Sashe 22
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hmmmmh! Allah dai ya kyauta domin sun gasa mini aya a hannu. Ni sai yanzu na ke jin daɗi abin da ya faru suka tafi, saboda wallahi tun da ta zo gidan nan na rasa natsuwa, kullum cikin bari-bari na ke yi kamar wata yarinya."
"Ai barnar da ta ke yi bana tunanin ɗan shekara biyu zan yi. Da gangan yarinyar nan ta lalata gas cooker, wai tana son ta ga ko wutar daga kasa yake fitowa."
"Ɓanna ai ta yi kala-kala, bayin ɗakin da suke duk ta lalata famfunan saboda wasa da ruwa."
"Ruwan da ba za ta yi wanka ba. Kai yarinyar nan ƙarshe ce gurin ƙazanta."
Hajiya ta yi ajiyar zuciya ta ce,"Na huta ai da nayi ninyar tallafawa rayuwarta, amma Allah ya ba ni ladar ninya, don tafiyarsu ji nake yi kamar an sauke mini kaya."
"Gaskiya yau za ki yi bacci har da munshari."
"Je ki gyara ɗakin gobe sai an yi wa gidan nan kwalema."
"To Hajiya Allah ya kyauta ya shirya su."
"Amin," Ta ce tare da ɗaukar wayarta ta yi ciki tana laluben numbar Daddy.
Bugu da ya ɗauka cikin girmamawa."Hello Abubakar, dama waɗannan mutane haka suke?"
Dariya ya yi jin da muryar da ta yi magana." Sun fi haka musamman Jimmalo, mai suka yi miki?"
"Ai ita ma kanta Tani ba sauƙi, saboda duk abin da take yi, ita ta ɗorata kan turbar hakan. Da ace ta ba ta tarbiyya mai kyau, da bata zama haka ba. Maraici hauka ne da za ta zauna ta lalata yarinya."
"Hmmmmh! Aini ban taɓa ganin mutane irinsu ba."
Abin da ya faru ta kwashe ta gaya masa. Dariya ya ƙara yi ya ce,"Yanzu sun tafi?"
"Sun tafi Abubakar. Gara su tafi wallahi har sun sanya mini hawan ruwa ba jini ba, domin na tabbata da za a duba jinina ya hau."
"Allah ya shirya su ai zama da su babu wanda zai iya. Hajiya ni fa tun da ta iya kallon Aliyu ta yi masa rashin mutunci na tsinke da lamarin yarinyar nan."
"Yanzu ma ba ka ga rashin kunyar da ta yi masa ba, kuma abin takaici Tani ba ta gani ba, sai zagi take yi wa Aliyu."
"Abin da ya faru kenan a lokacin da muka je ƙauyen su. Wallahi in kika ga yadda ta yi wa Aliyu sai kin yi mamaki. Da ace ban tsawata masa ba, na rantse ko bai kashe yarinyar nan ba sai ya ji mata rauni yadda ya fusata."
"Dole ya fusata ko ni na ga rashin kunyarta. Yanzu dai sun tafi kuma ba zan ƙara bibiyar rayuwarsu ba. Zumuncin ma na haƙura Allah ya gani na yi iyakan yi na."
"Haka ne Hajiya Allah ya ba ki lada."
"Amin, don Allah in zaka koma gidan ka biyo da likita ya duba ni."
"To shikenan Hajiya yau za ki yi bacci mai daɗi."
"Har da munshari Jimmalo ko hawan jini."
Dariya yayi sanan ya yi mata sallama ya kashe wayarsa. Mommy da take zaune a kujerar mai zaman banza tana saurarensu.
Dariya sosai ta yi ganin ya kashe wayar. Shima dariya yake yi.
"Dama na san ba za ta iya da su ba, domin Waɗannan mutanen sai Allah."
"Wallahi kuwa lamarin su kam babu wanda zai iya jurewa."
"Haka ne."Ya ce suka ci gaba da hirarsu.
Captain Aliyu
Awa ɗaya da minti goma daidai ya ɗauka zuwa Kaduna. Duk da yau yake son ya dawo, amma cikin natsuwa ya yi tuƙin har ya isa.
Dama ya sanar wa Anty Amarya. Tun da ta tashi ta fara shirin tarbarsa. Hanifah da ta ga ta aika kasuwa an yi mata cefane har dasu hanta nama da za ta sanya a cikin dambun, sai ta kalle ta lokacin da ta shigo ɗakinta tana zaune tana gyara tsaki.
"Anty Amarya, na fara zargin kamar mutumin ki zai zo?" Ta yi mata tambayar cikin tsananin murna.
"A'a Babanku ne yace na yi masa dambu." Ta faɗi hakan don bata dan su san zai zo, su zo suna masa kwarkwasa ya yi musu rashin mutunci.
"Gaskiya Anty ban yarda ba, saboda wallahi in ya Captain ne kawai zai zo kike irin wannan dambun. Don Allah ki gaya mini wallahi ina son Ya Captain. Ta ƙarashe maganar cikin hawaye tare da kama hannunta.
Tausayi sosai yarinyar ta ba ta, domin da akwai abin da za ta iya yi don ya aure ta, da tuni ta yi hakan. Ta sani sosai take son shi. Ba wai don ɗiyar mijinta bane, amma duk cikin 'yan matan tafi ƙaunarsa, saboda ta sha yi mata kuka kan ta sanya Captain Aliyu ya so ta, amma ta kasa fahimtar Aliyu ba irin mazan da za'a yi masa cushen mace, ko kuma a bashi shawarar ya aureta. Yana da ra'ayinsa kuma duk kusancin da mutum yake da shi, sam ba ya ɗaukar shawararsa. Har yau da suke ganin kamar asiri ta yi masa yadda yake kula da ita ya shaƙu da ita, amma ba ta da hurimin da za ta iya ba shi shawara ya ji. Abin da Captain ya so shi yake yi. Ko zaɓin da ya bata na matar da yake so, ai sai daya jero mata abubuwan da yake so.
"Hanifah, Please ki cire Aliyu a ranki yana da kalar zaɓin matar da yake so. Kina da kyau da ilmi za ki samu namiji na gari. Don Allah ki cire wa ranki son maso wani. Aliyu ba zai aure ki b.."
"Don Allah Anty kar ki mini mugun baki. Ba zan iya cire ƙaunarsa ba. Anty na yi kuka na yi addu'a da sadaka, amma har yau ƙaunarsa ƙaruwa take a cikin zuciyata." Ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka.
Sosai ta ba ta tausayi domin ta san tana son shi. Da ace akwai abin da za ta iya yi, za ta taimaka mata don ya aure ta, kuma shi kansa ya dace mata. Sam ba ta da makusa she is fine and looking dashing, amma Captain murɗaɗɗen mutum ne kuma ba a yi masa dole."
Ganin yadda ta ke kuka sai ta koma hannunta ta ce,"Ki bar kuka shi ne zai zo, zan yi ƙoƙarin yi masa magana, amma don Allah Hanifah ki rage son shi kar ki yi abin da zai cisga ki."
Wani ihun tsalle ta yi ta rungumeta."Na gode Anty, bari na je na shirya idanuna dakunnuwa cike suke da ɗokin jin muryarsa da ganinsa." Ba tare da da jira abin da za ta ce ba, ta ruga da gudu don ta yi wanka.
Anty girgiza kanta ta yi, cikin haushinta ta ci gaba da gyara tsakin.
Kamar yadda Hanifah ta zargi zuwansa haka sauran 'yan matan. A tunaninsu Anty Amarya ta ɓoye musu, don Hanifah ta yi kwalliyar da za ta sace zuciyarsa. Tun ba yau ba su da iyayensu suke zargin tana son haɗa su, saboda ita 'yar mijinta ne.
A dalilin wannan tunanin ya ƙara mata tsana a cikin gidan, amma sam bata damu ba tun da suna zaman lafiya da kishiyarta, sannan ƴaƴanta suna yi mata biyayya, domin biyayya da Hanifah take yi mata tamkar ita haife ta.
Tana wanke tsakin, ta ji sallamarsa shi da Yaya Sama'ila da yake ta tsokanar sa.
"Soja mazan fama." Dariya ya yi yana shafa kansa.
A tare suka shigo tsakar gidar, kusan duk mutanen gidan suna waje don shan iska.
Jin sallamarsa gabakiɗaya gidan ya ruɗe da murnarsa. 'Yan matan da suka ci kwalliya suka ƙyafe suna jiran zuwansa, zarginsu ya tabbata. Wani irin tsanar Anty Amarya ya kama su. Mufida da uwarta yadda take jin sonsa, in har ya zaɓi Hanifa ko da Malamai sai ta raba shi da ita, domin in har Captain bai aure ta ba, yi babu wacce za ta aure shi a cikin 'yan matan gidan.
Anty Amarya da take tsaye, da gayyen zogale a hannunta za ta tsinke. Sosai ta yi murnar zuwansa.
"Soja marmari daga soja mazan fama." Anty ta yi masa kirarin da ya faɗaɗa murmushinsa.
"Anty Amarya na same ku lafiya?"
"Lafiya lau Captain Aliyu, ya hanya da su Hajiya Mommy K.d da auta?"
"Duk suna lafiya suna gaishe ku." Ya ƙarashe maganar, tare da shiga cikin gidan don ya gaida iyayensa maza.
Ɗakin Baba Audi ya shiga, mahaifin su Mufida domin shi ne kawai take gida bai fita kasuwa ba, saboda janta da yake yi.
Bayan sun gaida shi, sannan ya zauna a gefensa yana masa ya jiki.
"Jiki da sauki soja. Na ɗauka za ka zo bikin, amma Ya Abubakar ya ce kana Yukrain?"
"Eh wallahi ai mun dawo duka bai wuce wata ɗaya ba."
"Da kyau, Allah ya yi albarka ya kuma tsare ku ya ba da sa'a. Kuna ƙoƙari sosai domin kune kuke tsaron rayukanmu da kuɗaɗen mu."
"Haka ne Baba Audu. Bari na shiga gurin Anty Amarya, na bar ka ka huta."
"To shikenan kafin ka tafi za ka je ƙwarbai ka gaida Goggonka Mariya ita ma ba ta ji daɗi ba, domin har sai da aka ƙara mata jini. Mahaifinka ya zo shi ma.Wataƙila ya gaya maka ciwon?"
"A'a ya manta ne duk da ban jima da zuwa ba na taho nan."
"To ya kamata ka duba ta, ta yi jinya sosai."
"Zan je Allah ya ƙara sauki."
"Amin, Allah ya yi maka albarka ya ba ka mata ta gari."
"Amin," Ya ce sannan ya miƙe zai fita.
Gyaran murya ya yi, jin haka ya dakata ya tsaya don ya san magana zai yi masa.
"Aure Aliyu sai yaushe? Ya kamata kayi aure, musamman aikin ka kana hurɗa da sojoji bata gari. Kai kanka Allah ne ya tsare ka, saboda shigarka soja bai sanya ka ɓata tarbiyar daka samu ba."
Jim ya yi sai ya ce,"Zan yi har yanzu ina dubawa ne. Matan ne dole dai mutum ya duba wacce za ta tarbiyartar da yaransa."