Sashe 7
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin abin da yake faɗa cikin zafi kukanta ya ƙaru. Sosai take kuka tana kallonsa."Ni ma ba laifinta bane, saboda kallon farko na kamu da sonka. Na yi iyakan ƙoƙarina na same ka a matsayin miji, amma kullum kalmar da kake gaya mini baka shirya aure ba. Na yi tunanin mallakan maka kaina shi ne kawai zai sanya ka aure ni, amma ashe kuskure ne yi. Kuskuren da yake ƙoƙarin nisanta ni da kai." Duƙawa ƙasa ta yi, ta riƙe hannunsa da yake son fita.
"Don Allah ka aure ni, wallahi in har ka rabu da ni zan shiga cikin wani hali."
Hannunsa ya fisge, tare da fita daga kicin ɗin yana jin zuciyarsa na zafi. Falo ya zauna ya ɗauki sigari ya kunna.
Yana zaune a farkon ta fito da gudu ta wuce shi. Haɗa kaya ta fara yi a ranta ta sanya ko shi ne autan maza ba za ta ƙara dawowa gareshi ba, saboda gara son shi ya kashe ta da ta zauna tana roƙonsa ya aureta yana wulaƙanta ta kamar ba ta da aji. Hawaye ta share tuna irin mazan da suke rububinta, amma ta tsaya yana yarfata. Da ta kuma tuna surarsa sai ta ji anya za ta iya haƙura. Addu'a ta fara tana fatan wannan ya zama na ƙarshe, da zata ƙara dawowa yana more jikinta, domin faɗin ba shi ne na farko ba.
Cikin kukan ta gama haɗa kayanta ta fito za ta tafi. Kallonta ya yi, sai kuma ya ɗauke kansa tare da kashe sigarin zai shige ciki.
Ganin haka ta sha gabansa cikin muryar kuka ta ce,"In sha Allahu ba zan ƙara dawowa cikin rayuwar ka ba. Zan yi nesa da kai, saboda na lura ba sona da aure kake yi ba."
Ba tare da ya ce mata komai ba, ya ɗauke kansa wanda hakan ya tabbatar mata da zarginta. Da gudu ta fice sai ya bi bayanta.
"Please in ta fita, ka rufe mini get kar ka bari kowa ya shigo." Ya ce wa Solo tare da komawa ciki, yana addu'ar wannan karon Allah ya sanya kar ta dawo, domin yadda kasan kaska haka ta manne mi shi.
Lubaynah tana tafiya tana kuka har ta isa gidan Yayarta Hannah. Ganin yadda ta shigo a birkice, ta wuce zuwa ɗakinta da take sauka sai ta bita da kallo.
Mijinta Nura ta miƙawa ɗansu Fadil da yake shan nono."Please baby ina zuwa na ga ta shigo a birkice, wataƙila sun yi faɗa da ɗan iska yaronnan da yake yaudararta."
"Ta ke yaudarar kanta dai, har wani namiji za ta rinƙa zuwa gidansa tana kwana, kuma ya aure ta. Kina tunanin ko ni ne zan zaɓawa 'ya'yana ita a matsayin uwa?"
"Ba ita ta sani ai duk yadda ake gaya mata ta ƙi ji. Ba ta yi kuka ba, sai ranar da ta ji aurensa." Ta furta bayan ta miƙa masa shi tana gyara zaman rigarta.
"Na gaya mata sojojin nan sam ba su da amana. Ya kamata ta yi wa kanta karatun ta natsu, ta nemi wanda yake sonta da aura, amma babu kaffara yaron nan ba sonta yake yi ba. Kina ganin ranar data kawo shi gidan nan, yadda yake fisgewa tana wani tarairayar sa kamar za ta zauce. Ga shi yana mata magana a tsaye tsaye cikin isa. Irin wannan ko sun yi auren, ba zaman lafiya za su yi. Yadda wasu sojojin suke ɗaukar mace ba a bakin komai ba, sannan ta haɗu da mai zuciya."
"Ita ta sani, wannan karon zam gaya wa Mommy , saboda babu ruwana tun da ta ƙi ji." Ta ba shi amsa tare da shigewa ciki.
Shiga ta yi tana kwance ta yi rub da ciki, kuka take yi sosai har da sheshsheƙa. Har yau in ta tuna wahalar da tasha a lokacin da ya rabata da mutuncinta, sai ta ji kamar za ta yi hauka, duk wahalar da tasha sai ya ce ba zai aure ta ba? Wannan tunani yake sanya ta ji ba za ta iya haƙura da shi ba.
"Wahallalliya mara sanin darajar kanta! Sau nawa na gaya miki Aliyu ba auren ki zai yi ba? Tsotse ƙwallon mangwaro zai yi, yar ya huta da ƙuda. Kina ganin dama zai aure ki ne?"
"Wallahi Anty Maryam dole ya aure ni, saboda in har ya bijire hakan sai na hana shi zaman lafiya da ita. Ba zan taɓa yarda ya yi aure ya bar ni ba, in har kin ga ya auri wata ki tabbata ba ni a cikin duniyar."
Hattara 'yan mata masu bawa maza kansu kafin aure, domin duk namijin da kika amince ya sanki a 'ya mace ba zai taɓa aurenki ba, sannan shi ne mutumi na farko da zai fara goranta miki. In kunne ya ji.....
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 4
"Wallahi Anty Hannah dole ya aure ni, saboda in har ya bijire hakan, sai na hana shi zaman lafiya da duk wacce ya aura. Ba zan taɓa yarda ya yi aure ya bar ni ba, in har kin ga ya auri wata ki tabbata ba ni a cikin duniyar."
"Sai ki je ki yi ta wahala har ki kashe kanki. Duk wanda bai ji bari ba, ai ya ji hoho. Ki ta biyewa daɗin bakinsa sai ranar da kika ji ɗaurin aurensa, sai ki yi nadama a lokacin da ruwa ya ƙarewa ɗankada."
"A ranar kuma zan yi nadamar yaudarata da ya yi, saboda in har ban yi nasarar kashe shi ba, sai na kashe matar daya aura."
"Shikenan kin yi maganin matsalar da kanki. Ya je ya auri wata ki ƙare rayuwarki a kurkuku." Ta ƙarashe maganar tare da ficewa cikin takaici.
Kwanciya ta yi, ta ci gaba da kuma har sai da ta yi mai isarta, sannan ta shi ta yi sallah ta fito falo don ta ci abinci.
Anty Hannah, tana zaune ganinta ta saki tsaki ta miƙe ta bar falon.
Zama ta yi kan dinning ɗin xuciyarta na suya. Sosai take ganin son zuciyar Aliyu da ya kasa gane tsananin sonsa, ba ita ta ɗorawa kanta ba, saboda da ace za ta iya cire soyayyarsa tuni ta rabu da shi, duba ga irin wulaƙancin da yake mata.
Iya ƙoƙarin da ta yi, na kwana uku ne ta rinƙa danne ƙaunarsa da kamar yanzu ake mata wahayinsa. Anty Hannah tana lura da ita, da take tasa hotonsa tana gani hawaye na bin kuncinta.
Ranar da takaici ya ibeta, ta karɓe wayarta za ta fasa."Wallahi kin ji haushi shashashar banza kawai! Haka kawa ki sanya wa kanki damuwa saboda soyayar wanda bai san kina yi ba? Tun da kika dawo ko kuskuren kiranki bai taɓa yi ba, amma kullum kina rungume da waya kina kallon hotonsa. Ni ina mamaki da takaicin 'yan matan yanzu da suke ɗorawa kansu fitina da sunan soyayya. Soyayyar ma so maso wani. Idan ba ya sonki ki yi haƙuri ki nemi Allah ya baki wanda ya fishi."
"Ba za ki gane son da na ke masa ba. Ni na san in har bai so ni ba, wataƙila sonsa zai kashe ni."
"Ubangiji Allah ya jiƙanki." Ta ce tare da wurgar mata wayar ta shige ciki.
Zama ta yi ta fara gwada numbarsa, amma har ta gama ringing ba tare da ya dauka ba. Daga ƙarshe kashe wayar ya yi. Ganin haka hankalinta ya ƙara tashi. Tsaƙonnin ta fara tura masa da haƙuri.
Aliyu kuwa tun da ta tafi sai hankalinsa ya kwanta. Fatansa kar ta dawo yana ta shirye-shirye tafiya Kaduna.
A ranar da ya shirya ya kulle gidan, ya bawa Peter makulli da zai rinƙa zuwa yana duba gidan.
"Na gaya maka in har Lubaynah ta dawo kar ka bata makulli, ka barta ta shiga, karka ƙara zuwa inda na ke."
"Ok sir," Ya ce bayan ya miƙa masa makullin.
Kayansa ya sanya a cikin motar, sannan ya rufe masa bayan motar ya ce,"Oga safe journey."
Kansa ya ɗaga, ya shiga cikin motar da Peter ya gama wankewa, sai ɗaukar idanu da sheƙi take yi.
Aliyu yana tuƙi ya jingina da kansa, a jikin kujerar motan yana shafa kansa. Iska yake shaƙa idanunsa lumshe, yana jin tsananin yadda ya yi missing ɗin su.
Sosai Mommy ta shirya ma zuwansa, sanin baya cin abincin kowa, ta shiga kicin ta yi masa abinci kala-kala.
Da ya isa gida cikin farinciki Mommy ta fito. Sosai take jin daɗin ganinsa, yadda ya yi shiga ta mutunci.
"Mommy, na same ku lafiya?"
"Lafiya lau ya gurin aiki?"
"Alhamdulillah momi kowa lafiya."
Gaisawa suka yi da Badamasi maigadi, sannan ya shiga cikin gida.
Sashinsa ya wuce ya yi wanka, sannan ya kwanta. Bacci sosai na gajiya ya yi, wanda bai ta shi ba sai da aka kira sallar magariba.