Sashe 44
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Miƙewa ta yi ta harare shi ta ce,"Ni ma na tsane ka, sannan ƙarya na yi?Ai na firgita ka saboda da gudu ka ru..." Bata ƙarashe maganar ba ta ga ya dumfarota tamkar kububuwa yana ƙoƙarin zare bell ɗinsa
Gudu ta fara suka fara zagaye falon."Aliyu, wai biye mata zaka yi?" Mommy ta ce ganin abin da suke yi.
Anty ce ta shiga tsakani ta ɓoye Jimmalo da ya kawo mata hauri.
"Captain Please.."
"Anty get out of this issue, domin za mu samu matsala dake in har kika ce za ki kula ƙazamar yarinyar na.."
"Ni ba ƙazama bace kuma ka..."
"Ke Jimmalo yayanki ne ba shi haƙuri!" Anty ta daka tsawa tana faɗin haka.
"Saboda anga kakata ta mutu za a ce na ba shi haƙuri." Ta yi maganar cikin kuka, domin ko sama da ƙasa za su haɗe ba za ta bayar ba, don bayar da haƙuri ba shi a cikin jadawalin rayuwarta.
"Ba na buƙatar haƙuri, ki bar ni na canza mata kamanni ƙazamiya kawai."
"Kanwarka ce don Allah ku daina haka kai sai ka biye mata?"
"Ki dai gaya masa, tun da ta dawo gidan nan suke sa mini ciwon kai." Mommy ta ce cikin takaici.
"Anty, kin san ina shiri da ke, in har kika son alaƙarmu ta cigaba to ki daina kula ta, domin na tsaneta kuma duk wanda zai yi hulɗa da ita shi ma na tsane shi."
"Aliyu bai kai haka ba, ka je sashinka yanzu zan biyo ka." Ta ce masa tana kallon sa.
"Yayata ce don ta ce za.."
"Jimmmalo an tambaye ki ne?" Ta katse ta jin za ta yi mata ɓaramɓarama.
"Gara ki zo ki gaya mini, domin ina tunanin komawa Abuja yau." Ya ce tare da juyawa zai fita.
"Ki ba shi haƙuri na ce." Anty ta daka mata tsawa tana faɗin haka.
A maimakon ta bashi haƙurin, sai ta murguɗa masa baki tare da yi masa daƙuwa. Zare idanu Anty ta yi wanda karab sai a idanunsa da ya juyo da nufin ya aikata mata da mugun kallo.
Ganin daƙuwar ya dawo daga gudu, yana jin kasheta kawai zai yi ya huta. Da sauri ta ruga cikin ɗaki ta murɗa ɗan makulli. Ta kwashe da dariya tare da kwanciya a ƙasa, ganin ta kunna shi. A ranta ta sanya za ta ci gaba da kunnashi, har sai an mayar da ita gurin Anty.
"Kai innnalilahi wa inna ilahir raju'un!" Mommy ta furta cikin damuwa.
"Kina ganin zagina ta yi Mommy. In har ban kashe wanna yarinyar ba sai na ƙaryata." Ya ce tare da juyawa ya fita.
"Lallai Mommy kina shan aiki." Cewar Anty ta bi bayansa.
Ruwa mai sanyi ya ɗauka ya sha, bayan ya shiga cikin ɗakin. Ganin Anty ta yi sallama ya amsa ta shigo.
"Aliyu gas..."
"Please Anty, in har ba maganar da ya sanya ki ka zo Kaduna za ki mini ba, gaskiya ba ni da lokacin sauraren na mahaukaciyar yarinyar nan." Ya katseta yana faɗin haka cikin huci.
Shiru ya biyo bayansu sai ta buɗe baki ta ce,"Na samu yarinyar kuma kalar macen da kake so, har hotonta da komai an tura mini. Mahaddaciyar Alkur'ani yarinya mai ƙaramin shekaru, abin da ya sanya na ƙarfafa maka ita, saboda tana da ra'ayin auren soja." Ta ƙarashe maganar tare da miƙa masa wayarta bayan ta shiga profile ta danna hotonta.
"Masha Allah! Anty ganin farko ta yi mini." Ya furta yana zooming hotonta.
"Amma bisa sharaɗin za ka daina duk abin da kake yi."
"Anty wallahi ba ni tare da Lubaiyna tsawon lokaci bamu tare, bayan nan ma sigarin da na ke sha ba sosai ba sai raina ya ɓace."
"Shikenan Allah ya ƙulla alkhairin a haifi mana 'yan dugwi-dugwi."
Dariya ya yi cikin jin kunya ya shafa kansa."Anty ina samu yarinyar nan burina ya gama cika, domin ko haka Allah ya barni sai fatan dacewa."
"Gaskiya ni kaina na yi maka fatan aurenta, abin ƙarin farincikin mahaifinta malami ne sosai. Ga numbarta sai ka kira ta."
"No, so na ke yi sai na nemi izini gurin mahaifinta, domin a ranar da muka je za mu samu mahaifinta don mu ganta, in har tana sona ba zan dawo ba sai an yi maganar sanya rana."
"Masha Allah! Ɗan gidana ya motsa da ƙarfinsa. Allah y ba ka ita."
"Amin, ai irin matan nan da suka fito daga gidan tarbiyya, ba a wasa da su."
"Haka ne kai ma na san ba za ta ƙi ka ba, domin babu macen da za ta ce bata sonka. Don Allah kar ka gaya ma kowa ni na yi maka hanyarta."
"Kin san ba zan fadi ba."
"Yauwa bari na wuce amma Captain yarinya..."
"Anty, kin kawo mini albishirin da ya sanya ni farinciki, kuma za ki sanya ni baƙinciki?" Ya furta fuskarta na ƙoƙarin canzawa.
"Shikenan za mu yi maganar anjima." Ta ce masa tare da fita.
Tana fita ya kulle ɗakinsa, ya ci gaba da kallon hoton Nu'aimah cikin tsananin shauki. Lokaci guda ya ji ƙaunarta ya mamaye zuciyarsa.
Numbar Kalim ya kira cikin tsanannin farinciki."Hello, abokina na samu matar aure. Zuwa gobe za mu je ka shirya da na dawo."
"Masha Allah! Da gaske Captain ka samu wacce kake so?" Ya yi masa tambayar cikin mamaki.
"Na samu Kalim ka taya ni da addu'a, Nu'aimah ta zama matata. Yar gidan malamai kuma Malama mahaddaciya."
"Lallai Allah yana sonka, ka gama sheƙe ayarka ka samu mace ƙwarai Allah ya sanya mu a danshinka." Dariya ya yi jin abin da ya ce, tare da kashe wayar bayan sun yi sallama.
Murna sosai yake yi kamar zai shiɗe. Zaman yi yana tsara yadda zai yi shiga da kalaman da zai tsara ta, har da kallon da zai yi mata, wanda zai sanya ta zurma daga haɗuwar farko.
Mai ɗinkinsa Muhammad, da yake garin Abuja ya tura masa da hoton shaddar da yake son ya siya ya ɗinka masa, sannan ya yi wanka ya fice zuciyarsa cike da murna.
Lubaynah, iya lokacin da ta jira ta dawo ta shiga tsananin damuwa, domin tunawa da take Captain ba zai saurarenta ba duba ga rabuwar da suka yi, hakan kawai ya sanya ta daure. Ga shi abin takaici tun da lamarin ya faru iyayenta suka canza mata fuska da tsautsaurar tsaro. Sai ta gane ganin Captain Aliyu ya haɗa mata zafi biyu. Ga rashin sa da kuma fushi da iyayenta suka yi da ita, wannan dalilin ya sanya ta ji za ta iya aikata komai don ta karkato da hankalinsa gareta.
A ranar da ta do ta tafi zuwa gidansu. Bayan sun yi hira sun gama zagin maza da suke tsotse ƙwallon mangaro su huta da ƙuda, sannan suka gangaro kan abin da ya kawota.
To Captain mai son auren mace ta gari. Shin kana cinmma gurinka? Ko reshe zai juye da mujiya? In har Lubaynah ta ji zai yi aure za ta zuba idanu kuwa? Ku ci gaba da bibiyar da zafafafen comments.
Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 22
*Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso kusa kar ayi* *babu ke*
*Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so*
*ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa*
*MTN 1gb 650*
*2gb gb 1300*
*Iya adadin da kuke so muna turawa*
*"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da kayan kitchen duk akan farashi me rahusa*
*Arabian oud*
*Lamsa oud*
*Black oud*
*Da Duk wane oud da kake nema*
*Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa*
*Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin*
*S D Y COLLECTION AND KITCHEN*
*Adress ringi road, na dorayi, kano*
*muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah*
*Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap*
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*08130902505*
Lubaynah, iya lokacin da ta jira ta dawo ta shiga tsananin damuwa, domin tunawa da take Captain ba zai saurareta ba kawai ya sanya ta daure.
A ranar da ta dawo ta tafi zuwa gidansu. Bayan sun yi hira sun gama zagin maza da suke tsotse ƙwallon mangaro su huta da ƙuda, sannan suka gangaro kan abin da ya kawo ta.
"Kin san shawarar da na yi? Ba da boka ko malam za mu fara aiki ba. Abin da na yanke ki je gidansa sai ki gaya masa cewar kin haƙura da shi, ki roƙe sa da ya zo ya gaya wa iyayenki kun tuba sannan har kin samu wani za ki aura. Kin ga na farko kin samu ya shirya ki da iyayenki."