← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 52

Sashe 38

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamaki sosai ya kamata, ganin yadda ta ɓata ƙaton sabulu guda ɗaya a ruwan buta. Ta buɗe baki za ta yi magana sai ta ga tana kallonta tana jan majina. Mommy ji ta yi kamar ta saka kuka saboda har hawaye sun cika idanunta, domin abin da ta yi ko auta ya yi sai ta yi masa shigen duka. Tara mata ruwan ta yi ba tare data kalle ta ba, sai ta ije mata soson wanka za ta fice

Zuciyar Jimmalo fes ganin yadda ta tunzurata."A mayar da ni damagaran na yi rayuwa a ƙabarin kaka Tani, saboda ita ce kawai za ta jure halina"

"Dama sai ita da ta ɓata tarbiyarki, ni ma na ƙosa ki koma Damagaran, in ba haka ba sai kin sanya mini hawan jini.' mommy ta ƙarashe maganar tare da rufe mata kofar.

Ba wani wanka ta yi ba domin datti kawai ta tayar, sannan ta kwara ruwan a jikinta ta fito. Da ace za a murza jikinta babu abin da zai hana zubar ɗauka, domin ita kanta da ta yi wankan ta san ba ta wanki ba.

Tana fitowa Nufaisah ta shigo ta kalle ta ta ce,"Mommy, ta ce ga mai da kaya ki sanya."

Harararta ta yi ganin haka ta saki tsaki tana mamakin rashin kunyarta.

Duk da kyawun kayan ba ta sanya su ba, sai ta ɗauki kayan Kaka Tani ta sanya.

"Ni ba zan sanya wannan hijabin ba." Ta ce tare da ɗaukar gyalen Kaka Tani ta yafa.

"Wallahi na yi kyau, sosai kayan Kaka Tani ba ƙaramin ɗaukar jikina yake yi ba. Allah sarki Kaka Tani na yi rashin Kakata mai ƙaunata." Ta ce lokaci guda idanunta suka kawo ruwa, domin duk lokacin da ta sanya kayan sai ta ji jikinta ya yi rauni.

"Mommy, ta ce ki zo ki tafi." Umma ta ce sai kuma ta tsaya dariya na son kubce mata ganin shigar da ta yi.

To Jimmalo za a shiga boko ko ya ya za a yi karatun? Mu je dai zuwa mu ga yadda za ta kaya.
Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0

*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!

08144072423

PAGE 19

*Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso kusa kar ayi* *babu ke*

*Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so*

*ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa*

*MTN 1gb 650*
*2gb gb 1300*

*Iya adadin da kuke so muna turawa*

*"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da kayan kitchen duk akan farashi me rahusa*

*Arabian oud*

*Lamsa oud*

*Black oud*
*Da Duk wane oud da kake nema*

*Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa*

*Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin*

*S D Y COLLECTION AND KITCHEN*

*Adress ringi road, na dorayi, kano*

*muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah*

*Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap*

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

*08130902505*

"Mommy, ta ce ki zo ki tafi." Umma ta ce sai kuma ta tsaya dariya na son kubce mata ganin shigar da ta yi.

"Dallah gani nan zuwa kike kallona kamar ba ki san ni ba." Ta daka mata tsawa, tana watsa mata harara kamar idanunta zai faɗo ƙasa.

Da sauri ta koma falo tana dariya."Mommy, kin ga shigar da ta yi kuwa? Yadda kika san wata tsohuwa."

"Ni dai kawai ta zo su tafi, na gaji da yarinyar a kwana ɗaya."Mommy ta ce kamar za ta yi kuka.

Daddy na saukowa daga sama da nufin ya kira Aliyu, sai ta murɗa ƙofa ta fito.

Dariya sosai ta kama su."Jimmalo, don Allah ki daina shigar nan. Ki kawo kayan nan a ƙona, mutane na gaya miki dariya za su rinƙa miki."

"Babu wanda zai ƙona mini kaya, kuma ba zan daina sawa ba." Ta ce cikin rashin kunya.

Mommy kallonta ta yi, domin ta gwammace da ba ta yi wankan ba, duba ga yadda ta taso da datti.

"Don Allah Daddy ku je kawai, wannan kafaffiyar yarinyar ba za ta canza kayan ba."

"Ok, Umma da Nufaisah ku taso ku tafi."

"Ok," Suka ce tare da fara tafiya.

Ganin haka suka bi bayansa, har da Jimmmalo da take ta yanke shawarar yadda za ta gudu ta koma Damagaran.

Aliyu na zaune a falonsa yana huci, kamar mesa Daddy ya yi masa sallama ya shigo. Tun lokacin da ya tura masa tsaƙon, ya fito yake jin kamar ya kashe kansa.

Jin sallamar Daddy ya sanya shi fitowa yana huci."Je ka kai ƙanwarka makaranta, in ka gama mata rigister ka kai ta islamiyar su Nufaisah."

Ganin da su Umma za a je sai ransa ya ɓace sosai, domin ya shirya sai sun fita ya ce ta bar garin, bayan ya wahalar da ita a mota, domin wani irin gudu ya shirya zai yi da ita.

"Mu je amma ba zan iya ɗaukar mahakaciyar nan a mota..." Maganar ta maƙale masa ganin shigar da ta yi

"Daddy, kana ganin shigar mahaukatan da ta yi? Su kansu masu makarantar ba za su ɗauke ta ba, ganin shigar haukar nan. Wannan yarinyar makarantar mahaukata ya kamata a sanya ta."

"Kai ne mahakacin ba ni ba." Ta ce masa cikin gatsali.

Ganin yadda ya harzuka sai Daddy ya ce masa,"Don Allah Aliyu ku je na riga na yi magana da mai makarantar. Kuma kar na ji ka kai hannu jikinta, innba haka ba su na yi mummunar saɓa maka." Daddy ya ce cikin ƙosawa.

Nufaisah da Ummu suka shiga gaba sai Auta a gaba. Daddy ya nuna wa Jimmalo gefen Umma da take ta addu'ar Allah ya sanya gefen Nufaisah za ta shiga, amma sai ta ga addu'ar ta ba ta karɓu ba, ganin haka ta yi dubarar juya mata baya ta toshe hancinta, domin har yanzu wari take yi.

Aliyu kafin su tafi sai da ya ƙarar da kwalbar turare, domin tana shiga ƙamshin motar ya canza.

Maigadi ya buɗe masa get ya fara tafiya cikin takaici. Yana fita daga gidan ya kashe motar ya fito.

Buɗe gefen da take ya yi, tare da fincikota ya watsa a boot, sannan ya shaƙi numfashi mai daɗi.

"Banza ƙazamiya mara kunya. In har zan fita dake sai dai ki rinƙa zama a Boot." Ya ƙarashe maganar tare da rufe boot ɗin da karfi.

Mamaki sosai su Umma suka yi, amma sai suka hankalinsa kwance ba tare da tunanin komai ba yake tunkinsa bayan ya ƙara fesa turare, domin wani irin wari take mishi. Jin zata dame shi da buga Boot ɗin ya sanya waƙa har suka isa.

Sai da ya mula baya sun gama fitowa kalli Nufaisah."Buɗe mahaukaciyar can." Da sauri ta ƙarasa tun kafin ya gama maganar saboda tausayinta, domin ta ƙara tabbatar da ba shi da imani.

Tana buɗe ta ta saka kuka, ta fita da sauri tana sauke numfashi. "Mugu azzalimi sai na rama abin da ka yi mini."

Ba tare da ya kalle ta ba ya wuce ofishin Principal. Jimmalo sai ta nemi guduwa, amma babu hanya kan dole ta bi bayan su Umma, tana ɗura masa ashar da jawo masa jifa'i.

Umma aji ta wuce da sauri, don kar ƙawayenta su ganta da Jimmmalo. Auta ya shiga na shi ajin. Nufaisah ce ta bi shi zuwa ofishin Principal ɗin.

A lokacin da ta fito, kallonta ɗaliban suke yi cikin tsananin mamaki. Ba tare da ta damu da leƙenta da 'yan ajin suke yi ba, ta bi bayan Nufaisah.

Captain kuwa tuni ya shige ofishin Principal ɗin"Mahaukaciyar ce innta yi abu duka ake mata sannan take natsuwa. Da zarar ta yi muku hauka ku sanya sajen ya yi mata dukan tsiya.

Ya cewa Principal ɗin da yake kallon ta cikin mamaki ganin shigar da ta yi.

"Ok bari na gama mata interview sai na san inda zan sanya ta, domin yarinyar ta yi girma kamata ya yi a sanyata a aji uku."

"She is illiterate ba ta san komai ba. Ku sanya ta a nursery one." Dariya sosai ya yi jin abin da yace.

"Ta yi girma sosai, domin ko primary six aka sanya ta ta girma, amma dole haka nan za mu sanya ta in ya so sai ki ɗaukar mata tuitor a gida."

Tsaki ya yi don,' wannan ba shafe shi ba, saboda a gurin shi in ta so ta mutu a jahila.

Ganin haka ya juya gurin Jimmalo da take ta raba idanu.

"Ke what is your name?" Ya yi mata tambayar yana kallonta.

Jin turanci ya yi mata ba ya gane ba, domin inda an tambaye ta bata san yaren da yi yi mata ba.
Chapter 38 · 0% Book details