Sashe 12
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Abinci fa? Daga tafiya kuka dawo ya kamata ku ci abinci." Ta ce sai kuma ta ƙwala kira tana faɗin,"Hafsatu, ki kawo musu abinci."
"Hajiya, da kin barshi in muka koma gida sai mu ci."
"A'a bari ta kawo ai mun gama." Ta ce tare da miƙewa ta nufi kicin ɗin, ganin ba ta ji kiran ba.
Bayan sun gana cin abinci sun mike ta kalli Daddy."Ina son ka samu lokaci sai ka kaini ko, domin so na ke na ɗauko su su yi kwana biyu, yadda Allah ya yi ma 'ya'yana arziki, dole su ci gajiyar haka tun da su kaɗai na ke da su.?"
"Hajiya karki ɗauko mutanen nan wallahi tsaf za su sanya miki hawan jini, domin in har tana gidan nan ba za ki iya shaƙar iska mai daɗi ba."
"Sai kuma na kyale 'yan'uwana su ci gaba da rayuwa a haka? Zuwa zan yi na ɗauko su, sai na gyara musu rayuwarsu na samu lada."
Ganin yadda ta yi maganar a xafafe ya ce,"Shikenan Hajiya, yadda kika ce haka za a yi." Ya ce cikin biyayya.
"Allah ya kaimu kuma ya yi maka albarka."
"Amin," Ya amsa cikin farincikin.
Ko da suka koma gidan hirar Jimmalo suka rinƙa yi. Har lokacin da za su kwanta, sannan aka kashe wutan gidan suka kwanta.
Captain Aliyu da tun da suka dawo ya shiga cikin ɗakinsa ya kulle ƙofa. Zuciyarsa tafasa take yi. Tun da yake ba a taɓa wulaƙanta shi irin na yau ba. Wulakancin ma wata yar ƙauye kucama ƙazama da ita.
"Yarinyar nan da ace babu zumunci. Wallahi sawa zan yi a harbe ta, sannan a ƙona gidansu." Ya furta tare da zaro sigari ya kunna yana shafa.
Kwanciya ya yi, sai kuma ya ɗauki waya zai kira Lubaiyna, amma sai ya fasa ya yi wurgi da wayar cikin takaici. A haka ya kwana cikin tsanannin takaicin abin da ta yi masa, domin ko abinci bai nema ba sai ruwa da ya rinƙa banka ma cikinsa. Ga shi yana gida ballanatana ya sha maganin damuwarsa. Cikin dare kasa bacci ya yi yana ta juye-juye har zuwa uku da rabi, sannan bacci ya yi nasarar sace shi.
Jummmalo zaune a baƙin ƙofar ɗakin Kaka Tani. Kaka Tani take gasa mata inda Aliyu ya haure ta. Ƙuta ta yi tare da jan tsaki."Na rantse wannnan ɗan iskan ɗan birnin da na sani da na karya masa muƙamuƙi, tun da ba shi da mutunci. Da wata fuskarsa kamar alalar da ba ta nuna ba."
"Ke ma jikalle kin cika rikici, daga ganin mutum sai ki hau neman shi da rigima?"
Ɓata fuska ta yi tare da kwaɓa-kwaɓa za ta yi kuka."Kaka Tani, kamar goyon bayansa kike yi, ko saboda sun kawo miki abin arziki..."
Bige bakinta ta yi cikin ɓacin rai,"Ja'irar banza kina ganin har akwai abin da za a kawo mini ya sa na goyi bayan wani? Ba kya gani takanas daga Kaduna suka zo gurina, amma na rufe idanuna na yi musu kashedi?"
"To ai ke ne ba ki ga ciwon da ya ji mini ba kike ƙorafi." Ta ce tana kallonta a sakalce.
"Ina miki ƙorafi saboda ki daina ƙoƙarin gwada ƙarfin ki da maza. Inda ya ji miki rauni ya kike so na yi? Kin san ke kaɗai ba ke gani na ji daɗi."
"Hakan ma ba zai faru ba, saboda kin san ina da ƙarfi. Ni fa kamar soja na ke, domin da ace a birni na ke na yi karatu, aradu soja zan zama na yi ta dukan masu laifi, ina harbinsu da bindiga, kuma ko ciwon da ya ji mini ai shammatata ya yi, wallahi da sai na kai ƙato ƙasa. Tsaf zan wawuri ƙafarsa na danƙarashi da ƙasa, amma ko yanzu a juri zuwa rafi, watarana fili zai fashe, domin na ratse duk lokacin da Allah ya haɗa ni da shi sai na kai gardi ƙasa."
"Kar na ƙara jin haka saboda ɗan'uwanki ne, kuma ba kya ganin irin abincin da suka kawo mana, duk garin nan wa kika ga 'yan'uwansa sun taɓa kawo musu haka?"
Ƙara ta saki tana birgima a ƙasa."Dama na faɗa kwaɗayin abin da suka kawo kike yi, shi ya sa da ya naushe ni, ba ki sanya taɓarya kin ragije shi."
Jikinta ya kama rawa ganin jin abin da take cewa."Haba Jimmalo, ki tashi a ƙasa kin ga kina ɓata kayanki, kuma na san ko sama da ƙasa za ta haɗe, ba za ki yi wanka ba. Ki je ki ƙara ganin kayan da suka kawo mana, na tabbata za ki yarda da abin da suke cewa."
Ƙara ta yi sai kuma ta kalle ta tana satan kallon inda kayan suke. Ganin haka ta kama hannunta tana faɗin,"Yauwa Jimmalo jikar Tani, ma za ta shi kin ji jikalle."
Kamar wata 'yar ƙaramar yarinya ta miƙe tana tafiya, sai ka ce yar kaciya ta isa gurin.
Zama suka yi suna duba kayan. Kayan abinci sosai suka kawo musu, da sabulu man-shafawa da kuma kilin."Kin ga kaya sosai har da man-shafawa na 'yar birni? Da ace ke wata ce sai ki yi wanki kuma ki yi wanka."
Ɓata fuska ta yi jin abin da ta ce,"Aradu ba zan yi wanka ba sai bikin Tasallah ya zo, ko ranar da kika sanya ni dole na yi haka na yi ta soshe-soshe, don haka ba zan cutar da kaina ba."
Zare ido ta yi cikin mamaki jin abin da ta ce,"Sai nan da sati biyu za ki yi wanka Jimmalo? Kin san irin ƙarnin da kike yi?"
"Ni fa ki daina cewa ina wari saboda babu ƙarin da na ke yi." Ta ƙarashe maganar tana sunsuna hammatarta da ya cika da gashi ba ta askewa."Kaka Tani shi shima ki ji wallahi ba ya wari."
Da sauri ta matsa nesa da ita tare da toshe hancinta."Ba kya dai jin warin, amma ko wucewa mutun zai yi sai ya gane ba kyau wanka. Ga kayanki can na wanke, amma ba za ki yi wanka ba?"
"Ba zan yi ba, sai lokacin bikin shi ma don kawai ina son na gurzawa Badaru rashin mutunci ne." Ta ce tare da ɗaukar ledar biskit. Ɓarewa ta yi ta kai bakinta."Kai 'yan birni suna morewa wallahi. Kaka Tani dole mu kai musu ziyara mu je mu ci yo daɗi." Ta ƙarashe maganar tare da miƙa mata ledar biskin ɗin.
"Ah'ah, wai ba dai daɗi ba, kin ji yadda kunnina yake zut!zut? Dole mu je birni, amma kuma kina ganin za su dawo, bayan kin fasa musu gilashin mota?"
"Za su dawo mana, in kuma ba za su dawo ba, sai mu tafi nemansu a birni. Ni fa na so na yi masa mutunci kar na nuna masa kalata, shi ne kawai ya nuna ƙyamata kamar ya ga kashi. Ni kuma haushin hakan ya sanya na fasa masa gilashin motar, saboda ya san ba a ja da ni, kuma kin ga ko dawowa suka yi zai ji shakkata."
"An gaya miki birni ƙauye ne da za mu je nemo su? Kuma na rantse ba na jin zasu dawo."
"In ma ba su dawo ba sai na je nemo su in kina jin tsoro."
"Ke ma kin san duk inda za ki ƙafarsa ƙafarki."
"Haka ne kakata." Ta ce sai kuma ta farko kwalin indomie ta fara iba tana ci.
"Allah ya isa domin Ubangiji kawai zai saka mana, yadda 'yan birni suke cutarmu, suna cin kayan daɗi. Kaka Tani ji wannan kalar biskit ɗin mai gishiri."
Karɓa ta yi ta kai bakinta tana lumshe idanu."Kut! Gaskiya Allah sai ya saka mana, domin garin daɗi na nesa. Shi ya sa kika gansu kamar an ɓaro su a kwali, musamman wannan mara mutunci ba dai gayu ba tsafta ba." Ta ce suna ta cin indomie suna santi.
"Ni fa ban ga kyan shi ba saboda dana kalle shi lokacin da ya mare ni, wai yana amai saboda warin jikina da biri yake kama."
Kaka Tani bata bata amsa ba, Salame ta yi sallama da tirenta na satin ayaba. Ganin ta a zaune ta yi turus! Sai kuma ta ƙarasa."Lafiya Jimmalo, ba za ki je sarin ayabar ba?"
Kallonta ta yi tana shirin ɓoyewa indomie ɗin, domin Jimmalo ba dai rowa ba. Kowa ya sanya da shegen rowa, da kuma son abun wani. Ko gidansu ƙawayenta suka zo tana cin abinci, babu kunya za ta cinye ba tare da ta yi musu ta yi ba, in kuma ta ga na wani jikinta har rawa yake yi. Ko ba a yi mata tayi ba sai ta sanya hannu. Ka yi magana ta ce za ta nuna ma mutum ƙarfi. Yanzu ma ɓoyewa ta yi tana mazurai.
"Ke wallahi Salame, gidanku kamar ba a iya tarbiya ba. Na gaya miki ki dinga sallama kafin ki shigo gidan mutane, tun da ba tsoho da tsohuwa suka gina ba."
Kama bakinta ta yi tana kallonta daidai lokacin da ta ƙaraso."Ke har bakin magana kike da shi? Ke da sai dai ki shigo ɗakin mutane da gudu, saboda an yi miki sai ki ji haushi?"
Harararta ta yi, tana tana ƙara ɓoye indomie ɗin ba tare da ta ce komai ba.
"Jimmalo, wai mai kike ci kike ɓoyewa? Bayan ke mutum ko a takashi ya sanya sai kin ƙwakulo?"
"Babu komai." Ta ce tare da ƙara yanke fuska.
Shammatarta ta yi ta ture ta ta ɗauki indomie."Kai Jimmalo, da ma taliyar birni kike ci shine za ki yi mini rowa?"
Cikin masifa ta miƙe za ta cakume ta, ammma jin ta ce taliya ya sanya ta tsaya."Uban wa ya gaya miki taliya ce? Biskit ɗin birni ne fa, kuma waallahi kika ƙara mini haka, sai na shuka miki rashin mutunci." Ta ce cikin fushi tare da komawa ta zauna.
Ba tare da ta ji kashedinta ba ta ƙara kai hannu ta karɓa."Ke wallahi taliyar birni ne. Kin san Yaya Kabiru yana zuwa birni? Da zai dawo ne ya siyo ya koya mana yadda ake dafawa, kamar taliya aka dafata ga daɗi wallahi."
"Mai ƙarya?" Ta furta tana juya ledar.
"Ɗan wuta kuma in ba ki yarda ba ki gwada girkawa."
Ba musu ta miƙa ta ɗauki tukunya ba tare da ta ɗauke ba, ta ɗora a wuta tare da kumbula ruwa rafin tukunyar.