ba zan je ba, saboda na tsani wannan mutumin, kuma in har zan ganshi sai na rama dukan da ya yi mini."
Zare idanunta ta yi jin abin da ta ce.Sai kuma ta yi murmushi."Kar ki damu ai ba gidana yake zama ba, kuma soja ne ba ya zama a garin."
"Au to zan je. Wato dama soja ne shi yasa ba shi da imani? To ai ni bana tsoron soja, saboda tsaf zan iya zama soja, na rinƙa harbe kan 'yan ta'adda. Wallahi tsaf shi ma zan kara da shi, saboda duk ranar da ya ƙara dukana sai na fasa masa kai." Ta ce tare da matsowa gunta, tana washe baki tamkar ba ita ta gama mata rashin kunya ba.
Hajiya jinjina kanta ta yi domin ta fara jin tsoronta, saboda yadda take maganar har cikin zuciyarta. Kallo ɗaya za ka yi mata ka san bata da tsoro. Har ta fara tunanin an ya za tafi da su, saboda kar ta kai tashin hankali gidanta, don ta san duk ranar da Aliyu ya zo haɗuwar ba za ta yi kyawu ba, amma da ta tuna Aliyu ba cika zuwa ba, saboda yanayin aikinsa, sai hankalinta ya ɗan kwanta tamkar ta yi baƙo ya mutu.
"Yee za ni birni bari na je na gayawa ƙawayena." Ta saka ihu tana faɗin haka.
"Amma za ki yi wanka ko Jimmalo?"
Jin tambayar da ta yi mata ya sanya ta ɓata rai." Ni ba wani wanka da zan yi, saboda ƙaiƙayi yake sani."
Zare idanu suka yi ita da Daddy."Ni dai na san in mutum ba ya wanka ne jikinsa yake ƙaikayi."
"Ba dole Hajiya jikinta ya yi ƙaikayi ba, domin daga ganinta tana shafe wata ba ta ga ruwa ba, ko ta yi wankan dadti kawai zata ta so."
"Ai in dai Jimmalo ne sai tafi haka, saboda har na gaji na daina magana. Ta rantse sai bikin ƙawarta za ta yi wanka."
Mamaki suka yi musamman daddy da ko aiki ya dawo bai yi wanka ba, sai ya ji jikinsa na ciwo, bacci kuwa da ƙarfi yake yi a ranar.
"Zan yi daka tsami, amma wanka sai ranar da na sanya ta zo." Kasa cewa komai suka yi har ta fice tana tsalle.
"Bari na haɗa kayan da za mu tafi da su, amma da na kin bari mun zo wani lokacin, tun da kin ga bamu shirya ba."
"Ƙarki damu hatta kaya kar ku ɗauka, akwai komai ita ma Jimmalo zan sanya ta haɗa mata kaya."
"Masha Allah! Shi ya sa aka ce da arziki a garinku gara a gidanku. Yau ga shi kin yi arziki kin tuna damu." Ta ƙarashe maganar tare da fashewa da kuka.
"Kar ki damu ki shiga ki shirya, bari ya shigar muku da kayan."
"To," Ta amsa cikin tsananin farinciki
Jimmalo kuwa, sai da ta gama zaga gari tana faɗa wa ƙawayenta, da abokan gabanta za su je birni a mota. Kafin kace mene ƙofar gidansu ta cika. Wasu suna mata murnar zuwanta birni, yayin da wasu hassada da baƙinciki. Wasu kuwa fata suke ta tafi kar ta dawo, domin ta zame musu kaɗangaren bakin tulu.
Ba su ɓata lokaci ba suka kammala shiri. Jimmalo riga da zani ta canza wanda babu bambanci da kayan da ta cire, domin sun yi duƙu-duƙu tamkar an ƙwato su daga bakin kura. Tun da ta sanya kayan sai da suka yi kusan sati biyu suna jikinta. Sai dai in wari ya sameta ta shiga rafi ta yi wanka da kayan. Kayan sallarsa ne tun da aka ɗinka ta daina sanya wasu kaya sai su. Babu irin faɗan da Kaka Tani ba ta yi mata ba, kan ta ije sai an fita babban sallah, amma ta yi kunnen uwar shegu da ita.
A lokacin da suka fito za su tafi, har wani yanƙayi take yi tana yanga. Tafiyar ma tamkar ba za ta yi ba, ita a dole za ta je birni. Kwalliyar da ta yi, sai da ta sanya daddy dariya ganin yadda ta ɓata fuskarta da kwalli.
Tana shiga cikin motar ventilation ɗin cikin motar ya canza. Daddy har sai da ya toshe hancinsa. Da sauri ya zuge glasses na motar yana sauke numfashi. Ita kanta Hajiya daurewa ta yi, amma kamar za ta yi amai.
Motar na fara tafiya, ƙawayenta suka fara bin motar suna ihu tare da kiran sunanta.
Ita kuma sai washe baki take yi tana ɗaga musu hannu.
Ana kiran sallar magariba suka iso Kaduna. A lokacin da direba ya do shi get ɗin gidan, waigowa suka yi suna kallon juna ita da Kaka Tani.
Sun kasa cewa komai, suna kallon get ɗin gidan mai tsananin kyau. Jimmalo kuwa ji ta yi kanta ya kulle tsoro ya kamata. Tunani ta fara ko cin kai suke yi. Ba ta ƙara shiga cikin tsananin mamaki ba, sai da ta ga maigadi ya buɗe get ɗin gidan sun shiga.
Fitowa suka yi a cikin motar, cikin razana suna zare idanu. Ganin yadda suke mazurai Hajiya ta kama hannunta ta ce,"Ku shigo cikin gidan.."
"Wayyo Allah na shiga uku wallahi ba zan shiga cikin gidannan ba, a cinye mini kai." Ta fasa ihu tare da yin hanyar ƙofar gida tana faɗin haka.
Ganin yadda ta buɗe sai Kaka Tani ta bita."Mu koma ƙauye, na rantse daga ganin gidan nan cin mutane suke yi."
Duk yadda Daddy ya so kar ya yi dariya sai da ya dara. Kallah maigadi kuwa, saboda dariya har sai da ya faɗi ƙasa yana mamakin inda ta same su.
"Cin kai kuma? Wallahi bana cin mutane. Kuma ba sayar da ku zan yi ba."
Da ƙyar suka yi nasarar shiga da shi. Sun zauna kamar za ka ce musu kyat su ruga. Duk rashin tsoro na Jimmalo sai da ta razana da kyawun gidan.
"Ku zauna don Allah ku saki jikinku, wallahi ba zan cutar da ku ba. Gidan nan wannan ya gina mini, saboda Allah ya buɗa masa yana da kuɗi sosai."
Miƙewa Kaka Tani ta yi tana kallon gidan."Yanzu Tine kina nufin yanzu wannan gidanki ne, wanda ɗanki ya gina miki gidan kwalba?"
"Wallahi kin san arziki na Allah ne."
"Haka ne kuwa ganin gidan nan ya tabbatar mini da hakan, amma sai dai ƙauye zan koma saboda bazan iya rayuwa a cikin gidan ba, don ni har yanzu zuciyata tana tantanmar cewar ɗanki ba shan jini yake yi ba ko Jimmalo?" Ta ƙarashe maganar tana kallonta.
"Aradu kuwa gara mu koma ƙauye kawai, saboda har na fara jin wuyana yana rawa kamar zai cire."
"Zo mu koma kafin ya cire mun shiga uku." Kaka Tani ta faɗa tare daka mata hannunta jikinta yana rawa.
"Ke ki ki ji tsoron Allah Jimmalo babu wani tsafin da nake yi."
Hajiya ta ce cikin mamaki. Ganin yadda Kaka Tani ta rikice, saboda ta ɗauka da gaske ne.
Dariya ta sheƙe da shi tana nuna ta da yatsa."Kai Kaka Tani kin tsufa kina son duniya. Wasa na ke miki ai ni na ga gidan zama sai na ga daman koma wa ƙauye."
"Ja'irar yarinya kawai ai sai na ga yaranki zan mutu."
"Wayyo abin kallo yana birni Kaka Tani dubi ƙaton tibin nan don Allah."
To Jimmalo jikar Tani a birni. Ko ya za ta kaya? 😁😁😁😁
Captain Aliyu ya kamata ka zo saboda your amaryato be ta zo😁😁😁
Tallah
Shin y’ar uwa, kin daɗe ana cin miki kuɗi saboda kina siyan maganin nonon da ba kyau ganin result ɗin sa? Kina cikin matan da suke mafarkin ganin sun zama masu cikowar ƙirji, in suka sanya kaya su yi kalar madara zubin ajebota? To maza ki garzayo kar ki ji ƙyashin siyan ingantaccen maganin gyaran nono don daga yau kukanki ya ƙare, in sha Allah. Kin gama kashe kuɗinki gurin maganin gyaran breast
Kizo kisamu ingantaccen maganin gyaran breast ɗinki a gurin Maman Sayyid collection, ta wannan numbar 08063114606 kisha hankalinki kwance maganinmu herbal ne wato na gargajiya bashi da side effects babu wani abun bature acikin maganinmu zallar saiwoyine da ganyayyaki da tsirrai na gyaran nono wanda babu cutarwa saidai su inganta miki lafiyarki inkina shayarwa yaronki zai samu isasshen ruwan nono maganinmu kowa na iya sha 08063114606 ina zaune a kano
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HKTsxAVvVlw2b9mPcAPKke
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423